AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 37-38

Via OHW????
Hilal yashigo dakin yayi tsaye yana kallonta, yanayin yadda tayi kwanciya yasa yaji aransa kamar tanada gajiya a tattare da ita hakan yasa bai tada taba,
Wurin cire kayansa yanufa ya cire tufafinsa, jallabiya ya janyo yasaka, sannan yanufi gado, har alokcin saida yayita kallon ameelah, yau cike yake da sha’awarta amma bazai takura mata ba, murmushi kawai yayi, ya kwanta ya janyo bargo, a hankali ya karanta addu oinsa na bacci sannan ya rufe idonsa,
Duk abinda ykeyi ameelah najinsa amma saita basar, kamar bacci take
Kusan awa daya tana kwance amma bacci take ba,
Sannan tatashi tayi mika tana kallon hilal, amma duk da hakn bata tashiba, sunansa tarika kira a hankali, taga ko motsawa baiba hakan ya tabbatar mata da cewa yayi bacci, sannan tatashi a hankali, tana tafiya cikin sanda harta fita daga cikin dakin,
Daman wayarta na falo tana chaji, wurin wayar tanufa ta dauko wayar tadawo saman kujera tazauna, agogon wayar ta duba 11:30, wani irin dadi taji domin bata saba alkawarin datayiwa Hmm ba,
Data ta bude cike dajindadi, massages suka fara shigowa, saida tajira suka gama shigowa kaf sannan tafara shiga whtsapp, bunbude sakonan takeyi ahankali tana yin reapply, hartakai ga number hajna beauty,
Dubawa tayi taganta tana online, ai kuwa nan suka fara chart hajna tayi mamaki sosai ta yadda taga ameelah tana matsayin matar aure amma tana chart din dare, har kusan 12..

11:56 Hmm ya shigo online, tana cikin charting da hajna taga text dinshi yashigo, da sauri tafito daga cikin hajna tadawo cikin hmm sakone yaturo

Hmm “Gaskiya beauty ina matukar jinki a raina, ta yadda kike cika mini alkawari”

Ameelah “hmm bakomai ai danna faran ta maka nake”,

Hmm “?? thnx i love yhu, ina jinsonki harcikin zuciyata, gaskiya bazan iya hakura dake ba, sonake kizamo mallakina”

Murmushi ameelah tayi kafin tafara typing

Ameelah “??toh meyasa kakeson nazamo taka”

Hmm “hmm beauty kenan saboda ina sonki mana, wai kinkosan yadda nakesonki, bana iya minti talatin batare da ka kalli pic dinki ba”

Ameelah “?? toh lallai kana sona sosai to idan nazamo mallakin wani fa”

Hmm ” ?? aikuwa wlh dasai nakashesa, kuma kisa hallahira”

Ameelah “?? kisa kuma, kana nufin zaka iya kisa akaina kenan”

Hmm “sosai ma kuwa wlh idn har akace za a rabani dake to baa nemi zaman lafiyaba”

Ameelah tayi dariya a zuce take fadan wannan baida hankali, inajin ya zauce, nadi nake matar aure taya zaiyi wannan ikirarin akaina, ni wannan soyayyar tamu a whtsapp kadai nadauketa amma banda zahiri,
Murmushi tayi sannan tafara reapply

Ameelah “???? toh idan nice nace bana sonka fah, yaza kayi “

Hmm “?????? kidainamin irin wannan wasar, babu abinda natsana a duniya irin yaudara, budurwa ukku nayi kuma kowacce nina kasheta da hannuna saboda ta yaudareni, beauty idan kema kika yaudareni, kasheki zanyi sannan kuma nakashe kaina, domin nasan dacewa nazo duniya da rashin saa, bantaba jin nakamu dason macce kamar ydda nakamu dasonki ba, Dan Allah beauty karki yaudareni,.domin bana bashin yaudarah”

Tun bata gama karanta text dinba tasoma jin jiri, wani zafi taji yafara fita daga jikinta, dukda fankar datake cikin falon, amma bata hana zufa yakaryi ta jikin ameelah bah,

Wani iri tsoro taji yakamata, ayya kuwa wannan mutum ne, hannunta tadaga tana dan fifitawa jikinta,…
(A zuci nace su ameelah angamu da …????)

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button