AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 43-44

Wata karamar asibiti ta tabayan layinsu nan ya dosa, a manne yakarasa asibitin, ya kashe motar ko cire keys bai tsayaba yazagaya ya dauko ameelah ya tafito da ita daga cikin motar yamayar da kofar motar ya rufe, yanufi cikin asibin a gigice yake tafiya yana kiran sunanta, amma bata motsaba yana isa cikin asibin likitoci suka karbeta, suka nufi emergency room da ita, hilal yayi kokarin shiga dakin amma suka hanashi, wuri yasamu agefe yazauna ydafe kai yana hawaye tambayar kansa yake “meya faru da ameelah Allah katada kafadunta”
Zufa ya karyo masa yasa hannu ya shafe,…
(Bawan Allah hilal, abin tausayi, matarsa sai ci masa Amana take, da sannu Allah zai saka masa)…

Lalluben aljihunsa yafarayi, yafito da wayarsa ya kira iyayen ameelah,

3:40am
Suka karaso asibitin, yana ganinsu yatashi tsaye suka karaso gurinsa, a gigice momy tace “meya faru da ameelanah.. Hilal meya faru da ita”

hilal ya girgiza kai “momy wlh nima bansanibah kawai nazo naganta akwance ne a falo”

Cike da mamaki momy tace “falo kuma, tokai kana ina” hilal ya bude baki zaiyi magana abba yace “yanzu balokacin wannan tambaye2 ne ba, kuzo muje muji me likitoci zasu fada akan” abba yafice momy ta kalli hilal kallon rashin fahimta sannan tabi bayan abba, hilal ma yabi baynsu…

Sunfi minti 29 a bakin dakin da Ameelah take ciki sannan likita fito, da sauri suka taresa,

abba yace ” likita meke damunta “

likita ya dube abba, momy and hilal yace ” babu abinda ke damunta sock ne kawai akwai abinda ya firgitata, tasana diyarsa tasamu sock, amma batada wani matsala kowanne lokacin zata iya farkawa, idan ta farka kuma tana bukatar hutu kafin kuwuce da ita gida”

abba yace “alhamdulillah, Allah mungodema, ya juya gurin likitin “yanzu likita zamu iya shiga muganta “

likita yace ” a a ba yanzuba kujira harta farka, ko kuma dayanku yashiga domin idan tafarka taga wadda tasani kusa da ita, kota samu natsuwa “

Momy tayi saurin cewa “nizan shiga likita” abba ya juyo ya kalleta, zumudin nan nata bata masa rai yake, ya harareta amma ko a jikinta, bata jira likita yayi maganaba ta tsunduma cikin dakin,
Likita yace ” ita kadai ta isa ku sai kuzauna acen kafin tafarka” ya nunawa abba wuri da hannunsa sannan yafice yabar wurin,
Abba da hilal suka samu guri suka zauna suna jirar farkawar ameelah…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button