AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 49-50

A sandare hilal yakai xaune saman kujira, “innalillahi wa inna ilaihin raju un” itace kalmar dayaketa maimaitawa a bakinsa, Ya tafe qirjinshi da hannu

yana mayar da nunfashi, gumi ya karwo masa, wani irin zafi yakeji a zuciyarsa, saboda tsananin kishi, idanuwansa sukayi jajir,
A hankali ya dora kansa a jikin kujera, ya rufe edo, kalaman dayaji a wayar sukadai ke masa yawa a kwakwalwa,

Cen bayan wasu yan mintuna ya bude idonsa, a lokacin hawaye suka sauka kan kumatunsa, yasa ya share,

Wayar ya dauko yafara duba number, number airtel ce, ya fiddo da wayarsa yayi copy na number, sannan yasaka wayoyin duka biyu aljihunsa, yatashi yanufi dakin ameelah,

wani dinkin atamfa yadauko mata tare da wani katon hijab, sannan yafito,
Saidai ya tsaya ya rufe gidan kam sannan yashiga motarsa, airtel office ya wuce direct yabasu number suduba masa, suka ce masa saiya jira nadan wani lokaci, gudun karsu abba suga yajima baidawowa yasa yabar musu number tare da cemusu zai dawo anjima,

Har a lokacin hilal yakasa dawowa hayyacinsa, jiyakeyi kamar zuciyarsa zasa fashe. Da zaiga wannan mutum da ya kira matarsa daya yayi mummunan saba masa,

Hakadai yakarasa gidan malam mai ruqiyya a bakin kofar gidan kafin yashiga yatsaya ya daidaita kansa domin ba yason su abba sugane yana cikin damuwa, sannan yashiga cikin gidan, ya mikawa momy tunfafin,
Abba da hilal suka fita momy ta chanzawa ameelah kaya, sannan suka dawo suna jiran farkawarta,

Kusan rabin wuni sukayi a gidan, tun cikin dare har safiya ta waye, sai misalin 12:00pm na rana ameelah ta farka, a hankali ta bude ido tana kallon su momy da suke gefe da ita, bakinta na rawa tace "momy ina ne nan meya kawoni nan"

murmushi momy tayi kafin takarsa gurinta tadafa kanta tace “ki kwantar da hankalinki, muna gurin nema miki lafiya ne “

Atsorace ameelah tace “lafiya kuma umma meya faru dani” momy tace ” aike yakamata muyiwa wannan tambayar, meya faru dake a daren jiya ?”

Gaban ameelah yafadi domin ita harta mata da abinda yafaru da ita sai yanzu da momy tayi mata wannan maganar,
Bakinta yadau bari, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, abba da hilal suna gefe suna kallonta, ameelah tace “nima bansaniba “

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button