BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 5-6

Koda ta gama alwalarma sai da ta tsaya ta duba wasu msgs din cikin sauri tayi reply sannan ta fito ta iskeshi yana tsaye yana jiranta saman sallaya.

Bayan sun qare sallar ya dade yana kwararo addu’a yayi mata en tambayoyi akan addini sannan ya jawo musu ledar Abnci, miqewa tayi tace “nidai a qoshe nake brci nakeji sosae, Yace “haba ameelatah, nasan bki qoshi ba ya zaki kwanta da yunwa? Tace “brci nakeji ne sosae, kuma bn iyacin abnci in inajin brci, bata jira me zaice ba ta haye gado ta jawo bargo ta lullube ta fiddo wayarta taci gaba da chat.

Harya gama dk abnda zaiyi yana kashe wutar dakin tayi sauri ta ajiye wayar don kar yaga haske ta kwanta kamar mai barci, Yaa miqa hannu yakai sau biyar da nufin tabata amma baiso ya tasheta dga qarshe dai ya haqura shima ya kwanta cike da tunane-tunane.

Saida ta tabbatar yayi brci sannan ta lallaba ta tafi falo tana sanda, saida ta tsaya ta dauki kazar da lemu don yunwar da takeji, ta zauna tana chatn tana cin abnci har dare ya fara nisa, sai murmushi take ita kadai don ba qaramin dadi chatn din ya matah ba!

Wani sabon frnd ne tayi a whatsapp yaa ita chat sosae, kota mnta da ynzu taa zama matar aurene data dage tana ta chat da maza?

1:40pm na dare hajna tafarka, jinkarar massages yamata yawa, tana chart bacci ya kwasheta ba shiru ta saki wayar akan gado, sai yanzu data farka tashiga laluben wayar, Ameela tagani online abin yayi matukar bata mamaki, Hajna ce tace “wai ke Ameelah ina kka baro Angonne daya barki kina chat first night dnki??

Ameelah tace “kinga nipa bnson iskanci in zamuyi firarmu muyi, miye a cikin chatn din??

Hajna tace “yau pa ne ranarki ta farko a gdan miji kamata yayi ku raya darenku cikin farin ciki ki bashi damar nuna miki soyayyar da yake miki,

Ameela Tace “Yayi brcinshi pa, nima jira nake 3 ta ida inje in kwanta,

hajna tace “tohm ni kinga tafiyatah don har nayi brci na farka amma kinata chat,

Ameelah tace “asha brci mai dadi mu ynxu muka fara. Lokacin hajna ta sauka

Haka taci gaba da chatn dn kusan kwana tanayi, sai da charging ta ya dauke sannan ta saka chajin ta tafi ta kwanta cike da farin ciki, don babu abnda ke saurin sanyata farin ciki kaman chat,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button