AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 3-4

Caraf edonta yafada kan wata number wadda aka rubutawa HAJNA beauty,
Danna cikin sakon tayi ya bude

Hajna ” shegiya ameela bakida dama wato har first night dinki saikinhau chart, ina angon yake daya barki kina chart”

Ameela “hmm?? yana bandaki zaiyi alwala, nima yace nazo muje amma nace masa yaje ina zuwa”

Hajna “tohh to ai saiki tashi kitafi mana, karyazo yasameki kina chart, karfa yafara gane halinki tun yanzu”

Ameela “hmm yanzu kuwa zantashi amma saina duba messages dina na Facebook domin akwai wani da wasan hausa da mukayi dashi zamu hadu 11:00pm kuma kinga yanzu 11 tayi yanzu haka nasan yana jirana”

Hajna ” ?? Ameela haryanzu baki daina kula maza a social network bah”

Ameela tana kokarin mayarwa da hajna da amsa,
Hilal ya turo kofar bandakin ya fito, da sauri ameela tamike tsaye tana sosa kanta,
Kallo daya yamata yagane batada gaskiya, lafiya kuwa ” hilal yafada,
ciken da rashin gaskiya Ameela tace ” bakomai ina duba wani abune a jakata “
Hilal yayi murmushi yana kara nazarin yanayin fuskarta yace, ganin waya a hannunta yasa yagane abinda takeyi “hmm kidaina karya batada kyau ameela, Annabi Muhammad s a w yana cewa alamun munafiki guda ukkune, kuma karya itace abu na farko daya fara fada, sannna kuma karya a duk yadda mutum yayita yana ganin kamar kadance yayi to karya batada kadan, yayi murmushi ganin tayi wani noke kai, yace “kije kiyi alwalar kifito inajiranki”
Bata daga kai ta kallesa ta nufi bandaki cike da kunya,
Tana karasawa bandakin tamayar da kofar ban dakin ta rufe
Takara janyo wayarta tashiga Facebook tana duna text inda akayi mata, sai reapply take musu harma ta mata da alwala tazo yi,
Hilal yana zaune gefen gado yana jiranta, kusan minti goma, shiru ko kukan ruwa bayaji,
Kina inane ” hilal yafada..
Ameela ta zabura da karfi saida wayar takusan faduwa,
Sannan ta daidai kanta ta kunna fanfo tafara alwala,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button