BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 48

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

48

……..Hannunsa daya ɗaga kamar zai mareta ya dunƙule, yanda ilahirin fuskarsa ta canja kammani ya matuƙar girgiza zuciyar Anaam amma ta sake aro jarumatar dole ta baibaye tata fuskar da zuciya da shi.
    “Ita ƙaddarar data kawoki, ita zata dawwamar dake a cikin gidan sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu! idan kuma k kin isa mara kunya ce ƙafarki ta taka ko gate mugani stupid girl”.
    Kafin ta samu damar cewa wani abu ya fice a ɗakin, hawaye ne suka cigaba da rige-rigen sakkowa a kumatunta, zubewa tai a saman gadon ta rufe fuskarta da tafukan hanunta. Taja tsahon mintuna tana kukan kafin kiran daya shigo wayarta ya katse mata shi. Amrah ce, kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga takai kunne batare da tayi magana ba. Daga can Amrah tamkar mai tsoron ajita ta fara faɗin, “Kina jina Anaam?”. A taƙaice tace mata eh kawai.
      “Ke kaɗai ce?”.
Cike da ƙosawa tace, “K dalla faɗi abinda zaki faɗa”.
   “Mtsoww! K daɗina dake masifa. Ina yarinyar na ƙawar Fadwa da muka gansu ranar da aka kai lefen Yaya Maheer?”.
         “Amrah dan ALLAH ki barni wane shirmene wannan?”.
“K Please karki kashemin waya maganace mai muhimmanci wlhy. Ina dai kin ganeta”.
    “Muje na gane, kamar Bibah suke kiranta”.
        “Yes! Exactly ita fa. Kin san yanzu ana tsaka da rigima a gidan nan kin san Mommyn su Yaya Shareff tana nan har yanzu tanata rikicin sai an raba aurenku, na fito daga gida zanje zan shiga cikin gidan kawai naga Bibah ɗin tare da Gwaggo da Maman Bibah a lungun mai shop ɗin nan, shine fa na lallaɓa naje kamar zan sayi abu a shagon, ki duba WhatsApp ɗinki na turo miki voice recording ɗin dana musu dan naga yanzu ma kin fini gane wani hausan”.
      Kamar Anaam zata gwaleta sai kuma tace mata “Okay” a taƙaice ta yanke wayar. Daga can Amrah bata damuba dan ta saba da halin Anaam tun suna yara, sai dai a yanzu ma ta fahimci kamar a cikin damuwa take dan muryarta da alamar tayi kuka.
      Taso share zancen Amrah ɗin amma sai yayta tsunkulin zuciyarta. Data ɗinta ta buɗe tare da shiga in box ɗin Amrah ɗin. Maganar ya ɗanyi ƙasa sosai, da alama ba gab take da su ba. Earpiece ta saka yanda zataji da ƙyau. Maman Bibah ce ta fara magana cikin alamun ɓacin rai.
    _“Amma ba haka kikai min alƙawari ba, kin tabbatar min idan shirinki na zubar da cikin nan na Fadwa ya tabbata da Shareff ya dawo zakiyi duk yanda zaki ya aure Bibah, sai kawai naji wai ga wadda ya aura, kin kuma ƙi saurareni tun ranar ɗaurin auren nan, na kira ta waya Gwaggo da kinji muryata sai ki kashe”.
      Da ɗan zafin rai Gwaggo ta amshe da faɗin, “Haba Luba, wace magana kikeyi haka. Kina zaton zan faɗi abinda bazan cika bane, ai ni na fara miki tayin haɗa Bibah da Mustapha saboda ganin dacewarsu, na kuma tabbatar miki kasancewar Fadwa a gidan bazai hanata shiga ba duk da ƴar uwa take a gurinta itama. To amma su Muhammadu sukai wannan sarƙa-sarƙar da kema kin san gwagwarmayar da aketayi na hana faruwarta. Ba yin kammu bane, kuma bamu san sun ɗaura auren nan ba. Amma ki kwantar da hankalinki, ni bana rama alkairi da sharri, Bibah kamar ta shiga gidan Mustapha ne ta gama. Yanzu dai kuje gida zanyi duk yanda zan a satin nan na leƙi gidan naku kinga wani zai iya ganinmu anan, kuma za’a iya zargin wani abu shiyyasa ma nace kada ku ƙaraso gida mu haɗu anan”.
      Mamaki, al’ajabi, ruɗani duk suka dirga a zuciyar Anaam lokaci guda, ba komai ta fahinta a zancen ba, sai dai maganar zubar da cikin Fadwa da su Bibah suka bata shawarar yi ta fahimci cewar Gwaggo ce ta sakasu su bama Fadwa shawaran kenan, sannan Bibah ma son Shareff take kuma Gwaggo ta mata alƙawarin samunsa matsayin miji duk da da wadda ta haifi mahaifin Fadwa, da maman Mommyn Shareff, da Kakar Bibah wadda ta haifi Mamanta da Gwaggo uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Kai kai kai wannan makirar tsohuwa da abin mamaki take, ta ƙyalƙyale da dariya dake tabbatar da ƙunar zuciyarta a bayyane. Cikin bushewar zuciya da cin alwashi ta jinjina kanta.   
        “Yes bazan tafi ba, amma Yaya badan kurarinka ba, sai dan koyama matarka da Mommy da aunty Halima hankali har da kai kanka a dalilin tsohuwar banza Gwaggo, yanzu na ƙara fahimtar matar nan itace take ƙulla komai dake a family ɗin nan tabbas. Zan tabbatar mata Karen bana! Shike maganin zomon bana kuwa..

      Bayan sallar la’asar sai gasu Amrah, tayi farin ciki da zuwansu matuƙa, musamman Ikram mai shegen surutu da bakinta baya shiru. Suka shiga buɗe kulolin abinci dake a falon wanda ita bama tasan da su ba, sai dai kai tsaye ta gane Fadwa ce ta kawosu tana ciki. Koda suka tambayeta ita ta dafa? Kai tsaye tace musu matar gidan. Amrah dai kasa ɓoye mamakinta tai sai da tace, “Wai kina nufin Fadwa?”.
      “Bayan ita akwai wata matar ne a gidan?”. Ta faɗa batare data kalli Amrah ɗin ba. Harararta Amrah tai da faɗin, “Banza kefa idan kina kan dokin zuciya ba’a maganar arziƙi dake”. Shiru Anaam ɗin tamata hankalinta na kan hotunan su Gwaggo da Amrah ta dauka. Dukansu ta tura cikin wayarta, daga haka suka cigaba da hira.
      An fara kiran sallar magrib Shareff ya shigo, fuskarsa murtik da alama har yanzu ransa a ɓace yake. Ikram ta sheƙa da gudu garesa dama tun ɗazun take tambayar yana ina Anaam ta mata shiru. Ɗaurewar fuskar ya ɗan sassauta yana shafa kan Amrah.
    “Autah yaushe kuka zo?”.
Hanunsa cikin nata tana murmushi tace, “Yaya tun around Four. Inata tambayar aunty Anaam kana ina? Taƙi amsani”.
       Kallonsa ya kai ga Anaam ɗin, anyi sa’a itama ta ɗago nata idanun a lokacin. Janyewa tai cikin salo tana ɗan taɓe baki, shima sai ya janye nasan yana ayyana (Zanyi maganinki ne) a ransa. Gaishe sa su Amrah sukai, ya amsa musu yana ficewa da basu umarnin tashi suyi salla. Bai dawo gidan ba sai da aka idar da sallar isha’i. Kai tsaye nan ya zarto domin maida su Ikram gida. Anaam jitai kamar karsu tafi, tai musu rakkiya har wajen motarsa, sai da taga ficewarsu sannan ta nufi komawa suka kusa cin karo da Fadwa.
      Kallon kallo sukema juna, Fadwa ta saki siririyar dariya tanama Anaam kallon sama da ƙasa. “Amarya! Amarya! Ta ango baƙya laifi ko kin kashe ɗan masu gidaaa hhhhh. Uhhm kamar haka ake kirarin ko?”. Tai maganar cikin sigar tambayar rainin wayo ga Anaam dake kallonta ita dai. Dariya Fadwa ta sake kwashewa da shi “Oh sorry amarya, ALLAH kina bani tausayi, dan ban taɓa gamo da amarya irinki ba ko’a hikayoyin marubuta. Dama tsiyar auren cushe kenan fa”. Ta ƙarayin ƴar dariya da matsowa gaban Anaam dake kallonta uwa ta samu tv ko bata fahimtar yaren da take magana da shi. Cikin yin ƙasa- ƙasa da murya murmushi shimfiɗe a fiskarta ta cigaba da faɗin, “Zan baki shawara ƙyauta dana tabbatar zatai miki amfani ƴar turawa, karki bari ki zubar da ƙuruciyarki da lokutanki masu muhimmanci a inda ko kallonki ba’a da bukatar yi, gara ki taimaki kanki, ki tattara komatsanki kibi tsoffinki ku koma inda kuka fito koda baki gama serves ɗin ba, koda yake dama mun san bashi akazo yiba neman miji akazo. Bokanku ya iya aiki tunda gashi kin samu ta hanyar cushe, sai dai kuma akwai matsala mai yawa dan basu jehoki gurbin daya dace ba, gara ki sani tun yanzu, wannan gidan sai ya zame miki tamkar kurkuku mafi muni da ƙuntata a rayuwarki, kina da zaɓin taimakon kanki ko cigaba da zaman cin kwakwa, AL-Mustapha Muhammad Shareff anyisa ne domin Fadwa Sadiq Dakata kawai”. Ta kare maganar da ƙyafta mata ido.
       A karon farko Anaam ta saki murmushi tana girgiza kai. “Hauka maganinka ALLAH, ke kuma sanyin da wannan yanayin yazo miki. ALLAH ya ƙara afuwa”. Tai gaba abinta.
    “Ubanki ne mahaukaci ƴar iska”.
Anaam ta cigaba da tafiyarta tana dariya batare data waiwayita ba. A falo ta zube maganganun Fadwa na dawo mata ɗai-ɗai cikin amsa kuwwa. Tabbas bata da burin yin dogon zango a zaman gidan nan, sai dai ya zame mata dole zaman a yanzu kodan kawo ƙarshen makircin Gwaggo, na biyu zata cika burin iyayenta akan zumincinsu da suketa ƙoƙarin ganin sun toshe duk wata hanya da zata wargazashi. Na uku Fadwa, dolene ta koyama Fadwa hankali ta kuma tabbatar mata sufa Mata suna suka tara lokaci shi zai nuna Zarah. Na huɗu Mommy, na karshe Shareff, zata tabbatar masa da cewar ita ɗin ba kanwar lasa bace, daga shi har matarsa sai ta goge musu hadda a cikin gidan nan…
      Ta saki murmushi a karon farko bayan ta kammala rubuta dukkan abinda ta gama lissafawa a cikin wayarta sannan ta mike. A dai-dai nan ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Itama ciki-cikin ta amsa masa tana ƙara tsume fuska. Shima dai tasa fuskar a tsuke take, ya ajiye ledar hanunsa yana kallonta tamkar mai harara. “Shi wancan ɗakin da kika bari babu gyara waye zai gyara miki?”.
       Shiru kamar bata jisa ba, ya sake dubanta a harzuƙe.
      “Baki jini bane?!”.
    Baki ta tura gaba, cikin magana ƙasa-ƙasa da tunanin bazaiji ba tace, “Matar taka ta gyara maka mana”.
    “Tunda ita ta kwanar miki a ɗakin ko”.
Kallonsa tai, dan batai zaton yaji ba, ta kauda idanunta da sauri ganin kallon da yake mata. Ƙafa ta ɗaga da nufin barin masa falon cafka ɗaya ya fisgota ta dawo gabansa. Marmar ta farayi da idanu da ƙyaƙyƙyaftasu, ta fara mutsu-mutsun ƙwacewa ya murɗe hannun. Ƙaramar ƙara ta saki da ƙanƙame masa hannu ta fashe da kuka. “ALLAH zai sakamin, kuma wlhy komi kamin sai na sanar da su Daddy…”
      “Bakin ki bazai mutu ba kenan?”. Ya faɗa da ƙara matse hanun. Wata muguwar wawura ta kaima hanunsa ta ƙallara masa cizo a ƙaramin yatsansa……….✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button