BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 9-10

Ameela tace “to shikenan mekakeso nadafa maka idan kadawo”
Hilal yace “basai kindafamin komaiba, zan siyo abinci nazo dashi idan dai ke kinada bukata kidafa kici,.na janye miki girki harzuwa nan da sati daya, ya durkusa yana kokarin saka takalmasa cover shoes, bayan yakarasa sakawa yace “to ni zan wuce, ki kularmun da kanki saina dawo” bai jira tayi maganaba yafita yabar dakin,

Bayan fitarsa ameela tayi ajiyar zuciya sannan takarsa bakin drowar tadauko hijab dinta tafara sallah,

 Bayan takarasa sallah, dasauri tatashi babu ko adu' a, tafita falo (najuyo na kalli abdul nace ina kuma ameela xataje ko adu'a batayi ba, Abdul yace nima ina nasani kawai dai musa ido mugani)

Da isarta falo ta nufi gurin data saka chaji jiya wayarta tadauko, ta kunna domin akashe take,
Bayan wayar ta bude, tadan tsaya tana kallon wayar cen taji messages sun fara shigowa, daman DATA dinta a kunne take tunjiyar da wayar tadauke,

Wayar tacika full chaji, ta sance wayar a daga chaja, takoma daki, saman gado tazauna tafara bude massages dinta,

Whtsapp tafara shiga, edonta yafada kan wata number data rubutawa HMM, image taga sunshigo acikin sakon number, da sauri tafara download dinsu, pic ne guda ukku, suka bude wani hadanden guy ne yasha wanka, ga makemen gilass a fuskarsa, a hankali bakinta yabude tace “wow, guy di ba laifi”

A kasan image din anrubuta “ganawa pic nan dan Allah kituromin naki”
murmushi kawai tayi taci gaba da dundunba masseges dinta, cike da farin ciki tanai musu reapply,
Tafi kusan minti 30 tana chart sannan tatashi ta ajiye wayar tanufi bandaki tayi wanka, tafito, tanufi gaban mirror tafara chaba ado,

Abinka ga kyankyawa bawani jimawa tayi tana mek up dinba, ta kammala tayi masifar kyau tatsaya tana kallon kanta a madubi, tana murmushi, a lokacin ne kyanta yakara bayyana, (sakin baki nayi ina kallon wane irin kyaune ga ameela aiko a cikin indiyawa aka kaita tsaf zata sare dasu, gab naji a dakeni tabaya a firgice nadawo daga duniyar tunanin dana shiga nakama bakin alkalamina naci gaba da rubutu “

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button