Labaran Kannywood

An bayyana Bikin Halima Atete a daya daga Cikin Manyan Bukukuwan da Jaruman Kannywood Sukafi Halartarsa Kuma Suka Nuna Kara

A jiya asabar ne aka daura auren Fitacciyar jarumar Kannywood Halima Yusuf wacce akafi sani da halima atete tare da Angonta me suna Muhammad Muhammad Kala.

Duk da cewa tun farkon da aka fara wallafa katin bikin jarumar Cece kuce ya balle a shafukan sada Zumunta inda yawancin mutane suke tamabayar cewa amma wannan shine karo na biyu da jarumar zatayi aure.

Domin Duk Tsawon Shekarun nan Wasu suna mata Kallon bazawara ne ba Budurwa ba.  Hakan yasa wasu daga cikin Abokan sana’ar ta sukaita maida martani wa wanda suka bankado wannan Tambaya.

A yau lahadi ne aka kammala Dukkan shagulgulan da sukai saura na bikin jarumar a garin Maiduguri…. Sai dai an yabawa Jaruman Kannywood matuka ganin yadda sukai tattaaki har izuwa garin na Maiduguri domin nuna farin cikinsu ga Abokiyar Sana’ar su.

An hango Fuskokin Manyan Jaruman Kannywood irinsu Adam Zango, Hadiza Gabon, Maryam Yahaya, Maryam ceeter da dai Sauran su wanda duk da sune aka gabatarda wannan Shagulgulan biki.  Ga Wasu daga cikin Hotunan karshe da aka dauka na a wurin Shagalin bikin

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button