Labaran Kannywood

Anyi Kira ga Ali Nuhu ya daure ya duba Lamarin wata babbar Masoyiyar Shi dake ta Wahalar Son ganin shi amma Yaki Kulata.

Anyi Kira ga Ali Nuhu ya daure ya duba Lamarin wata babbar Masoyiyar Shi dake ta Wahalar Son ganin shi amma Yaki Kulata.

Wata Budurwa wacce akafi sani da Mrs Ali nuhu kuma babbar Masoyiyar Jarumin ta bawa kowa mamaki duba da irin kaunarda take mashi hakan nema yasa ta canza sunan ta izuwa mrs Ali nuhu.

Kamar dai yadda kowa ya sani Jaruman Kannywood suna da masoya da dama, bama jaruman Kannywood kawai ba dukkan wani jarumi ko tauraro wanda yayi suna to yana da Masoya.

To amma wasu sukan zafafa Soyayyar da suke yiwa jaruman tafi ta kowa wanda hakan kesa har jaruman susan da zaman su koda kowa ba zasu kulasu ba a lokacin.

A kwanaki biyun nan ne jarumi Adam zango ya kira wata babbar Masoyiyar shi a waya wacce akafi sani sani da giwar mata, tayi farinciki matuka da kiranta da yayi domin ba ita kawai ba harma Mahaifiyar ta saida suka gaisa dashi. Ganin yadda take Matukar kaunarsa yasa aka nemo mashi numbarta ya kuma kirata da kanshi.

Hakan yasa mabiyan ta a shafinta na Tiktok suka bayyana cewa so take kawai jarumin ya aureta domin sonda take mashi ya wuce misali. Sai dai kuma ta fito ta karyata hakan inda take cewa ita bada aure take sonshi ba amma kuma idan har shida kanshi yace zai aureta to tabbas fa babu abinda zai hanata amincewa.

Giwar mata tayi farinciki sosai domin ta bayyana cewa takai Kimanin Shekaru uku ta neman haduwa da gwanin ta watau adam zango amma hakan bata samu, sai gashi shida kanshi ya kirata a waya.

Hakan yasa wasu Sukayi kira ga jarumi Ali nuhu kan shima ya daure ya duba Lamarin Budurwarda saboda kaunar shi harta dan gana sunan ta da nashi.

Budurwar tayi kaurin suna a kafar sadarwa na TikTok domin kusan duk bidiyoyin ta da takeyi Maganar dai bata wuce ta Ali nuhu, Sai dai kuma har yanzu jarumin baiyi magana ba akan lamarin

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button