Labaran Kannywood

Sabuwar rigima, Nafisat Abdullahi ta karyata Fati Washa akan cewa ita daman can akayi niyar sakawa a shirin LABARINA a matsayin Sumayya

Babbar jaruma a cikin masana’antar Kannywood wadda aka jima ba’a ga fuskarta ba a cikin shirye shiryen da ake yi a masana’antar tun bayan rigimar ta dasu Naziru Sarkin Waka a kan fim din LABARINA mai dogon zango.

Fati Washa a cikin wani shiri da Hadiza Gabon take gabatarwa data gayyace ce ta.

Hadiza Gabon ta budi baki ta tambayi Fati Washa,Ya akayi ta tsinci kanta a cikin shirin LABARINA series?

Rufe bakin Hadiza Gabon keda wuya Washa din tace ai tun kusan shekarar 2020 Malam Aminu Saira ya nemi su Zauna,har ta kai sun zauna suka tattauna,har ya kai wa yanzu da aka fara ganinta a cikin shirin.

Sannan bugu da kari jarumar tace ai ita ce akaso ta fito a shirin tun a shekarar 2016,amma saboda Nazifi Asnanic yace gwanda a saka Nafisa Abdullahi saita fi kyau da dacewa da shirin.

Haka dai bayan bayyanar labarin a shafin Twitter,shafin Labaran Kannywood ya rawaito wannan labarin kamar yadda mukayi bayani a sama,nan kuwa bayan Rahama Sadau ta gani saita kyalkyale da dariya.

Itama Nafisat din sai tayi dariya ta rubuta a harshen Turanci “Lol,is that what they told her? So she could do the show? Ok ooo 

Fassara: Hmm,au haka suka fada mata saboda taji dadin bayyana a shirin? To ai shikenan. Inji Nafisat Abdullahi din.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button