BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 16-20

Page 1⃣6⃣ to 2⃣0⃣

cigaba da sallan ta tayi amma gabadaya rabin hankalinta yana kofar daki inda haladu ke tsaye yana ta surfo ruwan ashariya,kiran da ya kwalo mata ne yasa ta kara firgita amma fa duk haka bata katse sallan ba.cizge labulen bakin kofar yayi yana fadin ina wannan shegiyar tayi… cak ya tsaya ganinta tsaye tana sallah,kan uban can yace da karfi wanda yayi sanadiyyar fitowar inna asabe daga cikin daki..dan dama tana jinsa kyaleshi kawai tayi ya gama na shi kafin ta dora nata,shiga cikin dakin yayi tare da fincikota ya wurgo ta waje kamar kayan wanki,,ita dai jiddah baiwar allah ba bakin magana dan tasan yau allah ne kawai zai iya ceton ta a hannun azzalumi haladu..shigowar indo da talatu ya katseshi tare da cewa yauwa kunzo a daidai kuzo ku cimin uban wannan zabayar,,shewa suka sa a tare dan dama su kamar jira suke,,hakuri jiddah ta fara bashi tare da fadin kayi hakuri inna ce ta sani ayki….ai bata karasa ba asabe ta kai mata naushi a baki tana fadin”kujimin yar iska zata min sharri yaushe na saki aiki ina ce hijabi kika zara kika tafi gun wannan tantirin yaron,yau saikinci ubanki a gidannan..dukan su suka rufu akanta suna dukanta kamar sun samu jaka da kansu suka gaji suka kyaleta,,ita kuwa jiddah baiwar allah a wannan lokacin bata da bakin magana domin bakinta yayi suntum jikin duk ya farfashe sai sheshshekar kukan ta ke tashi,,daga inda take tana jiyo shewar su a can kuryar dakin inna asabe.suna yi suna cin naman da tasha wahala gun dafa shi”da kyar ta samu ta rarrafa ta shige cikin daki akan katifar ta kwanta wadda bata da maraba tsumman gogegoge ta kwanta,,kafin kace me zazzabi ya rufeta dakyar ta jawo hijabinta ta lullube tana mai kara tausayin rayuwarta,,

a bangaren ammar kuwa baccin shi yake cikin kwanciyar hankali kiran sallah la’asar ne ya farkar dashi daga baccin da yake,domin kuwa duk iya shegen ammar baya barin sallah ta wuce shi gashi da tausayi.amma fa idan ka shiga gonar shi to fa ba mutunci

sai da ya idar sallah sannan yayi cikin gidah umma ce hakimce a falo tana kallon tv tana jefa fruit a bakinta,,wucewa yazo yi ta gabanta ko kallon inda take bai yiba,,babanka na hanya gobe,, juyowa kawai yayi ya kalleta kafin ya wuce..da harara ta bishi kafin tayi kwata ka kusa kama gabanka ai,,shidai baima samd tanayi ba..kicin ya shiga ya dakko abincin sa ya fice daga sashen gaba daya,,,yana gama cin abinci ya shiga wanka be dade ba ya fito shiryawa yayi cikin wasu riga da wando rigar me dogon hannu ce wandon kuwa jeans ne amma duk amma sa crazy,wata sarka ya jawo me uban nauyi ya dora ta a wuyanshi..sannan yasa pcap a kanshi,,ya fito a dan dabanshi sak amma hakan bai hanashi yin kyau ba..ficewa yayi a gidan a 360,,,

kiran sallah magribtne yasa ta mikewa dakyar ta rarrafa ta dauki buta alwala tayh kafin ta kara komawa cikin dakin dakyar ta samu tayi sallan ta kara komawa ta kwanta dan har yanzu zazzabin bai sake ta,,tana jiyo hayaniyar inna asabe da yayanta dan dama su sallah ba damun su tayi ba ,,kwala mata kira taji anayi kuma muryar inna asabe ce..cire lullubin tayi ta maida tasa a jikinta sannan ta nufi kofar dakin,,sallama tayi ba wanda ya amsa a cikinsu.sai wurgo mata kudi indo tayi tana fadin wuce ki siyomin pad a shagon sile bana son na shagon rabe,toh kawai tace tare da amsar kudin tayi hanyar waje,tafiya take kamar zata fadi amma haka ta cigaba,,

fitowar shi kenae daga masallacin su uku ne ammar auwal da kuma nura,tafiya suke da sauri domin time din wasansu ya fara,,tun daga nesa yake hangota tana tahowa a yanayin daya ganta yasa fuskar shi sauyawa,ina zuwa yace ma su auwal kafin ya isa inda take kallonta yake tun daga sama har kasa,dagowa tayi tana murmushin dole wanda yafi kuka ciwo,,waya miki haka kawai ya ce dan sai data dago kanta sannan yaga bakin ta a fashe ga kuma idonta daya kumbura,,kan uban can yace da karfi tare da zaro mata idanu,, tambayarki fa nakeyi yace a hasale,,a hankali ta fara fada mai abinda ya faru tare da fashewa da kuka,,,,,kutumar uba yau sai naci uban uban asabe sai na karya wa haladu kafa,,kai yau duk wani daya shafh asabe sai mun mai operation huci kawai yakeyi a lokacin da zai ga su haladu ba abinda zai hana bai cire ma tsohuwar nan da yayanta kafafuwa ba,,,maganar dayake da karfi ne ya janyo hankalinsu su auwal dama sun tsaya saboda karsu damesu,,, auwal yace yadai my man dogon tsaki yaja kafin ya basu lbrn abinda ya fara,,,,yeeeehuuuu,,cewar auwal kace yau anta bomu tunda aka taba jidda kai nura jeka tattaro su duna da bahago dukakasu da sauri nura yayi hanyar barin wajen domin cika aiki,,kara kallonta ammar kafin jeki gidan maman sahala zanzo in sameki,,,,

Toooh yaufa su inna asabe an taro pillars

yawan comment yawan typing

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button