BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 16

16

………“Ita kuma f…”
Bai karasaba Abie ya bashi amsa da faɗin, “Mamana Juwairiyya (Anam)”.
    “Woow masha ALLAH! Masha ALLAH. kace ɗiyar tawa ma ta girma ashe. Damma ƙaramin jiki ya ɓoye shekarun”.
        Gaidashi Anam tayi batare data sake yarda ta kallesu ba, ya sanya mata albarka itama da mata sannu akan ciwonta tare da addu’ar samun sauki. Su Maheer suka amsa da amin, banda Shareff dake ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihun wandon jeans ɗin jikinsa da kira ke shigowa. Saurayin ya karaso gabanta idonsa ƙyam a kanta ko ƙyafatawa bayayi. Ɗagowa tai itama ta kallesa. Ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗaɗa murmushinsa. Cikin ɗan rankwafowa da murya can ƙasa yace “Kona ɗaukeki da kaina”.
       Kanta ta girgiza masa tana satar kallon su Abie da Shareff dake waya duk da idonsa baya kansu, amma abinda bata sani ba kunnensa sarai yaji masa abinda saurayin ya faɗa. Shima ɗan janyewa yay daga kusa da ita ya mikama Shareff daya gama wayar hannu. Fuska ɗauke da murmushi yace, “I’m Muzzaffar Abu Kalla”.
     Cikin ido ya kallesa da ƙyau. Ganin su Abie a wajen ya sashi yarda ya mika masa nasa hanun kamar mai ciwon baki yace, “Al-Mustapha Muhammad Shareff”.
      “Nice name and nice to meet you”.
“Same”.
Shareff ya faɗa a takaice yana janye hanunsa. Muzzaffar ya mikama Maheer shima suka gaisa. Hakan yayi daidai da fitowar Aysha. Itama gaidasu tai su duka cikin girmamawa. Shareff yace ta kama Anam su shiga ciki. Sai da yaga shigewarsu sannan shima yayma abokin Abie sallama ya shige batare daya sake kallon sashen da Muzzaffar yake ba. Ganin haka shima Maheer yay musu sallam yabi bayansa.
       Kai tsaye sashen Mommy suka nufa saboda kiranta dake ta faman shigo masa a waya, duk da kuwa ya ɗaga na farko ya tabbatar mata suna ƙofar gida zasu shigo yanzun. Amma ta kasa haƙuri da tunanin suna raina mata wayone kawai. Da sallama suka shigo falon, har yanzu tana tsaye sai faman kai kawo take kamar an bata gadin kayan falon. Babu zato babu tsammani ƙarar lafiyayyen mari ya shiga bada ƙarar amsa kuwwa a illahirin falon. Maheer ya dafe kuncinsa wata azaba na ratsashi, wani ta sake kifa masa a ɗayan kuncin nasa. Cikin huci mai nuna tsananin ɓacin rai take nunasa da yatsa. “Wannan kaɗanne namaka daga cikin abubuwan dana tanada maka inhar rayuwarka bata nisanta da jinin Usman da Maryam ba anan gidan wlhy wlhy Maheer…..”
         “A wane dalili rayuwarsa zata nisanta da jininsa data kasance dolensa kenan Nafisa?”.
Muryar Daddy da basuyi zato ko sanin yana biye da su ba ta karaɗe kunnunwansu, ya dakatar da Mommy dake ƙoƙarin juyawa ga Shareff da mutuwar tsaye ta samesa sakamakon marin da Mahaifiyarsu ta sakarma ɗan uwansa na bazata
“Nafisa! Wai miyasa akoda yaushe kike son nuna ƙarfin iko akan ƴaƴanki wajen wargazamin zuri’ata? To bara kiji, na rantse da ALLAH, daga ranar da tunanin ƴaƴanki ya fara sauyawa zuwa shiga hurumin zumincina da ɗan uwana ko iyalinsa kamar yanda kike ƙoƙarin yi, zan tabbatar da shigarki nadama irin wadda bakiyi tsammani ba daga gareni. Idan kuma kinaga bazan iyaba saboda ɗaga miki kafa danai na tsahon shekaru ku ku gwada aikatawa ku gani”. Ya ƙare maganar da nuna su Shareff cikin tsananin ɓacin rai tare da juyawa ya fice batare da ya jira cewar waninsu ba.
       Daga ita har su da kallo suka bishi. Wani irin ɓacin rai na nuna kansa a fuskar Mommy. Ta watsama su Maheer wani mugun kallo batare data sake cewa komaiba itama tabar falon. Da kallon dai itama suka bita harta shige, Yaya Shareff ya sauke nannauyan numfashi da maida kallonsa ga Maheer, kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi, dan fuskarsa duk tayi sayin yatsun Mummy.
       Cikin ɗacin murya Maheer dake kallon yayan nasa ya ce, “Amma Yaya Mommy……”
     Kai ya jinjina masa alamar baya son jin komai, ya ɗan ƙara bubbuga kafaɗarsa tare da ɗan hugging nashi ta gefe sannan ya fice. Maheer ya bisa da kallo….
         Mommy da duk ke tsaye a bakin ƙofarta tana kallonsu tai ƙwafa. A ranta kuwa babu abinda take ƙullawa sai tabbatarma Daddy bataji maganarsa ba. Dan kuwa ko ana ha maza ha mata sai ta tabbatar da ƙiyayyar maƙiyanta a zuciyar ƴaƴanta ya jima baiyi abibda ya ɗauka alwashin ba. Iyaka dai yace ya saketa ko! To sai me, ko rabuwa tai da shi ta san yanzu Shareff da Maheer sun taka matsayin da zasu iya riƙe rayuwarta fiye da shi. Hussaina dake daga ɗakinsu tana sauraren komai itama ta ƙwalama kira, da sauri ta iso tana faɗin, “Gani Mommy”.
      “Ki bimun Yayanku kiga ya tafine ko ya koma can gidan”.
   “Okay Mommy”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa. Maheer ma yabar falon, dan haka ta fita da saurinta sai dai kuma dole tayo baya ta ɓuya dan hango yayun nata a tare. Yaya Shareff na waya ne, sai Maheer tsaye a gefensa alamar jira yake ya kammala.
        Wayar ya sauke bayan yayi sallama da Dr Jamal. “Miya faru kuma?”. Ya faɗa cikin kafe Maheer da idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya. Shima Maheer ɗin kallonsa yake rai ɓace. “Ni zanje na ƙara duba Anam yanzu, dan bazan iya ƙinyin hakanba gaskiya”.
      Wani irin murmushi da Maheer ya kasa bama fassara Shareff ya saki, sai kuma ya ɗago yana dubansa cikin ido “Brother be careful!”. Ya faɗa murmushin fuskar tasa na ɓacewa.
         Da kallo mai ƙara harzuƙa zuciya Maheer ya bi Yayan nasa, dan tuni harya bar wajen ya nufi gate. Cikin dakewa itama Hussaina tazo ta wuce sa kamar aikenta akai, a mota ta samu Shareff, yana kwance cikin kujera idanunsa a lumshe, a can gefe ta ɓuya tana kallonsa, ya kai kusan mintuna goma a wajen kafin yayma motar key yabar anguwar. Juyawa tai ta koma gida, bata samu Maheer a inda ta barsa ba, dan haka takaima Mommy bayanan data aiketa. Jin Shareff bai shiga gidan su Anam ba yasa Mommy sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai dai acan ƙasan ranta ta gama shirya makaman yaƙar su Mamie ta yanda inhar suka tashi tafiya sai sun wuce da ƴarsu wucewar da har abada bazata sake leƙo Nigeria ba balle ta raɓu mata ƴaƴa.

★★★

       Duk da ta faɗama Mommy damuwarta hankalinta bai kwanta ba. Sai faman kaikawo take na neman mafita. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran biyu daga cikin ƙawayenta da tafi aminta da su. Cikin sa’a kuwa dukta samesu, umarnin suzo gareta ta bada kai tsaye kai kace itaɗin haihuwarsu tai. Babu ko wanda ya musa mata saima tabbatarwa kafin mintuna shafiyar data basu zasu iso.
     Hakan kuwa akai, dan mintuna goma sha biyu bai gama cika cif ba Sima da Amal suka iso. Amal da Sima ƴaƴan talakawane fitik, sun haɗune da Fadwa a media. Komai tayi a shafinta na istagram cikin yabonta da mata Comments suke, idan wani ya zageta zasu haƙiƙice wajen kareta koda kuwa akan gaskiya aka zagetan. Waɗan nan garkuwa da suka dinga bata yasa ta fara kulasu har takai da sun haɗu a zahirin rayuwa. Da farko ganin su ba ƴaƴan kowa bane yaso sakata ja baya da su, sai kuma hakan ya gagara dan suna taka rawar gani a duniyarta ta yanar gizo sosai. Dole ta buɗe bakin aljihu wajen gyara su Sima ɗin ta hanyar siya musu kayayyakin sawa da kaisu wajejen gyaran jiki na manyan yara. Maimakon ƙananun man bleaching da suke shafawa saita ɗaurasu akan manyan harka masu tsada, dan ita Amal ma allura akai mata. Cikin ƙanƙanin lokaci ta canja musu rayuwa suka fara karo da manyan yara. Fadwa nada wasu ƙawayen bayan su Sima dan ita macece mai yawan kwashe-kwashen ƙawaye, ita da mafi yawan ƙawayenta sunyi matuƙar suna a media musamman tiktok a yanzu dake taka rawar gani a rayuwar yaranmu. Komai na rayuwar Fadwa da ƙawayenta a bayyane yake, duk inda zasu samo location ko baground ayi vedio bai musu wahalar zuwa koda a wajen kano ne. A ɓangaren lalacewa bazamuce dukansu a lalace suke ba, dan kuwa akwai wanda a cikinsu da yawa babu ruwansu da mazan inba a ɗan ɗauka vedio ba ko abota shikenan. Fadwa na ɗaya daga cikinsu, dan tunda ta tashi Shareff kawai take gani a idanunta da soyayya. Hakan yasa duk haɗuwar namiji ko kuɗinsa bai cika zama a gabantaba inba wani abun hanunsa take buƙata ba, tana samu kuma zata watsar da shi a wuce wajen. Duk kuma tanayi cikin taka tsantsan da Shareff baisan hakan ba. Hatta harkar media ɗinta Shareff bai sani ba kasancewarsa mutum da yafi damuwa da aikinsa fiye da komai, idan ka gansa a yanar gizo akan abinda ya shafi cigaban rayuwarsane ba kalle-kallen banza ba, sai ko ganin labarai masu muhimmanci da yafi ziyartar irinsu bbc koya zauna ya kalla a talabijin ma yafi masa sauƙi. Amma a wani lokaci Fharhan ya taɓa masa shaguɓe da tsiyar da Fadwa ke tsulawa a yanar gizon harya nuna masa wani vedio. Ransa ya ɓaci matuƙa duk da iyayensune suka matsa ya auri Fadwa tun baya kulawa haryaji ya fara sonta saboda son da take masa bana wasa bane. Sosai ya mata faɗa da gargaɗi harda barazanar barin rayuwarta inhar ya sake ganin wannan shirmen banzar daga gareta. Tayi kuka da alƙawarin dainawa a lokacin har sai ta baka tausayi. Daga haka bai sake bin diddiginta ba dan baida wannan halin sam ga waninsa, ya daiyi imanin yanda yay mata insha ALLAH bazata sakeyi ɗin ba. Sai dai kuma ba hakan bane, dan kuwa ko sati biyu kasa cikawa Fadwa tai saboda ta riga ta saba, amma tabi shawarar ƙawayenta ta samu Fharhan har gida tai masa cin mutunci da gargaɗi bayan ta gano shine ya nunama Shareff vedion. Daga haka ta cigaba da harkokinta sai dai cikin taka tsantsan. A ɓangaren shaye-shaye kam basa shan komai sai shisha da yaranmu suka maida fashion a yanzun, wanda ta koyane shima wajen wata ƙawar tata har su Sima suma suka koya a wajenta…
      “Baby Fady mike faruwa duk kin tada mana hankali?”.
    Amal ta faɗa cikin nuna tsananin damuwa da tashin hankali.
   “Miyema bai faruba Amal. Na tsaneta, na tsani yarinyarnan fiye da mutuwata amma Soulmate ya kasa fahimtar hakan. A yanda nakeji ALLAH zanfa iya kasheta ma….”
         Idanu duk suka zaro na tsorata da kalamanta. Cikin girgiza kai da tarar numfashinta Sima tace, “Kinga nutsu kimana bayani yanda zamu gane Please. Wacece? Miye haɗinta da mijinki kuma da har ya kasa fahimtarki?”.
   Maimakon amsa saita fashe musu da kuka. Hankalinsu sake tashi yayi, suka zagayeta suna lallashi. Sai da tayi mai isarta sannan ta fara basu labari. Da farko sun yabama salonta na kissing mijinta gaban Anam. Daga ƙarshe suka nuna tsantsar takaicinsu da biyema yarinyar da su Shareff sukai na yarda da wai taji ciwo.
    Sima tai murmushi tana kaɗa kai da taune lips. “Karku damu inada shawara, wadda nasan inhar kika bita Fady har abada yarinyarnan sai ta fita rayuwarki, nifa tun randa muka haɗu da itan nan a Saloon tare da shi nasan yarinyarnan ba ƙaramar ƴar bariki bace, sai da kika sake sanarmin haihuwar turai ce tashin can na ƙara tabbatar da e lallai hasashena nakan hanya ashe. To a wannan karon aurensa kike, dolene kiyi komai domin ki rabata da mijinki dama hanyar gidanki gaba ɗaya……”
      “Nifa wannan dogon bayanin naki ya isheni Sima. Dan ALLAH ki faɗa kawai ina saurarenki”.
   “Hhhh daɗina dake wutar ciki Baby Fady. Kwantar da hankalinki, indai dan wannan yarinyar ce mai kama da ƴar tsanar roba kisa a ranki zamaninta ya shafe a duniyarki zo muje daga ciki”.
     Bedroom ɗinta suka shige, suka shiga famfata tako ina. Sun ɗauka kusan mintuna arba’in kafin su fito fuskarta washar da murmushi kamar ba’itace a birkice ɗazun ba. Ganin har lokacin Shareff bai dawoba ta sakasu su gyara mata gidan. Duk da yanda ta sakasu aikin cikin bada umarni ya sosa musu rai haka suka zage suka hau mata gyaran lungu da saƙo, itako tana zaune a falo tana duba Comments na sabon posting da tai ɗazun a tiktok kafin su Anam suzo. Dan danan ko ina ya ɗau ƙamshi. Ta nuna musu jin daɗinta, amma duk da haka sai ta sakasu su mata girkin dare kuma tare da gyaro sashen Shareff. Kowacce da hanzari ta amsa ita zata gyara sashen Shareff ɗin. Hararsu ta shiga yi, sai dai kuma batare komaiba.
     Da sauri Amal ta waske da faɗin, “Na fahimci kowa girkinne bayaso, to muyi girkin tare aje a gyara can ɗin tare”.  Sima tace, “To hakan yafi kam”. Sai a lokacin Fadwa tai dariya da faɗin, “Duk zame-zamenkun dai sai kunyi, inba hakaba na fasa sayen ashoben Meerah ɗin”.
    Suma dariyar suka shigayi da faɗin ai ba’ayi hakaba duk zasuyi. Hakan kuwace ta kasance. Sukai mata girki tare da gyaro sashen mijinta batare da hakan ya dameta ba. Dan hatta bedroom da toilet saida suka gyaro masa. Tsakar gida kuwa dama maigadi ke sharesa fes shiyyasa da wahala kaga datti. Ganin magrib ta kusa ta basu kuɗin ankon datai alƙawari da cewa su tafi mijinta ya kusa dawowa bata bukatar ya dawo ya gansu. Basuce mata komai ba akan hakan sai dariya da sukayi kawai, tai musu rakkiya har gate suka wuce.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button