BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 24

24

……….Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu mintuna kamar kowa bazaice komai ba, kusan mintuna uku Amal ta nisa. Cikin ɗan ɗari-ɗari ta fara magana. “Ni dai a nawa nazarin da hange sai naga kamar cikin nan shine matsalarki. Kin san fa wasu mazan basu son da anyi aure ace ciki ɗin nan. Kigafa yanda Shareff ke sonki amma ace haka na faruwa tsakaninku wata baifi uku ba da aure, amma dai bamu san zuciyarsa ba kuma”.
Ta ƙare maganar da ɗan shafo gefen wuyanta ganin yanda suka tsura mata idanu su duka. Yanzu ma kamar bazasu ce komai ba, harta fara tsarguwa sai Siyyah ta katse fargabarta.
“Kuma fa maganar Amal kamar tana a kan hanya. Musamman idan mukai dubi da yanayin mijinki. Anya kuwa cikin nan bashine matsalar ba…”
Nufashi Fadwa taja da ƙarfi, zuciyarta babu abinda take hasaso mata sai yanayin Shareff a randa Dr Jamal ya tabbatar musu tana da ciki, ƙanensa da iyayensu kowa na murna amma shi bataga ko murmushinsa ba, da suka dawo gida ma baice mata komai game da cikin ba amma yana bata kulawa da duk take buƙata. Kenan in dai maganar ƙawayenta gaskiya ne kulawar yana bata ne kawai domin kar ace baya farin ciki? Ya ALLAH itako yaya akai ta kasa ganewa sai yanz………
Sima ce ta katse tunaninta da faɗin, “Fady nima dai ina ganin maganar su Amal nakan hanya gaskiya, dan na tabbatar badan cikin nan ba maybe ma tare da ke zai wuce ku ɗanyi honeymoon ɗinku. Amma gashi ciki ya muku cikas dole yayta maida allura galma a tsakaninku, ta hakanne kuma wannan yarinyar zata samu damar cika burinta akansa. A yanzu ma ɗaukar ciki duk ta wajigaki miji na gudunki inaga kin haihu, wlhy yara haukataki zasuyi ki fita hayyacinki. Baki ga miji hatta da followers naki sai sun gudu, dama kece mai kankaro mana mutunci saboda a yanzu kina cikin manyan tiktokers dake lokaci da kuma tarin followers a arewacin Nigeria, sunanki ya riga yayi zarra, da kin saki video tamkar wuta jaje haka yake danne duk wani posting, kiyi tunani”.
Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka ciko mata ido saboda maganganunsu sun matuƙar shigarta. Ta sake nisawa cikin ɗacin zuciya batare data kallesu ba. “Naji duk bayanan ku, sai dai ban san yaya kuke so nayi da cikin ba tunda ya riga ya shiga jikina, tun kafin faruwar haka ya kamata na ɗau mataki, amma a yanzu na riga nayi latti..”
“Bakiyi latti ba Fady, har yanzu kina da sauran dama”.
Ido ta tsirawa Bibah da tai maganar. Bibah ta jin jina mata kai da cigaba da faɗin, “Da gaske bakiyi latti ba, kwata-kwata cikin ana maganar ko wata biyu bai cika ba, ki zubar da shi kawai, hakan zai baki damar sasantawa da mijinki tare da fatattakar shegiyar yarinyar can a rayuwarsa. Idan ya fara nuna son ƴaƴan da kansa sai ki bama cikin damar shiga hankalinki kwance”.
Sosai maganar ta doki ƙirjin Anam dake saurarensu ta jikin window, dan a inda take zaune windown ɗakin Fadwa ne, tun kuma shigarsu ɗakin tana iya jiyo tattaunawarsu, sai dai da farko bata maida hankali ba sai da Amal ta fara danganta ciki da matsalar Fadwa. Duk da bata son Fadwa addu’a take a ranta kada ta ɗauki shawarar su Sima…….. Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani, Mamie ce, hakan ya sata mikewa a wajen tilas tana amsa kiran dan video call ne…..

Wayarta da Mamie ta hanata jin ƙarshen hirar su Fadwa, dan dai-dai tana kammala wayar suke fitowa kowannensu fuskarsa ɗauke da dariya. Su dukansu kallon banza suka shiga watsa mata suna jan tsaki, wasun su ma har da jeho mata kalmar zagi. Batako kalli inda suke ba, tamayi kamar bata gansu ba. Koda Fadwa ma ta dawo daga rakkiyarsu bata nuna ta ganta ba itama.
Itama ciki ta koma zuciyarta na kaikawo na neman mafita duk da bata san yaya ake ciki ba a yanzu. Fadwa ta karɓi gurguwar shawararsu kokuwa?Ba komai ta fahimta a hirar tasu ba dan ma suna haɗawa da turanci ne shiyyasa na zubda cikin yafi tsaya mata a rai. Ganinta shiru yasa Aysha data fito a wanka tambayarta ko lafiya. “Babu komai” ta bata amsa tana mikewa itama ta faɗa bayi.

Kusan sati ɗaya dayin wannan magana har Anam ta sakankance Fadwa bata amshi shawarar ƙawayenta ba sai kawai ga Khaleel da yazo ɗaykarta an tashi aiki yake sanar mata Fadwa na asibiti ta samu miscarriage. Tsabar yanda zancen ya daketa batama san sanda ta maimaita kalmar miscarriage ɗin ba cikin waro iro. Da damuwa a fuskar Khaleel ya gyaɗa mata kai. “To ya za’ayi, haka ALLAH ya ƙaddara, wajen 3 na yamma Aysha ta kirani wai Fadwa tace cikinta na ciwo ta rakata asibiti. Suna zuwa likita yace cikintane ke son fita yay mata allura don hana faruwar hakan amma ba’a dace ba. Yanzu haka su Mom ma duk suna can nima dan ɗaukarki na fito dan ta zubar da jini sosai gaskiya”.
Har cikin rai Anam kejin zafin abin dan ta tabbatar Fadwa da kanta ta zubar da cikin nan, kuma tabbas da likitan suka haɗa baki dan a ɓadda kama wa Ayshan. Jin batace komai ba Khaleel ya dubeta. “Ya naji kinyi shiru?”. Numfashi ta fesar da zuƙa, cikin kauda kai tace, “Ba komai ALLAH ya kiyaye gaba”. “To amin ya rabbi. Amma dai kowa baiji daɗin fitar cikin nan ba. Yaya Shareff ma koda na kirasa kasa magana yayi ya yanke wayar. Sai daga baya na sake kiransa wlhy bakiji muryarsa ba kamar yayi kuka. Hakan yasa na fahimci ba ƙaramin so da ƙwallafa rai yayi akan cikin nan ba fiye da kowa”.
“Huhmm!”.

Kawai Anam ta iya cewa saboda sun iso asibitin. Duk ƴan gidansu suna a wajen har Mommy da Gwaggo Halima. Ta gaida kowa da tambayar mai jiki ta koma kusa da Aysha. Babu jimawa da zuwansu su Abbah ma suka iso, daga gani daga wajen aiki suka wuto nan suma. Har sannan ba’a bar kowa yaga Fadwa ba. Amma dai doctor yace da sauƙi sun mata allurar barci ne dan ta jigata matuƙa.
Kasancewar kusan duk daga wajen aiki ko makaranta sukayi nan Daddy yace suje gida haka nan abar wanda zai zauna da ita. Gwaggo da ƙanwar Fadwa ɗin aka bari, sai Gwaggo Halima da tace sai zuwa anjima zata tafi ita. Su dai sallama sukaui musu suka wuce kowa na cigaba da jajanta abun a ransa.

Washe gari kafin su wuce office nan suka fara zuwa ita da Khaleel, sai Aysha data biyosu dan kawo breakfast. Sun samu Fadwa zaune tana waya da alama ita da mijinta ne, dan sai faman marairaice murya take hatta da Gwaggo dake kusa da ita bawani jinta take ba. Ganin tana waya Khaleel ya fita dan ganin doctor, Aysha tabi bayansa da sauri dan tana son amsar kuɗi a wajensa nayo cefane daya manta bai bada ba. Gwaggo da tun shigowarsu tai kamar bataga Anam ba ta miƙe tana ɓantarar goro. Hanyar fita ta nufa dan so take ta tare Khaleel a waje ta amshi kuɗi itama. Ɗakin ya rage daga Anam sai Fadwa dake waya tana ɗan ɗaga murya yanzu wai dan Anam taji. Anam ɗin kuwa tana ji, sai dai tayi kamar bataji ɗin sai faman buga game take a waya. Lokaci-lokaci takan kai yatsa ta gyara zaman gilashinta…. Tsakin da Fadwa taja lokacin da ta kammala wayar yasa Anam ɗan dubanta. Kallon juna sukai cikin ido, Anam ta janye nata cikin halin ko in kula…..
Yanda tayi sai ya batama Fadwa rai, duk da halin da take ciki muryarta ko fita bayayi da ƙyau ta watsama Anam harara da jan tsuka a karo na biyu. “Ban cika son ganin wanda ban gayyata cikin lamurana ba, ko kuma ban sani ba ko zargin namu ya zama gaskiya ne lashemin jariri akayi..”
Da turanci tai maganar, hakan yasa komai ya shiga kunnen Anam. Batai niyyar harta bar asibitin ba tai magana amma sai ta kasa hakan, dan a wannan gaɓar taga ya dace ta bama Fadwa amsa dai-dai da ita. A hankali ta taka gaban gadon tana zira wayarta a aljihun wandon uniform ɗinta na hidimar ƙasa. Babu alamar tsoro ko shakka a cikin idanunta ta tsaya gaban Fadwa dake mata kallon mamaki. Idanunta dake cikin farin gilashi ta lumshe ta sake buɗewa akan Fadwa. “Tabbas jaririnki kam cinyesa akai amma da allurar zubda ciki. Dan haka masu zargin zan basu amsar da suke bukata har shi mai cikin dan yasan ɗansa ko ƴarsa sun salwantane ta hanyar abortion bisa shawarar ƙawayenki masu ɗauraki a hanyar da bazata taɓa ɓullewa da ke ba. Ai ban san ke ɗin cikon bench bace ba sai yanzu. Ki fita a sabgata, idan kuma kikace zaki iya dani wasan biri zanyi da ke a tsakkiyar kasuwa na rantse da ALLAH! Be careful”. Ta ƙare maganar da ɗalla yatsunta biyu a saitin fuskar Fadwa tana wani irin murmushi da kashe mata ido ɗaya.
Numfashi Fadwa taja da ƙarfi, dan tun fara maganar Anam tai sumar wucin gadi……..✍????

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button