BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 46-50

Page 4⃣6⃣ to 5⃣0⃣

Jiddah rayuwa ta fara sauya mata domin kuwa maganin inna asabe ya fara tasiri a kanta a yanzu jiddah sallah bata dame ta ba,,makarantar ma yanzu tana SS2 amma ta daina zuwa bata karatun alqur’ani data saba yi duk safiya,ita kanta tana jin wani iri a jikinta amma kuma tana son yin karatun amma data fara sai taji kasala ta rufeta,,,

tabbas asiri gaskiyar mai shi wannan haka yake ta bangaren inna asabe da ya’ya’nta domin yanzu farin ciki suke ciki kamar an basu kyautar kujerar makkah,,,

a safiyar yau ne inna asabe ke shirin komawa wajen bokanta domin yin aiki na karshe a kan jiddah saboda haka tun asuba ta tashi tana sauri ta fita dan kar ta tarar da layi haka nan take jin farin ciki a cikin zuciyar ta..ko farkawa bata bari sunyi ba ta zari mayafi sai gidan boka…tana zuwa bata tarar da kowa ba dan ta bugo sakko…yana ganinta ya fara washe wagegen bakin shi wanda ba haure ko guda daya a ciki,,magana ya fara mata da katuwar muryar sa,,lallai ke jaruma ce muna son aiki da irin ku wadan da basa bata mana aiki,,,saboda haka wannan ma aikin naki tabbas zan miki me zafi..wata laya ya ciro a kasan inda yake zaune tare da mika mata layar,,,tana rawar jiki ta amsa..wannan layar a kasan inda take kwanciya zaki haka rami ki binne ta,,sannan ya kara dakko wani garin magani ya mika mata,,wannan kuma ki zuba shi a daidai inda kika san zaka taka,,tofah da taka kuma ta kwanta akan wannae layar aikinki
ya gama,,,amma kuma da sharadi,,sharadin meye boka inna asabe ta fada,,dan kuwa ita a ranta ko meye sharadin zata yarda komi munin shi kuwa indai jiddah zata wulanka a idon duniya,,,sharadin kuwa shine duk randa aka tona wannan layar to wannamd asirin kan daya daga cikin ya’ya’n ki zai koma,,duk da ta tsorata amma hakan bae hana ta amsawa ba da ta amince,,dan kuwa tasa aranta bame tonewa,,
shidai boka maimaita mata yake yi,,amma da yake zuciyar ta ta kekyashe bata damu ba,,,kudi ta ciro ta mika masa sannan ta fito ta fara tafiya dan samun abin hawa,,,

Ammar ne zaune a compound din gidan shi kadaine amma kallo zaka masa kasan ya lula duniyar tunani ,,abbas ne tsaye akan shi amma shi baima sani ba,,,ruwan dake hannun sa ya yarfa masa,,firgigit ya dawo hayyacin sa,,,murmushi yayi kafin yace
lafiya,,ina fa lafiya kana nan ka antaya cikin tinanin jiddah koba haka bane nasan dai ita kadai keda wannadm matsayin,girgiza kai ammar yayi kafin ya fara,,hakanadm a yan kwanakin nan nakejin faduwar gaba kamar wani abu mara kyau zai sameni kuma tunanin jiddah yana fadomin cikin raina koda yaushe,,,numfasa wa abbas yayi kafin yace ni ina ga kamar rashinta a kusa da kaine ya kawo hakan amma ba abinda zai faru,,ya kamata ka kirata kaji lafiyarta,,,na fada maka na kirata amma wayar bata shiga anya lafiya kuwa ya kamata inji daga gareta dan ni wannan shirun nata bana lafiya bane dan yasan koshi bai kirata ba ita zata kirashi,,,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button