BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 26

26

……….Gyaran murya ya ɗanyi bayan yaja wasu seconds yana sauraren yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Bazaki daina wannan kukan ba wai?”. Ya faɗa a hankali tamkar ba shi ba…
      “Na daina”.
Ta bashi amsa wani kukan na sake kufce mata. A karon farko taji yayi murmushi har tana iya jiyo sautinsa a cikin kunnenta, ya ɗanja numfashi da sake sauƙaƙa muryarsa “Ya isa nace ko. Ki ɗauka ruwa ki wanke fuskarki zan ƙara kira”.
     Cikin jan numfashi tace, “Nace fa na daina Yaya”. Dan haka kawai take jin daɗin yanda yake mata magana da lallashi.
         “Ni banji kin dainaba ai, tunda ga hawayenki ina gani na sauka a z….” cikin sauri ya haɗiye sauran maganar da dafe goshinsa yana cije lips ɗinsa jin zai saki layi. Itama da ba wani gama fahimtar maganar tasa tai ba cikin rawar murya tace, “Yaya dan ALLAH ka faɗama Abie zan dawo Malaysia, idan nice nace zaimin faɗa shi da Mamie”.
      Furzar da numfashi yayi, cikin ɗan kaurara muryarsa yace, “Bazan sanar musu ba, kuma kema karna sake naji kin sanar dasu wani abu ok”.
    “Amma Yaya kag…..”
“Umarni ne ba shawara ba”. Yay saurin katseta. Baki ta tura da hararar wayar kamar yana gabanta, “To nidai bazan koma gidanka ba, sai dai na koma gidan uncle Jafar da zama (Ɗan uwan Mamie da abie ne).
         “Ashe kuwa zan zane miki jiki da bulalai”.
   “To ni Yaya ya kake so nayi? Sai na dinga zama inda ba’a son ganina kamar wata mara gata”.
      “Waye baya son naki?”.
  “Matarka mana. Kuma ALLAH idan bata fitamin a ido ba zan fito mata da ainahin kalata, dan zan koya mata hankali…”
        Dariya ce ke son kufce masa, sai dai ya riƙeta ya dai saki murmushi. “Uhuyim! Ke har wata kala ce da ke ashe? To faɗamun yaya kalar taki take dan mu kiyaye ni da matata”.
   “To ni ai bance kai ba”.
“A idan zaki koyama matata hankali ai dole ina ciki. Kinga gara mu kama kammu kar truth color ɗinki ta samu barin Nigeria auntynmu”.
        A yanda yay maganar ya saka Anam fashewa da dariya. “Oh oh ya kaga Anam Auntyn su Yaya, gaskiya kowa zaiji a jikinsa ne, yanda kake mana mazurai nawa sai yafi ALLAH Yaya”. Sai ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.
       Kansa ya ɗan girgiza da shafawa yana sakin murmushi, yasan ta iya surutu, sai dai bata taɓa sakewa da shi ba irin haka. Sai dai yaji surutunta da wani. Ya ƙara sakin murmushi da fesar da numfashi a hankali yana lumshe idanunsa da sake lafewa cikin kujerar falon daya kasance masaukinsa. Haka kawai ya tsinci kansa cikin nishaɗi dayin wayar tasu……

       Yayin da Anam da Shareff ke waya anan acan gidan Mommy ce ke neman wayarsa a fusace saboda hukuncin da Daddy ya yanke cewar Anam bazata bar gidan Shareff ɗin ba kamar yanda suka buƙata har sai ya dawo kamar yanda shima ya buƙata. Amma sai taƙi samunsa anata nuna mata waya yakeyi. Ranta ne ya ƙara ɓaci ganin mintunan dake ta ƙara tafiya amma ana sake jadadada mata ana amfani da layin. Ta tura massege babu reply. Ga Fadwa nata musu kuka ita indai Anam zata koma mata gida to ita bazata koma ba..
      “Wai ni yaron nan da ubanwa ma yake waya hakane? K Hussaina jeki ki gano min Daddynku waya yakeyi”.
   Miƙewa Hussaina tayi tana amsawa da to ta fice. Mintuna kaɗan ta dawo ta sanar mata ba waya yake ba, hira yakeyi ma shi da Abba.
  “Kai! To da ubanwa yaron nan ke waya?”.
Kuka Fadwa ta sake fashewa da shi. “Wlhy yanzu haka shegiyar yarinyar can ce ta kirashi tana ƙulla mana sharri a wajensa. Na tsaneta, bana sonta. Idan ta koma min gida saina kasheta”.
    Shigowar Gwaggo falon ya hana Gwaggo Halima da Mommy bama Fadwa amsa. Takai zaune tana murmushi idonta akan Fadwa. “In dai bazaki kiyayi gaggawa akan al’amuranki ba kuka yanzu kika fara shi. Da kinyi haƙuri kin cigaba da jiran nawa shirin da ba’akai ga haka ba. Ku kuma kun biye mata. Duk yanda kuke tunanin yarinyarnan tabar gidan Mustapha da ƙarfin tuwo bazai yuwuba, wannan kuma zancen ita ta zubda ciki da kuka ƙulla ƙara kusantata ma da gidan kukayi tunda gashi su Muhammadu sun tabbatar muku yanzuma ta fara zama. Duk wanda ya baku shawarar juya zancen zubewar ciki da ita ta zubar ya baku gurguwar shawara ne ga tabbaci kun gani”.
       Mommy da takai zaune cikin sanyin jiki da maganganun Gwaggo ta dubi Gwaggo Halima. “Maganar Gwaggo haka take Halima. Munyi kuskure nima na fahimta. Da Fadwa ta sanar mana zatai hakan ya kamata mu dakatar da ita mu fara yin nazari, tare da bincikarta wanda ya bata shawarar yin hakan tunda mun san zubewar cikinta bashi da alaƙa da yarinyar da gaske”.
     Itama Gwaggo Halimar ajiyar zuciyar ta sauke. Sai kuma ta jinjina kanta, “Hakane Gwaggo anyi kuskure, ba kuma kowa ya jawo hakan ba sai Fadwa da shegen gaggawarta. Na faɗa mata ta kwantar da hankalinta mu jira naki shirin amma rashin haƙuri yasata yanke wannan hukuncin. Gashi yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba tunda abinda take son yay nesa da ita da mijin nata damu baki ɗaya bai tabbata ba. Kuma tabbas zaman yarinyar nan cikinmu ba alkairi bane,  na tabbatar yanda bamu ƙaunar ubanta shima bazai taɓa son mu ba, amma ya kawota cikinmu saboda sharri irin na ɗan uba da baka ganesa sai ALLAH kawai. Gwaggo kiyi haƙuri, yanzu minene mafita?”.
      Baki Gwaggo ta taɓe. “Toni mizance yanzu kuma. Nawa shirin ma ai kun ruguza da shirmen ƴarku. Sai kubar yarinyar ta koma gidan kamar yanda Muhammadun ya faɗa. Zanje na sake sabon shiri a kanta dan wannan karon dole ne muyi shirin da zata koma inda ta fito kuma har abada bazata sake dawowa ba. Kai bama ita da suka haifa ba, har Usman da Maryam (Aunty mimi) bazasu sake waiwayo ƙasarnan ba har abada balle ita karan kaɗa miya”.
    A take fuskokinsu suka washe da murmushin jin daɗi. Fadwa tace, “Amma ni dai gaskiya ayi da sauri. Dan wlhy idan ina ganinta a gidana ji nake kamar na shaƙeta ta mutu. Bana son Soulmate ya dawo ƙasar nan tana gida na”.
       “Batun kafin ya dawo ƙasar nan bazai yuwuba. Domin kin ɓata komai ga shirin yin hakan kuma ai. Dolene muyi ɓadda kamar da zasu cire ɓaranɓaramar da kikai a ransu gaba ɗaya daga nan har zuwa lokacin bikin Maheer, so nake da bikin idan sun zo su tattara ƴarsu su wuce yanda bazasu sake dawowa cikinmu ba har abada. Idan kuma kika ƙara yin wanu shirme to kiyi kuka da kanki bani Hannatu ba kuma”.
     Baki Fadwa ta tura gaba sai dai batace komai ba. Nan su Mommy suka shiga jadadada mata ta kiyaye kar kuma a sake samun wata matsalar kamar yanda Gwaggo ta faɗa. Idan tai haƙuri komai zai zama labari dan suma basu da burin daya wuce Anam ta bar gidan ai. Miƙewa Gwaggo tayi, “To bara nayi nan karma wani ya shigo ya ganni. Shima kuma Mustapha kar wanda ya kirasa akan maganar mu jira muga ko wani zai sanar masa a cikinsu”.
   Duk sun gamsu da hakan. Daddy dake bakin ƙofar yaja da baya a hankali yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa. Dama yazo ne dan ya sake kwantar ma da Fadwa hankali da nuna mata tabar zargin kowa akan zubar cikin ta ɗaukesa matsayin ƙaddara. Amma sai gashi yaji ainahin abinda ma ke faruwa. Bai bari Gwaggo data fito tana murmushi ta gansa ba, sai ma ya juya yabar wajen ya fasa shigar…

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button