BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 7-8

Washe gari
Tun 5:30am hilal yafarka daga bacci, (Allah sarki hilal, bai samu bacci mai dadiba, kamar irin wanda ko wane ango yakenema a daren farkonsa) haka yatashi yaje yayi alwala, sannan yadawo yatsaya yana karewa Ameela kallon, ba shakka bacci takeyi harda minshari, hilal ya girgiza kai yafita yanufi masallaci,

Bayan ankarasa sallah hilal yatsaya masallaci yayi addu'oi sosai akan aurensu, Allah ya basu zuria dayyaba, 

Koda yagama addu’oin sa haske safiya yafara fito, nan yabaro masallaci yadawo gida,

Kan gadon daya barta  kwance anan yasameta, ko alamun tashi batayiba, 

Yadan tsaya yana kallonta kafin yasa hannu ya daki kafarta “kee…kee..Ameela, kitashi” tayi mika sannan tayi nishi mai karfi, ta bubbude hannaye kamar mai shirin tashi sai kuma ta fasa ta koma kwance,

Hilal yaja tsaki yakara dukan kafarta, takara jan nunfashi cikin muryar bacci tace “lafiya wai”
Hilal yace “ina kuwa lfy gashi har gari yawaye bakiyi sallar ba”
Ameela taja tsaki ta ya mutse fuska “haba Dee yanzu dan Allah ina amarya zaa tasheni da wannan safiya ai kamata yayi abarni natashi dakaina, dan Allah katafi kabarni” takara komawa kwance,

Ran hilal yabace jiyakeyi kamar yakai mata duka, meya shiga tsakaninsu da har zatace tana amarya za a tasheta, yace ” ameela banason rainin hankali, kitashifa nace”
“To jeka naji zantashi” Ameela tafada tana kwance,
Hilal yakara jan tsaki, ya juya yakarasa bakin drower ya ajiye tazbi dinsa sannan, ya cire jallabiyar dake jikinsa ya dauko tawul nawanka yadaura sannan yanufi bandaki,

Kusan minti goma yayi acikin bandakin sannan yafito, still tana nan inda take, baccin ta takeyi,

Falo yafita yaje yadauko ruwan sanyi a firjin yazo ya auka mata su, 

 Da karfi tafarka "nashiga ukku na lalace" tafada cikin magagin bacci, 
Yayi tsaye  akanta yana jiran yashewar idanunta, 
 A hankali ta bude idonta suka hada ido, talura da yanayinsa ransa yabace matuka, 

Sannan ta kauda kai daga kallosa tasaukar da murya “kayi hkr Dee wlh bacci ne yahau kaina”
Cikin hargowa hilal yace “wane irin bacci dazai hanaki sallah da wuri, idonsa yakai ga agogon dayake manne a ginin dakin, yace ” duba agogo kigani karfe 7 harta wuce kinan nan kina bacci, yaushe kika tashi kuma yaushe kikahadamin kayan breakfast, koso kike naje waje naci, da auren nawa”

A hankali ameela ta tasauko daga kan gado tatsaya tana kallon hilal tace “ai amarya bata abinci sai tayi sati daya, haka naji ana fada”

Wani irin haushi hilal yaji kamar ya fashe da kuka yace “to shikenan tunda amarya bata abinci saitabar angonta da yunwa”

yana karasa maganar yanufi wuri shirinsa,
Ameela tayi murmushi tanufi bandaki tafara alwala,

Koda takarasa alwala tafito hilal yakammala shirinsa,
Ta tsaya abakin kofar ban dakin tana tsantsefe hannayenta, ta kalli hilal cike da mamaki “fita zakayj bazaka jira na kammala sallar na shirya maka breakfast dinba”

Yajuyo ya kalleta cike da jin haushinta, sai kuma ya danne bacin ransa, (domin bacin rai bayada wani amfani, hasali karshen bacin raima nadama yake kawowa) tana tsaye bakin kofar bandaki, baice da ita uffanba, yaje yadauko jakarsa ta zuwa aiki sannan yayi ajiyar zuciya yace “kibarshi kawai naci a waje, saboda idan natsaya jiranki zan iya yin late”
Ta shagwabe fuska “nidai Dan Allah katsaya,.karfa mutane sufara zagina suce wayewar garin daren aurenmu, an ganka kanacin abinci a waje”

murmushin karfin hali hilal ya kirkira kafin yace “bakomai matata ai kowa nada uzuri dan Haka namiki uzuri amma nayau kadai, karki kuskura kikara aikata irin hakan”
Ameela ta sunkuyar dakai cike da kunya, kalaman hilal suna matukar sanyata kunyarsa mutum baida zafin rai, dama haka takeson miji mai sanyin hali,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button