BABU SO… 14

Washe gari monday Anam ta koma aiki, Abie da kansa ya kaita. Hakan ya mata daɗi, ya kuma sakata a farin ciki har fuskarta ta kasa ɓoyewa. Da Yaseer ta fara cin karo, wanda rabonsa da zuwa aiki tun randa ya kaita gida. Kallon kallo suka tsaya yima juna, farin cikin da take ciki ya sata fara sakin murmushi. Cikin harshen turanci da mutsukka idanunta take faɗin, “Ko aljani ne kemin gizo”.
Duk yanda ya so daurewa sai ya kasa. Ya saki murmushi yana gyara tsaiwarsa. “Ba aljani bane ifiriti ne”. Dariya maganar tasa ta bata. Ta ko ƙyalƙyalawa cike da nutsuwa tana kare bakinta da handkerchief. Jiyay gaba ɗaya ya narke a kallonta, harma zuciyarsa na jin anya kuwa zai iya kiyaye dalilin da ya sashi jin zai nisanceta kuwa?… Matsowarta kusa da shi ta katse masa tunani. Har yanzu fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙwara. “ALLAH da gaske naji kewarka Friend. Wane laifi mukai haka ake fushi damu harda tafiya babu sallama?”.
Hannayensa ya haɗe alamar ban haƙuri????????, fuskarsa a marairaice sai dai baice komaiba. Cikin ƴar dariyar data ƙara zuwa mata tace, “Shikenan ya wuce muje ciki”.
Tare suka shiga, suka cigaba da hidimomin gabansu. Koda aka tashi aiki Maheer ne yazo ɗaukarta. Ta nuna farin ciki anan ma dan tunda yazo hidimar biki ta hana su zauna su gaisa da ƙyau. Maheer baida damuwa, yanada sauƙin kai sosai ga barkwanci, sai dai Shareff ya fisa haƙuri nesa ba kusa ba, kawai dai yafisa sakewa da mutanene shiyyasa ake ganin kirkin Maheer fiye da Shareff ɗin.
Bai wuce da ita gida kai tsaye ba. Sai da suka biya wani joint sukaci kayan kwaɗayi sukai hira sosai sannan. A hanya yake cemata yaushe zata rakasa gidan amarya yaga gida. Cikin taɓe baki ta bashi amsa da “Yah Maheer kaje abinka kai kaɗai kawai”.
“Miyasa bazakije ba ke?”.
“Ba komai, kuma ni nama riga naje ai”.
“Idan kin koma ma ai duk cikin zuminci ne”.
Maimakon ta amsa masa sai ta canja da wata hirar. Shima sai bai sake maganarba har suka isa gida.
A kwana a tashi ango da amarya sukaci kwanaki shidda da angwancewa. Soyayya ce ake zubawa tamkar babu gobe. Basu da matsalar abinci, dan kullum sai Mamie ta aika musu na safe na rana harda na dare ma, sai da Yah Shareff ɗin da kansa yace a daina kai na daren sannan Mamie ta hutar da kanta. A komai nane suke da juna tamkar su haɗiye kansu. Basu da wata damuwa sai suci suyi ƴar soyayyarsu. Babu inda yake zuwa dan ya ɗauka hutu na sati biyu dama, duk da sati ɗaya yay niyya Fharhan ya takura masa akan biyu dai sannan gajiyar biki ta sakeshi. Ya dauka sati biyun dai kawai badan yana tunanin zama har su cika baije office ba, dan yasan sunada ayyuka danƙam harma da wasu sabbin projects da yake fatan samu wanda zasu fito ne daga gwamnati.
Yakan je gidansu a kullum da yamma ya gaida iyayensa, sai dai koya shigo wajen su Mamie basa haɗuwa da Anam. Dan a mafi yawan lokuta yakan zone bata dawo aiki ba. Bakuma dan lokacin dawowar tata baiyiba. Kawai dai yanzu Maheer na matukar ɗauke mata hankaline, yama hana Abie kaita da safe shi ke kaita ya kuma je ya ɗakkota, bakuma su dawowa gida sai sun ɗan zaga gari wani lokacin ma sai bayan magrib. Wannan dalilin yasa duk sanda Yah Shareff yazo baya samunta a gidan. Bai dai taɓa magana ba, hasalima bai nuna ya san da wanzuwarta ko saɓanin haka ba. Itako dama ko’a jikinta harma mantawa take da shi yanzun, dan koba komai ta huta da harara da kallon dake matuƙar ƙona mata rai daga garesa.
Yau ta kasance juma’a. Da wuri Maheer ya ɗakkota a wajen aiki da jaddada mata ta shirya da wuri zatai masa rakkiya wani waje. Batare data tambayesa ba tace to. Ciki ta shige, bayan ta gaida Mamie da Abie ta wuce ɗakinta. Dan aunty Mimi da yaranta sunje Abuja gidan yayan mijinta, amma yau suke saran dawowarsu. Wanka tai ta shirya tsaf cikin kwalliyar doguwar rigar material dan Yah Maheer yace mata tasa kayan hausawa. A lokacin har tana ɓata fuskar cewar ita suna damunta bata son zafi, lallaɓata yay, dan yafi son ganinta a kayan saboda ƙyawun da suke mata. A bikin nan ba ƙaramin son ganin kwalliyarta ya dingayi ba. Koda Mamie tace ta zauna taci abinci catai a’a zasuci a wajen cin abinci Yah Maheer zata raka wani waje. Mamie ta ɗanyi jimm sai kuma ta sauke numfashi, gargaɗi tamata nata kama kanta tare da jin tsoron ALLAH.
“Insha ALLAHU Mamie bazaki taɓa yin kaico akaina ba, yanda nake a gaban idonki haka zan cigaba da kasancewa a bayan idonki. Domin UBANGIJIN dake azaba ga wanda ya saɓa masa, yake rahama ga wanda ya bisa yana kallona koda ke baƙya ganina”.
Murmushi Mamie tayi, cike da jin daɗi da alfaharin tarbiyyar da suka bama gudan jininsu tilo duk da suna rayuwa a inda kowa ke ganin dole ne yaro ya lalace, sai dai ba hakan baneba, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. “ALLAH yay miki albarka, ya kuma baki ikon tabbatarmin da hakan”.
“Amin Mamie na uwa ɗaya tilo”.
Ta faɗa tana sumbatar hanun Mamie sannan tai mata sallama ta fice.
Tun tafiyar tasu batai nisa ba sosai ta fara fahimtar inda suka dosa. Taso ta share amma saita kasa. ta dubesa a shagwaɓe “Yaya nifa….” Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar fadin, “Ban son kice komai. Ai ni zaki raka ko”. Shiru tayi badan taso ba. Dan tana ganin girmansa da kima sosai a zuciya da ayyuka. Hira ya cigaba dayi mata, wani ta amsa wani tai murmushi har suka iso. Har ciki ya shiga da motar, kamar yanda ya saba mata a tsakanin nan shine ya fara fita sannan ya zagaya ya buɗe mata fuskarsa dauke da murmushi kamar yanda tata ma ke ɗauke da murmushin mai bayyana haƙora. Tace, “Kai Yaya Maheer shine har da wani ɗan respect?”.
Dariya ya sanya, idanunsa akan fuskarta yana ji kamar ya haɗiyeta dan murmushi na mata masifar ƙyau. Ƙara risinawa yay irin na respect ɗin yana nuna mata hanya alamar suje. Dariyar ta sake sanyawa da salute nashi itama….
A hankali ya lumshe idanunsa da ɗaukesu daga garesu yana sakin siririn tsaki dan komai yana faruwa ne akan idanunsa kasancewar yana daga barandar sashensa tare da Fharhan da Khaleel suna magana akan office. Tsakin nasa yasa Khaleel da Fharhan da suma ke kallon su Anam ɗin maido dubansu garesa. Sai dai kasancewar ya riga ya maida ga lap-top ɗin dake cinyarsa yasa basu fahimci da ainahin wa yake ba. Khaleel ya mike yana miƙama Maheer daya iso wajen hannu yana faɗin, “A’a Brother dama nan kawo ashe?”.
“Eh wlhy, ai ban san kaima nan din kayo ba damun haɗa tafiyar ma ai”.
“Ai babu damuwa tunda ga ƴar rakiya ka samo”.
Murmushi kawai Maheer ɗin yayi da maida hankalinsa ga Fharhan suka gaisa cikin mutunci dan duk abokan Shareff suna ɗaukarsu yayu suma.
“Babban Yaya barka da yammaci”.
Maheer ya faɗa idonsa akan Shareff. Sai lokacin ya ɗago, ya ɗan dubi Maheer ɗin fuska babu yabo babu fallasa. “Daga ina haka?”.
“Daga gida muke. Yau dai nace bara nazo na gaida amarya na huta da gorinta”.
“Hakan nada ƙyau”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa nakan abinda yakeyi dan dama tuni ya maida kansa ga lap-top ɗin. Shima Maheer maida dubansa yay ga Anam data coge can taki karasowa. “Hajjaju ƙaraso mana ku gaisa da su Yaya”.
Baki ta tunzura, badan taso hakan ba ta nufesu tana ƙunƙuni. A jimlace ta gaishesu, batare data damu dawa ya amsa ba waye bai amsa mata ba tabar wajen. Shima Maheer bayanta yabi sai dai ganin ta sake cogewa alamar bazata shiga falon ba yaja hanunta. Ƙoƙarin amshewa take amma ya hana hakan sai da suka shige ya saketa. Kowa babu a falon sai uban ƙaurin abinci daya gaurayesa, ga falon a ɗan hargitse alamar dai yau bai samu gyara ba koma ba yau ɗin kawai ba. Anam ta yamutse fuska kamar mai tsantsami tana bi ko’ina da kallo a karo na farko dan waccan ranar batai ba.
“Ni kamar ƙaurin abinci nakeji fa?”.
Ya Maheer ya faɗa yana dubanta. Baki ta taɓe da kauda kanta batare data amsashi ba. Shima sai bai sake magana ba ya shiga ƙwala kiran sunan Fadwa a tunaninsa ko ta shiga wani uzirinne a ciki batasan abincin na ƙunewa ba. Kusan sau uku sannan ta fito daga hanyar bedroom hanunta rike da waya tana murmushi, da alama abu take dubawa da yake sakata nishaɗi………..✍
????????Wayyo Fady baby ya zaki bamu kunya haba selen mu so kike ƴan uba su sami na faɗa yau????. Koda yake munada bakin ramawa????