BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 15

15

……….Da kaurin abincin ta fara cin karo, dan haka ta kwasa da ɗan gudu zuwa kitchen tana faɗin, “Wayyo ni Fadwa yau ma yayi ƙauri”.
      Daga Maheer har Anam da kallo kawai suka bita, Anam ta taɓe baki da neman kujera ta zauna. Ganin haka shima Maheer ɗin sai ya zauna yana ƴar dariya. “Tofa bama yau aka fara ƙonawaba kenan. Lallai Yaya an shigo abba tuwa ashe. Nikam gaskiya bazan iya haƙuri da mace bata kulamin da cikina ba”. Ya ƙare maganar yana tsare Anam da idanu.


     Idanu ta ɗan waro da ɗage kafaɗarta baki a tabe alamar I don’t care, sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya. Ihun da Fadwa ta saki ya hanashi cewa komai ya mike da sauri ya nufi kitchen ɗin. Anam kam maimakon ta tashi sai ta ɗauka waya tana cigaba da dariyarta. A dai-dai nan shima ya shigo falon kasancewar

Fharhan da Khaleel sun wuce office saboda sunada uziri. Buɗe ƙofar ta sakata rage dariyar da ɗan kallon ƙofar, sukaima juna kallon ido cikin ido. Nata ta fara janyewa saboda hango wani irin yanayi mai kama dajin zafinta a cikin nasa idanun, itakan ta rasa mitaima Yaya Shareff ya tsaneta a duniyar nan, idan dan tazo gidansa ne ya kwantar da hankalinsa wannan shine zai zame mata na ƙarshe insha ALLAH.

Bata sake yarda ta kalla inda yake ba, sai dai har yanzu tanajin nasa idanun a kanta. Hakan ya sakata a matuƙar takura, sai dai kuma ta kasa motsawa balle ko yinƙurin barin wajen tayi….


      Dariyar Maheer ta sakashi janye idanunsa a kanta ya juya garesa, sai yay karo da idanun Fadwa dake tsaye ƙyam a kansa tana masa kallo mai cike da tuhuma. Fuska ya sake tsukewa cikin basarwa ya maida hankalinsa wajen bin falon da kallo. Sosai ransa ya ƙara ɓaci fiye da wanda yake ciki tun ɗazun, duk gargaɗin da yay mata akan karya shigo ya sake ganin falon nan haka da datti batajiba kenan

Ya ɗan cije lip ɗinsa kawai batare da yace komaiba ya juya ya fita. Hakanne yasa Maheer bin bayansa shima. Anam ma mikewa tai, ta zabgama Fadwa dake binta da kallon wulaƙanci harara sannan ta fice tana jan ƙaramin tsaki.
      Duk da kiran da Maheer yay mata batai niyyar binsu sashen Shareff ɗin ba. Sai dai ganin Fadwa na leƙenta ta window rai ɓace ya sata nufar can tana wani murmushi daya ƙawata fuskarta. A bakin ƙofa ta coge, Maheer ya juyo yana kallonta, cikin tsokana ya wulla mata ƙaramar harara. “Malama wa kikema aikin gadi zaki mana tsaye anan? Zoki zauna jareh”.


     Murmushi kawai tayi itama, batare da tace komai ba ta zauna a kujerar kusa da shi tana satar kallon Shareff dake latsa waya kamar ma bai san da shigowar tata ba. Baki ta taɓe itama ta ɗauka tata wayar ta shiga latsawa. Ba’a rufa mintuna huɗu ba Fadwa ta shigo ɗauke da babban basket dake ɗauke da kuloli da duk abinda maicin abinci zai iya buƙata. Maheer ya miƙe ya karbeta yana dariya, cikin ƙasa da murya yace, “Badai mai ƙaurin zaki bamu ba?”. Harara ta ɗan sakar masa da kai masa ranƙwashi ya kauce, dining ya nufa domin ajiyewa, ita kuma ta nufi inda Shareff ke zaune har yanzu idonsa akan wayarsa. Zama tai kusa da shi tana mai rungumesa tare da manna masa kiss a kuncinsa. “I miss you my Soulmate”.


    Maimakon amsa mata sai ya ɗago ya ɗan saci kallon Anam. A zahiri idonta akan waya yake, sai dai kunenta da hankalinta na tare da su….. “Wai har yanzu fushin kake?”. Fadwa ta faɗa cikin kunnensa hanunta ɗaya na cikin nasa ɗaya na shafo wuyansa zuwa gefen kunne. Hanunta dake kan wuyansa ya janye, a hankali yace, “Miye haka wai, muje ki bani abinci”. Bataso haka ba, sai taji inama ya biye mata kodan ta turama wannan yarinyar haushi. Amma ko yanzu ma bata ɓaci ba, tayi alwashin sai Anam ta

daina zuwa mata gida har abada daga yau dalilin abinda ta shiryama ranta zatai mata. Cike da isa da yauƙi tabi bayan Shareff zuwa dining, dama shi Maheer tunda ya dire abinci yaja kujera ya zauna acan abinsa.
        Cikin bada umarni Maheer yacema Anam ta taso suci abinci, ta ɗago tana girgiza masa kai alamar a’a. Hararta yayi, “Kinsan ALLAH idan na taso ɗaukarki zanyi kamar bab…..”
    “You’re vary stupid!!”.


Ya faɗa cikin suɓutar baki idanunsa na wani irin ƙanƙancewa. Furucin da fusatar tasa ya saka Maheer haɗiye sauran abinda ke bakinsa. Anam da Fadwa kam gaba ɗayansu suka zuba masa ido dan yanda yay maganar a fusace duk sai da suka zabura. Waya yakeyi, wayar da kafin zancen Maheer yinta yake da murya can ƙasa dako Fadwa dake kusa da shi tana ƙoƙarin fara zuba masa abinci bajinsa take ba. Hannu takai da nufin taɓashi ya maka mata harara dole ta janye, sosai abun ya bama Anam dariya, tako yi gefe da kanta tanayi sai dai ƙasa-ƙasa. Maheer ya kalleta yana murmushi shima.

Cokali ta ɗauka ta saka a cikin abincinsa babu ko ɗar ta kai baki, da sauri ta ɗiba tissue ta tufosa a ciki tana ambaton ya ALLAH. Shima dai Maheer yay cak ya kasa cigaba da tauna na bakinsa. Yayinda shima oga kwata-kwatan ya tufo nasa cikin tissue ɗin daya fisga yana kallon Fadwa rai a ɓace.
“Kinada hankali kuwa? Wannan gishirin fa!”.


Ɗan zabura Fadwa tai baya jikinta na tsuma. Ya sake jan tsaki da miƙewa zai bar wajen tai saurin riƙosa. A fusace ya juyo gareta sai dai saurin rungumesan da tayi ya sashi haɗiye kakkausan furucin da yay niyyar jifanta da shi. Jin bai tureta ba ta ɗago da sauri dan a gareta wannan damace da zata aiwatar da shirinta, babu zato kuwa babu tsammani ta haɗe bakinsa da nata. Da sauri Maheer yasa handkerchief ya rufe fuskarsa yana dariya…


     Faɗuwar abu da tarwatsewarsa kan tiles tare da sakin siririyar ƙarar Anam ya sakashi saurin ture Fadwa yana jan numfashi da ƙarfi. Maheer ma da sauri ya janye handkerchief ɗin dake fuskarsa tare da haɗiye dariyarsa. Kusan a tare suka zabura kanta, sai dai Maheer ya rigashi kai hannu zai riƙo Anam, a ɗan fusace ya fisgo hanun Anam ɗin da Maheer ya kama ta dawo jikinsa, cak ya ɗagata daga dirƙuson da tai ya

maida saman kujera, ƙafarta dake fidda jini ya ruƙo yana kaiwa tsugunne gaban kujerar, sai da ya rumtse ido sannan ya tsige yankin kwalbar cup data shigeta. Tako sake sakin ƙara jikinta na rawa dan har cikin ƙwaƙwalwarta taji cire glass ɗin. Handkerchief ɗin hanun Maheer ya fisga ya ɗaure mata ƙafar, sannan ya sake ɗaukarta cak yay waje da ita. Maheer da shima ke a rikice bin bayansu yay da sauri…..


      Sosai zuciyar Fadwa ta kumburo cikin ƙirjinta tamkar zata fashe, itace ta tura kofin da hanunta ya faɗi lokacin da taga Anam zata miƙe a yanda ba kowa ya gani ba musamman ma Shareff data rungume. Tsabar yanayin da take ciki ko kwakwkwaran motsi ta gagarayi har tajiyo fitar motar mijinta. Hajijiyar da taji tana kwasartace ta sata saurin dafe kujerar dining…

      Basu san ba ƙaramin ciwo Anam taji ba sai da suka isa wani clinic dake anan cikin anguwar. Sun fara mata allurar rage raɗaɗi kafin su tabbatar musu ciwo taji sosai kuma sai an ciro sauran kwalbar daya karye a wajen sannan a mata ɗinki. Basu wani ja zancen ba akai mata duk abinda ya dace tana faman kuka da raki. Sai da komai ya nutsa ta samu nutsuwa da daina kuka har sun fita sunyo sallar la’asar sun dawo sannan suka sami damar ganinta. Tausayinta dukansu ya sake kamasu, dan cikin ƙanƙanin lokaci har ƙafartata ta kumbura. Ƙin yarda tai ta kalli ko sashin da Shareff yake. Cike da shagwaɓa tace, “Yaya Maheer ni ka kiramin Mamie da Abie su zo”.
      “A haba dai sarkin rigima. Ni babu wanda zan kira dan maybe ma su sallamemu yanzu mu wuce gida. Wai ni garin yaya ma hakan ta faru ne? Keda ke zaune a kujera?”.
          Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido data ballama Shareff daya tsareta da idanu shima alamar bukatar son ji.
   “Ina saurarenki ya akai hakan ta faru?”.
          Nan ma ƙin cewa komai tai, sai dai ta ɗago yanzu sosai ta kalli Yaya Shareff har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Maheer da bai hakura da son jiba yay ƙoƙarin zagayawa inda ta juya fuska Shareff ya dakatar da shi. “Malam ya isa”.
   Kamar Maheer zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda shigowar Nurse. Sannu tai musu tare da mikama Shareff dake kusa da ƙofa takardar hanunta. “Yallaɓai zaku iya tafiya da ita gida yanzu, ga wannan magungunan sai a saya mata tai amfani da su, ALLAH ya kiyaye gaba”.
    Amsar takardar yay da gyaɗa mata kansa kawai. Sai da Nurse ɗin ta fita sannan ya dubi Maheer dake tambayarsa ko can gida zasu wuce kawai?. Bai ce masa komai ba ya fita a ɗakin, shi kuma Maheer ya koma inda ta juyar da fuskarta.
      Kallonsa tai da faɗin, “Yaya nidai mu tafi gida kawai, bazan koma gidansa ba, kuma wlhy ta kwana da sanin yanda ta zubarmin da jini sai na rama koba yanzu ba”.
        Ɗan zaro ido Maheer yayi da zama a kujerar dake gaban gadon. Kafin ya samu damar cewa wani abu Shareff da wasu Nurse suka shigo ɗakin. Kallonta yake cikin ido saboda yaji abinda take faɗa. Maheer ma kallonta yake sai dai ya kasa cewa komai dan bai fahimceta ba. Da taimakon Nurses ɗin aka kawota wajen mota, tanata mitar ita dai a kaita wajen Mamie. Bai kulata ba, sai Maheer dake lallashinta. Sun tsaya wani pharmacy ya bama Maheer takardar da atm ɗinsa tare da faɗa masa pin……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button