BABU SO 15

★★
Tun bayan fitarsu take auna son kiran Mamah (Gwaggo Halima) sai dai gargaɗinsa akan kai ƙararsa ga iyayenta ko nashi na taka mata birki. Sosai ta kasa zaune ta kasa tsaye balle tsaida shawara. Har cikin ranta tsoro ne da shakku ke cizon zuciyarta dake ayyana mata abubuwa masu dama. Ta rasa miyasa yarinyar
nan ke yawan shiga mata hanci ne? Kodai akwai alaƙar da suka jima suna jin tsoron ta kasance ne ta ƙullu tsakanin mijin nata da baƙar yarinyar nan? “Kai ina, wlhy zuciyata bazata iya ɗauka ba”. Ta faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma zuciyarta farmaki. Ba yau ta fara irin wannan tunanin ba, shiyyasa a koda yaushe take ƙara jin tsanar yarinyar bayan wadda mahaifiyarsu ta cusa musu akan
iyayenta da ita kanta, bata son ganin wata alaƙa tsakanin Mijinta da Anam, amma abin tsoron a kullum kusanci take gani a tsakaninsun, kusanci irin wanda tafi shiga tashin hankali da shi a yanzu fiye dana baya.. Tabbas lokaci yayi da zata ɗauki mataki, idan tace mataki tana nufin koma wane irine in har zai nisanta tsakanin mijin nata da wadda takema kallon maƙiyya tun a zamanin tsatson kakanni da suka haɗa kishi…..
Harta danna kiran Mahmah ta yanke, dan tasan rashin haƙuri da haɗiye abu irin nata, maida akalar kiran nata tayi ga Mommy, bugu ɗaya kuwa ta daga. Ta gaidata cikin ladabi da kwantar da murya. Itama Mommy sai ta amsa da kulawa sosai. Shiru ya biyo baya, Fadwa na tunanin ta inda zata fara…
Mommy ta katse shirun da faɗin, “Fadwa babu dai wata matsala ko?”. Nan ma shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya da fara kukan da bata san yana makale a makoshinta ba. “Lafiya Mommy”. “A’a Fadwa, ya zakice lafiya kuma kina kuka. Kinga kar kiji komai faɗamin matsalarki kinji, Shareff ne ko?”.
“Bashi bane Mommy yarinyar nan ce Anam”.
“Anam!!”.
“Eh Mommy”.
Shiru Mommy tayi zuciyarta na tafasa, taja nannauyar ajiyar zuciya tana mikewa. Falon ta fara zagayawa har lokacin wayar na a kunnenta sai dai ta kasa cigaba da cewa komai kamar yanda itama Fadwa tai shiru. Kusan mintuna biyu sannan Fadwa ta katse shirun da faɗin, “Mommy wlhy ni bazan iyaba. Zuciyata bazata iya ɗaukar cigaba da ganin wannan yarinyar mai ƙirar karuwai na shigomin gida ba. Inba hakaba zan iya kasheta na halaka banza…..”
Rai ɓace Mommy ta katseta da faɗin, “Shi Shareff ɗinne ya kawota gidan?”.
“A’a tare da Yaya Maheer sukazo. Yanzu haka daga ta ɗanji ciwon da tana akan sani tayisa dukansu sun kwasheta zuwa asibiti a ruɗe. Kusan awa huɗu kenan har yanzu basu dawo ba. Wlhy Mommy na tsaneta, dan ALLAH nidai ta daina zuwa min gida”.
Katse wayar Mommy tayi, ranta a matuƙar jagule ta fara laluben number Maheer, harta katse ba’a ɗauka ba, ta sake kira nan ma ba’a ɗagaba. Ranta ya sake ɓaci ta maida akalar kiran ga Shareff. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga, cikin girmamawa a gareta da tausasa harshe na ɗa nagari ga iyaye yay mata sallama da faɗin, “Mommy barka da yamma”.
“Kuna ina?”
Ta jeho masa tambaya batare data amsa gaisuwar tasa ba. Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya kalli Anam dake kwance cikin kujera idanunta a lumshe. Kamar mai raɗa ko tsoron tada jariri a barci yace, “Pharmacy”.
“Kai da wa?”.
Kallon Anam ɗin ya sakeyi suka haɗa idanu, a marairaice ta janye tana kauda kanta gefe. Numfashi ya ƙara saukewa, cikin sake tausasa harshe yace, “Ni da Maheer ne….”
“Dawa kuma?”.
Ta tare numfashinsa tun kan ya ƙarasa. Bai iya karya ba, shi mutumne kai tsaye koda ace gaskiyarsa zata ja masa laifi ko matsala zai faɗa ya amsa hukuncin daga baya. Dan haka yace, “Mommy da Juwairiyya ne da taji ciwo”.
A fusace tace, “Waye Juwairiyya kuma?”.
A hankali yace, “Anam”.
“Kusameni kai da Maheer”.
Ta faɗa tana yanke wayar. Tsirawa wayar ido yayi kamar mai son ganin Mommyn a ciki, sai kuma ya ɗan girgiza kansa ya ƙara kallonta ya ɗauke kansa yanama motar key saboda hango Maheer na fitowa. Baicema Maheer ɗin komaiba ya canja hanyar zuwa gidansa zuwa amsa kiran Mommy. Shima Maheer ɗin baiyi magana ba a tunaninsa mitar Anam ce ta sashi canja shawara.
Gidan su Anam ɗin ya fara tsayawa, sai dai bai shiga da motar ba yay parking a ƙofar gate. Kusan atare suka fito shi da Maheer. Maheer ɗinne ya buɗe mata murfin yana faɗin, “Kefa yau kin zama gimbiya sai dai a ɗaukeki ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi duk da hango mugun kallon da Shareff ya watso mata. Tana ƙoƙarin miƙa masa hannu duk da tsokanarsa dama tai niyyar yi su Abie suka fito shi da baƙon abokinsa da suka jima basu haɗu ba. Hannun Maheer ya janye ya nufi su Abie ɗin kamar yanda Shareff yayi. Abie dake kallonsu fuska ɗauke da murmushi ya riƙo hanunsu su duka yana kallon abokin nasa. “Waɗan nan yarana ne, Babana Al-Mustapha muna kiransa Shareff. Architect kuma Shugaba mai mallakin companyn da nake maka bayani, sai Barrister Maheer”.
“Masha ALLAH yaran albarka”.
Murmushi duk sukayi suna mai rissinawa da gaishesa. Ya amsa cike da kulawa yana riƙo hannayensu shima. Albarka ya dinga saka musu kafin ya juya ga motarsa dake fake a gefe yana faɗin, “Ato ga ɗan uwanku ma ai tare muke da shi sai ku gaisa ko”.
A tare duk suka kalli motar, dai-dai da fitowar Anam daga mota itama cikin matuƙar son nuna dauriya sai dai ta kasa taka ƙafar ta nema zubewa. Da sauri Shareff ya nufeta saboda ratsa kunuwansu da siririyar ƙararta tayi, ya riƙota dai-dai ta kusa kaiwa ƙasa.
“Ance ki fitone?”.
“Nifa na gajine ga zafi a motar”.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa saboda idanun su Abie dake kansu, yayinda kunnuwansu ke jiye musu bayanin da Maheer ke musu na cewar ciwo taji a ƙafa.
Ƙoƙarin ɗaukarta Shareff ɗin yake yi tai saurin ja da baya cikin zare idanu da bugawar ƙirji sakamakon ganin wanda batai zaton gani ba.
“W…waya kawoka gidanmu?”.
Ta faɗa idonta kar a kansa kamar yanda shima ita ɗin yake kallo. Su kuma su Abie su dukan suke kallo. Tattausan murmushi ya saki yana mai janye idanunsa cikin na Shareff da yay wani irin mugun kicin-kicin da fuska, akan fuskarta ya maida cikin ɗaga kafaɗa yace, “Ina tare da Daddyna ne. Amma badan nasan nanne gidanku ba Beauty ”.
Sau ɗaya ta kalli abokin Abie ɗin ta maida kanta ta duƙar. Cikin sake faɗaɗa murmushi Alhaji Abu kalla ya dubi ɗan nasa da ƙyau. Kansa ya shafa yana mai kauda kai da sakin ƙaramar dariya. Alhaji Abu Kalla yay ƙaramar dariyar shima da ɗauke idonsa ga ɗan nasa ya maida ga Abie da shima dai murmushin yake da sonjin ƙarin bayani……….✍