BABU SO 16

Shawarar da suka bata ce ta sata goge duk wani ɓacin ranta har na rashin dawowar Shareff gidan har yanzu. Wanka tayi tare da tsara kwalliya mai ma’ana. Ta tsuke cikin wandon jeans da top da sukai matuƙar fidda ainahin ƙyawunta da ƙyawun sura. Kamar yanda gidan ke kamshi itama kamshin take bulalawa. Ganin yanda tai ƙyau saida tai ɗan shot video tare da bin waƙar da akafi yawan challenge akanta a yanzu ta ɗaura a shafinta na tiktok da istagram. Ita ɗin mai followers ce, cikin ƙanƙanin lokaci likes ɗinta suka fara hauhawa, video ɗin ya fara trending ko’ina kamar ita kaɗaice ke lokaci. Sosai farin ciki ya mamayeta damuwarta ta ƙara gogewa baki daya musamman da ƴan koranta na kusa suna koɗata da zafafan Comments. Yayinda masu kishi da ita da ganin ta fisu suka fara jefa Comments na baƙar magana harda masu zagi, a gefe masu gaya mata gaskiya na jeho nasu akan ya kamata ta rage yin video da ƙananun kaya da gashi a buɗe kodan igiyoyin aure dake a kanta a halin yanzun. Su Sima ne suka taƙarƙare wajen maida murtani ga masu irin wannan Comments da masu zaginta, itako sai ma ta kashe datar acewarta sai Comments ɗin sun taru zatazo ta duba….
★★★
Ɓacin ran jin asalin abinda ya faru daga bakin Anam duk da bashi take faɗawa ba da tabbacin Fadwa ce ta kira Mommy ta sanar mata wannan Accident ɗin ya hanashi komawa gida. Dan ya tabbatar in har ya koma a yanayin da yake zai iya yanke mata kowanne irin hukunci da yazo masa a rai. A yanzu kuma baya buƙatar haka a garesu, dan bazai so ace daga yin aure sati ɗaya kwana biyar da tarewa hakan ya fara faruwa ba. Office ya wuce kai tsaye, inda Fharhan da Khaleel sukai mamakin ganinsa tunda sun san duk wani abinda zai iya kawosa office ɗin sun kai masa shi har gida ya duba.
Ko gaisuwar da sakatariyarsa ke masa bai amsa ba, hannu kawai ya ɗan ɗaga mata duk da washe baki da take faman yi da tayasa murnar aurensa. Har ya kama handle ɗin ƙofar office ɗinsa zai shige ya juyo. “Bana bukatar kowa yasan ina nan ok”.
“Yes sir”.
Ta faɗa cike da girmamawa a garesa. Shigewarsa yay harda murzama ƙofar key, bai zauna a cikin office ɗin ba ya shige ainahin ɗakin da yake gudanar da zane-zanensa. Har mafi yawan ma’aikata suka tashi babu ɗuriyarsa, Khaleel yaso shiga ya dubasa sai kuma ya fasa saboda tun bayan shigiwarsa ya biyo bayansa amma sakatariya ta sanar masa yace baya bukatar kowa.
Kiran sallar magrib ya sashi fitowa, shiru companyn alamar kowa ya tafi gida, sai masu gadi su biyu kawai dake gate. Nan ya tsaya yay salla tare da su a massallacin dake cikin company ɗin sannan ya fito. Harya ɗauka hanyar gidansa ya canja, gidansu ya nufa, sai dai kai tsaye a gate ɗin gidan su Anam yay horn, mai gadi ya buɗe masa ya shige.
Duk suna falo gaba ɗaya zagaye da Anam dake faman rakin za’a gasa mata ƙafa da ruwan zafi. Taƙi yarda Mamie tai mata hakama aunty Mimi da suka dawo ɗazun. Amrah ce ta kira Abie, isowar Abie ɗin kusan dai-dai da shigowarsa, kusan su duka suka juya suna kallonsa da amsa masa sallamar da yayi. Cikin girmamawa ya rissina ya gaida Abie da Mamie, aunty Mimi ma suka gaisa.
Tun shigowarsa ta ƙara ƙarfin kukanta, takuma ƙi yarda tako kalli sashin da yake. Haushinsa takeji sosai batare da tasan dalili ba. Takaici ya saka Mamie daka mata tsawa..
“Wai wane kalar iskanci ne hakan Anam? Shin ke ɗin ƙaramar yarinyace da kowa zaita fama dake akan abinda zai amfaneki…..”
Da ido Abie yay mata alamar tayi haƙuri, ta ɗauke kai da ƙoƙarin barin wajen cikin takaicin ƴar tata. Abie yay murmushi da maida kallonsa ga Shareff da ke faman daƙilar waya kamar bai san abinda ake a falon ba, sake kallon Anam ɗin yayi cikin sigar lallashi “Mamana to Yayanki yay miki ko?”.
Da sauri ta ɗago tana girgiza kanta, “Garama kowa yamin akan shi yamin Abie”. Ta faɗa cikin zafi-zafi da share hawayenta. Amrah ta taɓe baki da barin wajen, yayinda aunty Mimi da Abie ke dariya.
“To saboda mi baki son nashi? Bayan tun ɗazu muke nan ana fama dake ga ruwan har sun huce”.
“Aunty Mimi nidai bana so ke kimun”.
Aunty Mimi zata kai zaune Shareff da har yanzu bai nuna yasan mi suke ba ya dakatar da ita. “Aunty barta, a canja ruwan dai”. Babu musu Aunty Mimi ta bashi waje ya zauna, ruwan zafin ta ɗauka ta nufi kitchen. Anam kuwa ƙafarta ta shiga ja baya, sai dai ta kasa jan jikinta saboda table daya tokare ta. Shi dai bai kulata ba har aunty Mimi ta dawo da ruwan, Abie kuma dama yayi ficewarsa saboda wayarsa da aka kira. Ganin yanda ruwan ke turirin zafin ya ƙara ɗaga hankalin Anam, cikin marairaicewa take duban Aunty Mimi amma tai kamar bata gantaba itama.
“Ni wlhy bana son naka!!”.
Ta faɗa da ɗan ƙarfi da son sake jan jikinta baya ganin ya amshi towel babba da ƙarami a hanun aunty Mimi. Babban ya ɗaura akan cinyarsa batare da ko kallonta yayi ba, ƙafin kuma ya saka ƙaramin a ruwan zafin, ƙafar tata ya kamo takai hannu zata rike, wani mugun kallon daya sata janye hanunta babu shiri ya watsa mata,
“Idan hanunki ya sake kawowa nan saina ɓallashi shima kiyi jiyyarbaki ɗaya”.
Kamar ta rushe da kuka takeji, sai dai tayi alwashin bazata bar hakan ta faruba insha ALLAH. Yana ɗaura towel ɗin daya naɗoma ruwan akan kafarta dake kan cinyarsa alwashin nata ya zama tarihi, dan da gaske kukan ta sanya musu mai ƙarfi tana ƙanƙame ƙafar aunty mimi dake kusa da ita tana matso masa towel ɗin daga ruwan zafi.
Sosai yanda takeyi ɗin ke neman sakashi dariya, amma ya danne da ƙyar ya cigaba da daddana mata ƙafar a nutse. Ta haɗa uwar zufa kafin a gama, hatta da aunty mimi da tasha riƙo ta haɗa tata zufar dan ba riƙon wasa Anam tai mata ba. Su Amrah da kukan Anam ɗin ya sasu sake fitowa dole sun kasa daurewa sai dariya suke kwasa, aiko ta wawushi throw pillows ta shiga jifansu da shi. Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da ya shiga layin ƴan dariya da Abie ma ya dawo yana yin tasa a gefe, Mamie ma dake a kitchen dariyar take kwasa dan borin Anam dabanne dana kowa.
Ba ƙaramin ƙuleta dariyarsa tayiba fiye data kowa, shi dai da baisan laifinsa ba bai bartaba sai da ruwan ya huce ya shafa mata man da aka bata a asibiti sannan ya saki ƙafar da kumburin har ya fara saɓewa, sai ga mutuniyar gyangyaɗi na ɗibar idonta. Da ɗan sauran murmushin da bai bar fuskarsa ba yake tambayar aunty Mimi ko taci abinci dan yana son tasha maganinta.
“Inafa taci, tunda Aysha ta kawota fa takema mutane bore a gidan nan har sai da Mamie ta mata tas. Anam ɗin ya kalla cikin ido, babu zato hararar data wullo masa ta iso garesa. Da sauri ta kauda fuskarta dan batai tunanin zai juyo ba. Abie dake kallosu a gefe yace, “Bara na maidata ɗaki sai taci abincin acan kawai ta kwanta”.
Dakatar da Abie ɗin yayi cike da girmamawa, dan bai kamata shi yana wajen ba yabarsa yay jigilar ɗaukar Anam ɗin. Cikin matuƙar zaro idanu da suɓutar baki Anam tace, “Wai Yayan ne zai ɗauke ni?”.
Harara ya wurga mata, ta kauda kai gefe cikin ƙunƙuni take faɗin, “Ni dai ALLAH bana so, garama a nemomin wheelchair……..”
Ranƙwafowarsa kanta na shirin ɗaukar nata ya sata haɗiye abinda take faɗar da sauri tana ƙoƙarin zabura gefe………..✍