Labarai

Innalillahi Yadda Wata Amarya Tayiwa Kanta Bidiyo Tana Chanza Kaya

Wata amaryar sabon aure kamar yadda tace tsautsayi ya saka ta yin bidiyo lokacin da take chanza kaya bayan wasu kwanaki taji labarin an ganta a soshiyal midiya tana chanza kaya a cikin wani bidiyo wanda ta dauka da kanta.

Wannan amarya ta bayyana tayi wannan bidiyo ne Dan nishadi amma kuma daga baya zamo mata bala’i domin ta bayyana lokacin da taji labarin tama kasa dubawa domin ta tabbatar da gaske ne ko karya ne domin tana da tabbacin tayibidiyo tana chanza kaya.

Wannan amarya ta bayyana cewa “lokacin da ta dauko wayarta domin ta duba a inda akace an ga bidiyon nata ta kasa shiga domin tana da tabbacin shine a lokacin da ta shiga kawai sai taji numfashinta ya kokarin daukewa domin ta fuskanci tashin hankalin da bata taba ba.

Ta dalilin wannan bidiyo ba gidan mijina ba har gidan iyayena suka tsane ni wannan bidiyo ne yayi silar mutuwar aure na sannan na rantse da Allah bani bace na daura wannan bidiyo nasan dai nice nayi shi amma kuma ina da tabbacin daya daga cikin kawaye nane.

Domin waya ta ko mijina baya dauka nahi wannan bidiyo da sati daya aka daura shi kan soshiyal midiya a daidai wannan tsakanin lokacin babu wanda yayi amfani da wayata sai kawaye na da suke zuwa saboda sabon aure ne ina da tabbacin daya daga cikinsu ce tayi mun wannan zaluncin.

Shiyasa yanzu babu yarda a tsakanina da wata kawa yanzu haka bana da kawaye.” Ta kara da cewa zan baiwa yan uwana mata shawara domin nasan bani kadai ke yin bidiyo na aje ba wasu ma suna koba na chanza kaya ba zaka ga sunayi bidiyon rawa ko bidiyo tare da mijinsu.

Idan kunsan kunyi bidiyo bazaku boye shi ba inda sai an saka lambobin tsaro sannan za’a samu damar ganinsa to kuyi hakuri ku rufawa kanku asiri kada kuyi bidiyon nan domin kina bacci gidan mijinki ko iyayenki labari zaizo maki an ga bidiyon. Allah ya rabamu da mummunar kaddara ameen ya Alla.”

Wannan shine bayanin wannan amarya cikin hawaye.
Related Articles

Leave a Reply

Back to top button