BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 18

        ★★★★

  Duk da bata ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ba sai ta kasa sakewa da Yaseer gaba ɗaya yau. Kullum shike fita da ita su ciyo abinci a inda yasan za’a samu abinda take iya ci. Amma yau saita ɓoyema ganinsa. Daga salla ta maƙale a massallaci taƙi fita. Sai ma ta ɗauka alkur’ani tahau karantawa.
       Sai da ta daidaici lokaci yaja sosai sannan ta fito. Kamar jira tana fitowar wani abokin aikinta yazo ya sanar mata tana da baƙo. Da mamaki take kallonsa dan bata tunanin wani zai iya zuwa wajenta a yanzu. Daga Muzzaffar har Dr Jamal bata tunanin ganin wani anan, garama Muzzaffar yakan zo idan ya daidaici sun tashi yace zai ɗauketa sai dai bata taɓa yarda ba. Kamar bazata je ba sai kuma taga gara taje dai taga wanene.
Turus tayi lokacin data iso taga mai kiran nata, zaune yake a cikin mota sai dai ƙafarsa ɗaya na waje dan ƙofar a buɗe yake……….✍????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button