BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 19

Bata buƙatar zaman tunanin abinda ya shafi waninsu, dan haka tai connecting bluetooth ɗinta ta manna a kunne. A hankali takai kwance bisa grass carpet dake a ɗan ƙaramin garden ɗin dake bayan ɗakin aunty amarya tana lumshe idanunta cike da nishaɗi, dan waƙar da take saurare tana matuƙar sonta, mawaƙin ɗan ƙasar malaysia ne, waƙar ma anyitane da yaren malay sai dai an cakuɗa da turanci. Tayi nisa sosai wajen sauraren waƙar fuskarta shimfiɗe da murmushi, ga idanunta a lumshe sanyin inuwar wajen na ƙara girmama nishaɗinta, bakinta sai motsawa yake a hankali alamar bin waƙar takeyi….


Jin ƙamshinsa ya ƙara ƙarfi cikin hancinta ya sata kasa cigaba da jurewa ta buɗe ido a hankali batare da tabbacin mai ƙamshin bane a wajen. Sai dai kuma cin karo da shi ɗin tsaye ya sakata ɗauke numfashi na wucin gadi. Da sauri ta tashi zaune duk tana jinta a daburce, hijjab ɗinta dake gefe ajiye ta ɗauka ta rufama jikinta dake sanye da wando three quarter da top ƙarama, zafine ya isheta ta sakasu kasancewar a ɗaki take, sai da taji hayaniyar mutane zasu dameta ta sako hijjab kawai ta fito, ganin babu kowa anan ya sata cirewa ta ajiye dan ta samu iska mai ƙyau ta shigeta.


Rigarsa ya ɗan tattare sama ya zauna shima bisa grass carpet ɗin dake a share tas dan aunty amarya kullum cikin kulawa take da wajen saboda tsananin son garden da takeyi. Mace ce ƴar gaye mai son hutu da gudun yawan hayaniya. Duk da Anam taji wani irin da zaman nasa wajen amma sai ta dake abinta. Sai dai ta kasa cigaba da bin waƙar daketa maimaita kanta. Shima da tun zuwansa wajen baice komai ba kallonta kawai yayi na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya kai hanunsa kunnenta ya zare bluetooth ɗin ya saka a nasa kunnen. Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, ya lumshe idanu ya buɗe tare da kauda su a kanta yana sauraren waƙar………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button