BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 20

20

………“Waye mawaƙin nan?”.
Cikin shakku da mamakin ta kallesa. Ganin zai kallota tai saurin janye idanunta a kansa, ta bashi amsa cike da basarwa.
       Ɗan Murmushi yayi dan ya riga ya ganta. “Ya iya waƙa gsky, kuma cikin nutsuwa da ma’ana”.
     Itama Murmushi tai a karon farko tana dubansa. “Shiyyasa nake son waƙoƙinsa sosai nima ai. Bashi da hayaniya, sannan duk abinda zai faɗa yakan dace da furicin zuciyoyi”.
         Tsareta ya ɗanyi da idanunsa, hakan yasa ta kauda nata. “Wane furucine ke dacewa da ma’anar zuciyoyi?”.
     A yanda yay tambayar tamkar mai raɗa ya sata juyowa ta sake kallonsa, sai kuma ta janyesu har yanzu murmushinta bai ɓace ba. “Yaya bai zama lallai tunanina dana kowa yazam iri ɗaya ba ai, zata iya yuwuwa nice kaɗai ke fassara haka ko fahimta a lokacin da nakejin waƙoƙin nasa”.
      “Uhhm nice. Kinga nima sai ki turamin maybe na fahimci irin taki fahimtar ko! Ki samun duka waƙoƙin sa ta WhatsApp”.
           “To ai bani da number ka”.
     Cikin ido yake kallonta, ta risinar da nata dan bazata iya jurewa ba. Shima sai ya ɗauke nasa ya maida ga tsuntsaye biyu dake shan ruwa a ɗan kaskon da aunty amarya kan zuba dan su. “Baki so hakan bane shiyyasa baki da ita”.
     Murmushi kawai tayi, amma batace komai ba, ta dai cigaba da kallon tsuntsayen kamar yanda shima har yanzu idonsa na kansu. Shiru kusan mintuna uku, tashin tsuntsayen ya sashi katse shirun nasu da faɗin, “Zanyi tafiya zuwa China, kuma zan jima dan zan samu a ƙalla kwanaki ɗari acan ko ƙasa da hakan insha ALLAH”.
       Mamakinsa ya sata ɗagowa ta dubesa, kasancewar nasa idon na kanta ya sashi ɗan lumshewa alamar tabbatarwa… Bata da zaɓin daya wuce kaɗa masa nata kan itama. “ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada abinda za’aje nema mai albarka. Ya tsareka daga haramun, ya haɗaka da halal”.
     Ajiyar zuciya yaja mai ƙarfi, har takai ta sake ɗagowa ta kallesa, murmushi ya sakar mata, irin wanda zata iya rantsewa bata taɓa cin karo da shi a gareta ba. Ta ɗanyi tsammm tana kallonsa, gaba ɗaya ganin al’amarin nasa take na yau kamar almara. Lakace mata hanci da yay ya sata saurin ɗauke kai cike da kunyar kanta. Ya ɗan murmusa yana gyara zamansa. “Zaki koma gidana k da Aysha ku zauna har na dawo”.
       “What! Yaya ni ɗin?”.
   A yanda tai maganar ya sashi kafeta da idanunsa sosai. “Bazakije ba kenan?”.
     Fuska ta ɓata da tura baki gaba, “To ai ni dai kasan bama shiri da matarka”. 
     “Idan kikaje zama yanzu ai sai ku fara shirin kafin na har abada”.
Ba wani fahimtarsa tai sosai ba saboda da hausa yay maganar, amma sai ta girgiza kanta. “No bazamu taɓa shiri da matar can taka ba. Dan nama kusa fara kai mata naushi idan tana cigaba da min kallon banza. Karta ɗauka tsahonta da girman jiki zai razana ni”.
      Yanda take maganar cike da masifa da tsiwa ya bashi dariya sosai. Ya kauda kai gefe yana murmushi. Kafin ya sake juyowa fuska a haɗe yana kallonta. “Matar tawa zaki nausa?”.
    Batace komai ba, sai dai ta sake tura baki gaba. Zaiyi magana ring ɗin wayarsa ya dakatar da shi, Mommy ce, dan haka yakai kunne cike da ladab yay sallama.
     “Kana ina ne wai Shareff? Ga matarka sai amai take anan duk ta galabaita kazo kuje asibiti”.
          “Ya ALLAH!”.
    Ya faɗa a hankali yana lumshe ido. “Okay Mommy ina zuwa. Amma bara na kira Jamal kin san yau weekend ne ba lallai mu samu yanda muke so a asibitin ba”.
    “To ya hanzarta dan ALLAH”.
“Okay bara na kirasa ɗin”.
     Koda ya yanke wayar kasa haƙuri Anam tayi, dan bata san wa akace baida lafiyar ba. “Yaya waye za’a kai asibiti?”.
            Yana ƙoƙarin kiran Dr Jamal ya bata amsa kai tsaye. “Fadwa ce keta amai wai, duk ta galabaita”.
    Sosai ta nuna jimaminta kasancewarta mutum mai tausayi. “Ayya ALLAH ya bata lafiya, dama bata da lafiya kuma ka yarda ta fito Yaya?, ai da ka barta a gida tunda kowa yasan ciwo”.
         Numfashi ya ɗan furzar, rashin ɗaukar wayar Dr Jamal ɗin ta bashi damar bata amsa. “Bawai kwance take ba, yanzu ma inaga taji ƙamshin abinda bata so ne shine aman yazo”.
      Kallonsa tai cikin mamakin amsar tasa, sai dai kafin tace wani abu kiran Mommy ya katseta. Ɗagawa yay yana mikewa. “Mommy na kira bai ɗaga ba maybe baya kus… Yauwa gashi ma yana kira ina zuwa”. Yankewa Mommy tai, shi kuma ya samu damar ɗaga kiran Dr Jamal ɗin. Ya ɗan matsa da ga wajen Anam ɗin suna magana. Da kallo ta bisa, sai kuma ta ɗan ɗage kafaɗa da ɗauke kanta cikin ɗan taɓe baki. Hijjab ɗin da taketa faman ƙudundune jikinta ta warware ta sanya da ƙyau itama ta miƙe da nufin komawa sashen aunty Amarya tai kwanciyarta kawai ko ɗan chart tayi da ƙawayenta na Malaysia.
      Ya gama magana da Dr Jamal ya juyo kawai ya hangota har takai ƙofar baya ta kitchen ɗin aunty amarya. Idanu ya tsira mata harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan ja numfashi tare da barin wajen shima.

★★★

     A sashen Mommy Fadwa sai sake langaɓewa take ganin yanda Mommy da Mamah suka rikice. Dan itama Mamah (Gwaggo Haliman) tazo wajen saka ranar ta Maheer. A haka ya shigo ya samesu zagaye da ita. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana miƙa masa hannu wai itafa yazo zata mutu. Cijewa yay yayi kamar baiga hanun da take miƙo masa ba, koba komai ai sa raga dan iyayensu. Sannu yay mata tare da zama yana gaida Mahmah. Cikin kulawa ta amsa masa itama. “Dama bata da lafiya ne haka Babana?”.
     Ɗan duban Fadwan yayi ya janye idanunsa. “No Mamah bawai tana kwance bane, kawai dai idan taji ƙamshin abinda bata so ne take amai, amma baima taɓa kaiwa kamar na yau ba”.
    Kallon juna Mamah da Mommy sukai, kowanne zuciya cike da son ƙarin bayani, sai dai sun san ba lallai su samu daga Shareff ɗin ba bara kawai su jira zuwan Jamal. Babu ko wani jimawa Jamal ya iso, Shareff ɗinne ya fita ya shigo da shi. Bayan ya gaishesu ya ɗan yima Fadwa tambayoyi tana amsa masa da ƙyar. Da ga ƙarshe ya bata tsinken gwaji.
     “Inaga yi amfani da wannan mugani ko abinda nake zargi ne. In ba shi din bane sai na ɗeba jininki”.
   Mommy ce ta amsa, ta kamata suka shiga toilet ɗin nan cikin falo. Bayan wasu mintuna suka kawo masa tsinken kamar yanda ya bukata. Murmushi ya saki yana mai kallon Shareff cikin ido, ya ɗauke kansa da maidawa gasu Mommy. “To inaga ma basai ta kaimu da gwajin jininba a yanzu-yanzun, dan abinda nake zarginne dai. Ko zuwa monday zata iya zuwa asibiti ta sameni ALLAH ya inganta ya ƙara lafiya. Bara na bata wannan maganin zai sa ta ɗan samu nutsuwa daga galabaitar da tai nayin aman”.
      Sosai bakunan su Mommy yake a washe, yayinda su Hassan suka cika falon da ihun murna suna faman rungume Fadwa. Shi dai uban gayyar tuni sun fice shi da Dr Jamal, sai dai har cikin ransa yaji daɗi duk da ya jima da zargin hakan a ransa. Dr Jamal ya sake masa Congrat, cikin tsokana yana faɗin, “Lallai abokina ka zama namijin duniya, irin wannan bugu na daga kai sai mai tsaron gida haka. ALLAH ya inganta mana”.
      “Ɗan iska kaji da shi dai. Yanzu ina ka nufa?”.
    “Gida ya kamata na koma, amma tunda ka kawoni nan nima bara naima tawa flower ɗin barruwa”. Ya ƙare maganar yana laluben number Anam. Sarai Shareff ya fahimcesa, dan haka baice komaiba sai ma basar da zance yay kamar baiji ba. Kusan sau uku yana kira ba response, ya ɗan ɗage kafaɗa yana duban Shareff. “Musty inaga yarinyar nan bata kusa da wayar. Bara kawai na wuce na dawo taɗin dare. Yaushe ne tafiyar taka jibin?”.
       “Zan wuce da safe ne dan zan fara shiga Abuja, da ga can zan wuce”.
    “Okay to da yamma zan shigo gida insha ALLAH”.
    Sallama sukai ya wuce, shi kuma ya koma wajen su Mommy da suka dasa sabuwar tarairaya ga Fadwa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button