BABU SO HAUSA NOVEL
BABU SO 25

Khaleel da kukanta ke ƙara ƙona zuciyarsa da takaicin su Mommy ne ya shiga lallashinta, da ƙyar ta ɗago idanunta da sukai jajir tana kallonsa. Zatai magana ya girgiza mata kai alamar tai shiru. Shirun kuwa tayi sai dai hawayenta sun kasa tsayawa. Khaleel ya miƙa mata goran ruwa dai-dai kira na shigowa wayarsa. Ganin mai kiran ya sashi ɗagawa babu ɓata lokaci ya kai kunne sa.
“Bata wayar”. Daga can aka faɗa cikin bada umarni. wayar ya sake miƙa mata. Bata musa ba ta amsa tana cire goran data sha kusan rabin ruwan cikinsa. A jajjare ta dinga sauke ajiyar zuciyar dake shiga har cikin kunensa daga can………✍