BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 30

30

……….Ganin tanata bubbuɗe abincin tana nuna masa ta kurma yay mata nuni da fruit salad kawai. Ta nuna masa abinci, yay mata alamar 1spoon kawai. Yanda ya buƙata haka tai masa, sai dai tasa masa haɗin salad a gefen shinkafar da ɗan yawa saboda tasan yafi buƙatar hakan. Da idanu yay mata alamar ‘thanks’ ta sakar masa murmushi.


         Sun fara cin abincin yay sallama da wanda suke wayar ya ajiye. Harya maida hankali ga abincinsa ya ɗago ya kalla Aysha. “Ina Anam?”. Ya faɗa a taƙaice. “Yaya tana ɗaki bata da lafiya, nayi-nayi ta taso taci abinci amma taƙi kuma ko magani bata sha ba”. Idanu kawai ya zubama Ayshar, sai abincin dake bakinsa da yake taunawa a hankali. Sai kuma ya janye kamar baiso yace, “Kiramin ita”. Mikewa Aysha tai da faɗin to.
      Da ƙyar ta taso Anam, amma da tace bazataje ba ita abarta. Sai da Ayshan tace, “Kin san dai zai iya zuwa har ɗakin nan ya ɓata miki rai ko”. Kamar bazata tashin ba sai kuma ta tashi tana ɓata fuska ga idanunta jazur. Ya ɗan juya musu baya, dan haka har suka ƙaraso wajen bai ɗago kansa ba. Sai da Fadwa tai magana idonta akan Anam datai gefe da fuska sannan ya ɗago. Kallonta yay da ƙyau ya janye idanunsa. Hakan yasa Fadwa sake yin magana cike da kissa. “Baki da lafiya kuma sai kije ki kwanta da ciwo a ɗaki Anam?”.
    “Uhhm”.
Kawai Anam ɗin tace a taƙaice, amma ko kallonsu taƙi yi daga ita har mijin nata. Murmushi Fadwa ta sake saki a zahiri, sai dai a ranta daɗin damar data samu takeyi, cikin sake sakin fuskarta tace, “Kije ɗakina saman mirror cikin First aid box akwai maganin zazzaɓi sai ki duba wanda zaki iya sha”.


        Yanzu kam sosai ta juyo ta zuba mata idanu, mamakin kissa da sabon salon Fadwan fes a kan fuskarta, sai dai kafin tace wani abu Shareff da yay kamar bayajinsu ya katseta. “Ki wuce ki ɗakko kizo kici abinci kisha”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa, ta jefama Fadwa dake murmushi har yanzu wani kallon banza ta wuce zuwa bedroom ɗin nata da yau ne karon farko da zata shigesa.

Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo tana taɓe baki sannan ta nufi mirror zuciyarta na ƙoƙarin danne abinda ke taso mata saboda kayansu data gani a watse a ƙasa da saman gado alamar ansha bidiri dai. Magunguna ta samu zube akan mirror ɗin wanda har ta ɗauke kanta ta kasa sai da ta sake kallonsu.


     Wani irin mummunar bugawa ƙirjinta yayi lokacin da idonta ya sauka akan sticker ɗin ɗaya daga cikin magungunan. Batama san sanda tai wurgi da maganinba ta fasa ƙara dayin tsalle gefe jikinta na maƙyarkyata. Aysha da Fadwa har rige-rigen isowa ɗakin suke. Yayinda uban gayyar ya shigo a ƙarshe fuskarsa a haɗe. Aysha dai dama kanta tayi, Fadwa kam dariya ta fara sai dai shigowarsa ya sata gimtsewa da sauri itama ta nufi Anam ɗin. Da robar maganin data cillar yaci karo, ya ɗauke kansa da maida dubansa gareta saboda abinda take faɗa tafukan hanunta rufe da fuskarta taƙi yarda Aysha ta buɗe.
      “ALLAH ya isa! ALLAH ya isa ƴar iska wayyo Mamie na ban yafe ba ban yafe ba…..”


    “Ikon ALLAH badai mu bane ƴan iskan ko Anam?!”. Fadwa ta faɗa cikin tafa hannaye da nuna damuwa na makirci saboda ganin ya shigo. Shi kuma ɗakin yabi da kallo har idonsa ya dawo kan robar data cillar ɗin, baima san sanda yakai hannu ya ɗauka ba yawun bakinsa na ƙoƙarin kamewa. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ya buɗe akan Fadwa ransa a ɓace. Sai da gabanta ya faɗi ganin yanda idonsa ya kaɗa yay jazur cikin lokaci ƙanƙani.
      “Kamata ku fita!”.


Ya faɗa cikin bada umarni ga Aysha. Hanun Anam daketa faman jera ALLAH ya isa har yanzu ta kama suka fice. Sai da suka fice ya tako ya zauna a bakin gadon ya dafe kansa bayan ya ajiye maganin gefensa. Ƙoƙarin danne tsoron dake faɗi a ranta tai ta nufesa, cike da kissa takai hannu kan kafaɗarsa. “Soulmate wlhy na man….”


      “You’re vary stupid da zaki faɗamin kin manta. Kinsan suna shigo miki ɗaki zaki ajiye waɗan nan abubuwan a inda idonsu zai gani. Koke da kika saka kanki ajiyewar dole ne sai kin bar stickers nasu a jikinsu saboda baki da hankali!!”.


         Yanda yake masifa ba ƙaramin bugu zuciyarta ke mata ba. Ta shiga girgiza masa kai dan yana yine kamar zai mareta. Ta matso da nufin rungumesa ta basa haƙuri ya tureta ya fice. A falo ya sami su Anam har yanzu tana faman kwarara ALLAH ya isa, Aysha na tambayarta wai miya faru ta kasa bata amsa.
     “Shut up!! stupid!”.


Ya faɗa a tsawacen daya tilasta Anam gimtse bakinta da janye hanunta dake akan fuskarta har yanzun. Da sauri ta sake maidawa ta rufe ganinsa tsaye a gabansu. “Idan kika ƙara wani magana anan saina mareki, dalla kuwuce kuci abinci”. Kusan a tare duk suka miƙe zuwa dining ɗin, yabi bayansu yana jan tsaki mai ƙarfi. Aysha ta zuba mata abincin, jin yanda yaketa faman jan tsaki a jajjere ya sata cin abincin badan taso hakan ba. Laumarta baifi uku ba tai yunƙurin mikewa ya watsa mata harara. Da sauri ta koma ta zauna kamar zatai kuka.


        A daidai nan Fadwa ta fito jiki a saɓule, sai dai daka kalleta zaka san tayi kuka. paracetamol ta ajiye gaban Anam tana satar kallonsa, fruit ɗinsa yake sha sai dai fuskar tamkar zatai aman wuta. Kujera taja ta zauna. shiru wajen ya ɗauka babu mai ko tari sai ƙarar cokula. Anam ce ta fara turo nata dan da gaske zazzaɓin nata neman dawowa sabo yake. Aysha ta ɓalla mata magani ta bata. Amsa tai tasha babu musu, tana kammalawa tabar wajen da ɗan gudu-gudu dan karma yace zai dakatar da ita. Itama Aysha sauri-sauri tai ta gama ta gudu ta barsu a wajen……

★★★

        Washe gari duk da ta sake tashi da zazzaɓi tana idar da sallar asuba tahau haɗa kayanta da suka rage, dan tun dare ta tattare wasu. Tambayar duniya Aysha ta mata akan miye take haɗa kaya bata tanka mata ba. Har Ayshan taji haushi tai shiru, tamayi kwanciyarta ta juya mata baya. Koda taji ƙarar jan akwati da fitarta bata motsaba tamayi kamar tai barci ne.


    Taji daɗin ganin babu alamar wani ya tashi a gidan, ko mai gadi ma sai da ta ƙwanƙwasa masa ƙofar ɗaki ya fito ya buɗe mata da mamakin ganinta da kaya. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska bai bashi damar mata tambayar dake a ransa ba. Duk da nauyin akwatin nata ga wata jikkar data ratayo haka taita jansa har titi. Hijjab din Aysha ne har ƙasa jikinta saboda da kayan barci ta fito. Sai da ta iso har babban titi ta samu napep, ALLAH ya sota ma babu nisa zuwa titin. Kai tsaye ta faɗa masa anguwar dazai kaita. Ya faɗa mata kuɗin tace suje kawai.


       Sanda suka iso gidan ba kowama ya tashi ba musamman yara dake hutawa saboda cikin hutu ake. Da mamaki Mom ke dubanta, ta tura baki gaba da faɗin, “Mom bani two hundred zan bama maigadi a wajensa na amsa naba mai napep.” Komai Mom batace ba ta mika mata five hundred. Fita tai ta kaima baba maigadi amma sai yamaƙi amsa. Dawowa tai ta bama Mom kuɗin tare da faɗawa saman three sitters ta kwanta. Mom dai na binta da kallo. “Lafiya da kaya da sassafen nan?”.


       “Ni Mom na gaji dama da zaman gidan can ALLAH. Kawai na taho ne ni tunda Yayan ya dawo ai”.
         “Hummm”.
Kawai Mom ta faɗa ta ɗauke kanta. Anam kuwa barcine ma ya ɗauketa take a wajen dan jiya kasa barcin kirki tayi, haka kawai ta dinga mafarkin abinda ta gani saboda ta saka abin a ranta harda amai tai kusan sau uku a daren jiya dan ƙyanƙyami abin ya dinga bata. Tunda take bata taɓa ganin halittar namiji ba a rayuwarta koda a hoton ma saboda tsayin daka na tarbiyyar iyayyenta a kanta, duk da kuwa ta tashine a wani yanki da yasha banban da nata. Hatta wayarta tanada matakan tsaro kashi-kashi da idon iyayenta ke akai akoda yaushe saboda bata kariya daga faɗawa tarkon musibar zamani na gane-gane dake zama silar watsa tarbiyyar yaranmu da yawa a wannan zamanin ta hanyar waya..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button