KannywoodLabarai

Saidai Ku Cigaba Da Zagina Ina Nan Kan Ra’ayina Na Sukar Masu Tura ‘Ya’ya Almajiranci – Nafisa Abdullahi

A rubutu da tayi a shafinta na Twitter mai suna @NafisatOfficial, ta ce: “Ya bayyana cewa wasu mutanen ba su ji dadin maganar da nayi ba, na cewa a daina haihuwar ‘ya’yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba. Eh, na san an ce ku yi aure ku hayayyafa, amma a ina aka ce ku haifa ‘ya’yan ku watsar da su?.

Kun cika son bada kariya ga abunda kuka san cewa ba daidai bane. Suna cewa wai in bari in yi aure kafin in tsoma bakina a cikin irin wannan maganar, to ta ina rashin aurena ya shafi wannan maganar?”

Jarumar ta cigaba da cewa: “A yau idan nace ba zan yi aure ba, babu wanda ya isa yayi wani abu a kan hakan. Ma’ana ra’ayinku a kan aure na ba shi da wani amfani.”

“Duk wanda yaji haushin nace a daina haihuwar ‘ya’yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba, To ya tabbata yana daga cikin matsalolin da muke fuskanta a arewa ko a kasar baki daya.

“Sannan a kalla abinda zai iya kawai shi ne ya yi zagi ko yace je ki yi aure, shikenan! Allah ya kyauta.”

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button