Labaran Kannywood

Rahama Sadau kenan rike da kyautar da akayi mata ta Gwarzuwar kasashen a Afrika

Kamar yadda muka labarta muku a satikan baya idan baku manta ba,an bawa Jarumar kyautar kambun Gwarzuwar Jarumar Kasashen Afirika.

Rahama din ta wallafa hotunan ta masu jan hankali tare da kyautar da akayi mata din,mutane da dama cikin su harda Abokan sana’ar ta sun tayata murna matuka.

Sai dai a wani bangaren guda kuma wasu suna ganin ai wannan ba abun azo a gani bane saboda kyautar Gunki kawai aka bata.

Haka dai mutane masu mabanbantan ra’ayoyi sukaci gaba da bayyanawa.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button