BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 37

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

37

………Kiran sallar farko ya farka, dama ba wani barcin kirki yayi ba, dan bai baro asibiti ba a daren jiya sai kusan ƙarfe ɗaya, shima sai da Abie ya korashi dan suma duk lokacin suka wuce aka bar aunty Mimi kawai da Anam dake barci. Sai da ya watsa ruwa kozai samu ƙarfi sannan yay alwala ya fita massallaci, gari ya ɗanyi shaa ya shigo gidan, ya ɗan ja tsaki dan gaba ɗaya gidan yay masa wani irin girma, yayi niyyar sakama Fadwa ido yaga iya gudun ruwanta amma a yau yaji bazai iya hakan ba, dan ya kula sai ya fito mata ta inda bata zato sannan zasu samu dai-daito. Wayarsa ya ɗauka yana zama bakin gado dayin ƙaramar ƙwafa, aunty Mimi ya kira, bugu biyu kuwa ta ɗauka suka gaisa, ya tambayi yamai jiki tace da sauƙi amma bata tashiba har yanzun dai.
     “Masha ALLAH, nima zan shirya yanzu zan shigo, ko kuna buƙatar wani abu ne shiyyasa na kira?”.
    Aunty Mimi ta amsa da “To ALLAH ya kawoka lafiya. Bama buƙatar komai tunda bata tashiba balle aji ko ita tana son wani abu ɗin”.
        “Okay to sai nazo”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Bai wani jima ba ya kammala shiryawa ya fice, sai da ya shiga mota ya fara kiran number Fadwa, harta tsinke ba’a ɗagaba, ya sake tsuke fuska ransa na ƙara ƙuna dan ya tsani raini a rayuwarsa. Wayar ya jefa kujerar gefansa yay ma motar key ya fice.

        Gama wayar aunty Mimi babu jimawa ta farka, da taimakonta taje toilet dake a cikin ɗakin, jikinta sam babu ƙarfi, hakan yasa Aunty Mimi taimaka mata ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi sosai sannan tai alwala suka fito. Murya a karye irin ta mara lafiya tace, “Ummie bazan iya salla a tsaye ba ina ganin jiri”. Taimaka mata aunty Mimi tai ta zauna kan sallaya, dai-dai nan masu gyara ɗakin suka shigo tare da wata nurse. Su dukansu suka gaida Aunty Mimi da tambayar mai jiki, ta amsa musu da fara’a.
        Gyaran gado mai sharar ta fara, yayinda Nurse ɗin ke tsaye tana jiran Anam ta idar. Sai da tai addu’a Nurse ɗin ta taimaka mata ta koma saman gado, kwancia ta ƙarayi dan gaba ɗaya batajin ƙarfin jikinta. Harta lumshe ido sallamarsa ta sakata buɗewa, kallo ɗaya tai masa ta maida ta rufe abunta fuskarta na sake tsukewa. Gaisheshi Nurse ɗin tai hakama mai sharar, ya amsa sama-sama yana ƙarasawa gaban aunty Mimi ya ajiye ledojin hanunsa. Aunty Mimi dake dubansa da murmushi tace, “Babana mun hanaka barci ko?”.
      Murmushi ya ɗanyi da kaiwa zaune a ɗayan gadon dake ɗakin, ya rissina yana gaisheta kafin ya bata amsa da “Ko badan kuba dole na fito ai yau akwai office”.
        “Tofa ango guda da zuwa office”.
   Idanunsa ya sauke akan Anaam batare daya ce komai ba, cikin son basar da zancen yace, “Har yanzu bata tashi ba?”. Kallon Anaam aunty Mimi tayi, ganin tayi luff kamar bata jinsu tai ƴar dariya. “Yanzun nan tai salla ma, tana komawa saman gadon kana shigowa. Sallamar Doctor ta hanashi cewa komai, tare yake da nurse ɗin ɗazun, ya miƙa masa hannu suka gaisa yana tambayar yamai jiki. Da aunty Mimi ma suka gaisa sannan ya ƙarasa gaban gadon.
       Cikin tsokana yace, “My patient barcine ko likimo?”. Duk da ta jisa bata motsa ba, sai dai taɗan buɗe idonta ta kallesa ta maida ta rufe. Murmushi yayi da sake faɗin, “Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya. Sister Rabi taimaka mata ta tashi”.
     Da taimakon Nurse daya kira sister Rabi ta tashi, sai langaɓewa take kamar zata saki kuka, cikin lallashi doctor yake mata ƴan tambayoyi akan yanayin jikinta tana bashi amsa, ko sau ɗaya taƙi yarda ta kalli sashen da Shareff yake. Bayan doctor ya kammala ya bada umarnin a bata abinci ko kaɗan taci zai aiko a sake saka mata ruwa da allurai uku, dan suna buƙatar ta samu barci sosai da alamu suka nuna kwana biyu bata samu. Koda ya fice shi da Nurse ɗin bata yarda ta kalli inda yaken ba, saima ƙoƙarin kwanciya da taso yi aunty Mimi ta dakatar da ita. Idanunta ta ɗago cikin marairaicewa ta kalli aunty Mimi, har ƙwalla sun taru dan ma gilashin idonta ya ɗan ɓoyesu duk da fari ne tas, karaf suka haɗa ido, ta sake yin kicin-kicin da ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. Shiko ya kafeta da nasa idanun sai dai shima tashi fuskar tsamm take babu wasa.
    “Ummie jiri”.  
Ta faɗa a hankali.
“Na sani mamana ki daure kici abinci kamar yanda doctor yace sai ki kwanta ɗin. Bata iya musu ba, dan haka tai shiru. Aunty Mimi ta bubbuɗe ledojin da Shareff ya shigo dasu, kayan tea ne a leda ɗaya, ɗayar kuma abincine dai-dai cin mara lafiya kuma abinda Anam ɗin take matuƙar so. Amma da yake daru takeji sai tace ita bata son shi, aunty Mimi sai lallashinta take amma ta kafe ita bata sonsa a kira Mamie ta kawo mata wani.
     Sarai yana jinsu amma bai tanka ba, sai danna wayarsa yake kai kace hankalinsa baya kansu sam. Ana cikin badaƙalar Khaleel ya iso. Cikin shirin office yake, ya gaida aunty Mimi da Shareff ɗin yana ajiye basket na abinci da Mom ta aikosa ya kawo. Kafin ya karasa gaban gadon yana kallon Anaam da ƴar sakin fuska dan shi murmushi ma kakan daɗe baka gani ba tare da shi. “A jiki yayi sauƙi granny tunda gaki zaune, jiya har mun fara ƴar ƙwalla da murnar cin gummba”.
    Murmushi ta saki tana kallon Khaleel ɗin kamar ba ita ke bori ba. “Kai Yaya Khaleel, kai ashe soma kake na mutu?”.
     Murmushi yayi shima a karon farko, “To Granny na sani ko lokaci yayi jikin tsufa”.
          Ta ɗan hararesa tana ɗauke kanta, dariya yayi nan ma. A ɗan shagwaɓe tace, “Yaya mika kawo min?”.
   “Breakfast ne Mom tace a kawo miki kafin su ƙaraso”.
   “Na gode”.
Ta faɗa tana maida dubanta ga Aunty Mimi da ke kallon Shareff daya miƙe fuskarsa kicin-kicin kamar zaiyi aman wuta. “Ummie zanci”. Da ga shi har Aunty mimi kallonta sukai, yay mata wani mugun kallo ya ɗauke kansa. Itama harara ta balla masa ta ɗauke nata idon. Sarai yaga harar dan haka ransa ya ƙara ɓaci, batare da yayima kowa sallama ba ya fice abinsa.
     Daga aunty Mimi har Khaleel da kallo suka bisa…..

        ★Yini guda ƴan dubiya nata leƙowa jefi-jefi, sai dai babu Gwaggo babu Mummy, Aysha ma satar hanya tai ta biyo su Mom da zasu zo tazo ta duba Anam ɗin. Dan Mommy ta hana yaran ɗakinta duka. Shareff dai bai sake leƙowa ba sai kusan takwas na dare, da alama daya tashi aiki sai da yaje gida sannan ya dawo nan dan jallabiya ce a jikinsa. Yanzu ma Anaam yitai kamar bata san ALLAH yayi ruwansa ba, shima kuma daga gaisuwa da yay da Aunty Mimi da wata ƴar uwar Mamie data zo duba Anaam ɗin yaja bakinsa ya tsuƙe. Aumty Mimi suka fita zataima baƙuwar rakkiya aka barsu su biyu. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar babu masu rai, sai ƙarar iskar fanka kawai kakeji, taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa sai faman cin apple ɗinta take da aunty mimi ta yanka mata hankali kwance. Idanu ya ɗan tsura mata amma duk da haka ta ƙi ta nuna tasan da zamansa….
      “A tunaninki wannan rashin kunyar taki zaisa ki samu biyan buƙatar taki?”.
    Shiru babu alamar tama jisa tanata dai cin apple ɗinta, ransa ya ƙara ɓaci, cikin jin zafi da ɗacin da muryarsa ta kasa ɓoyewa yace, “Oh ga mahaukaci na magana ko? K! Ki shiga hankalinki wlhy, inba hakaba zakisha baƙar wahala a banza stupid kawai”.
        Babu ko ɗar a cikin idanunta ta ɗago ta zuba masa su duk da suna cikin gilashi, “Yaya Shareff ALLAH bazai baka damar bani wahalar ba kuwa, dan hanyar jirgi daban ta mota daban. Aure ne dai nace bana so kuma komi za’amun bazan so ba dan inada wanda nake s……”
    Ji kake “bumm!” akan bakinta, sam batama lura da sanda har ya taso ya iso gareta ba. Ya ture hanunta da take ƙoƙarin ɗaurawa saman lips ɗinta ya maye gurbinsa da nasa yatsun biyu, cike da baƙar mugunta ya shiga murzasu. Duk da dukan da take kaima hanun nasa bai janye ba sai da ya tabbatar ya murjesu san ransa sannan ya saki. “Karki fasa rashin kunya, nima bazan fasa ɗaukar mataki akanki ba”. Ya ƙare maganar gab da fuskarta har yana busa mata numfashinsa da iskar bakinsa dake ƙamshin mouth freshener na banana.
      Kuka ke son taho mata amma tanata ƙoƙarin dannesa dan taci alwashin bazata sake barin hawaye akan fuskartaba game da wannan auren, zata ƙwaci kanta da ƙarfinta kuma duk abinda za’ai mata sai dai ai mata bazata zauna zaman aure da shi ba. Shima baibi takanta ba dan harya fice ma abinsa rai ɓace. Taja wani shegen tsaki da ɗaga gilashinta ta share ƙwallar da suka taru a fatar idon dan ta danne sauran ta hanasu tasiri. Koda aunty Mimi ta dawo bata tambayeta ina Shareff ɗin ba, da alama dai sun haɗu a waje ne.
      Daga ita har shi haka suka kwana rai a ɓace. Washe gari ma shine ya fara zuwa asibitin, sai da yaje wajen doctor ya biya komai ya basu sallana sannan ya iso ɗakin. Da aunty Mimi kawai yau ma ya gaisa, ƴar darun tasa na kwance ta juyama ƙofa baya baima san idonta biyu ko barci take ba. Shine ya sanar ma aunty Mimi an sallamesu, tai godiya ga ALLAH sannan ta miƙe ta fara haɗa kayansu. Ya ɗauki kayan ya fita da su, ita kuma ta tada Anaam da dama idonta biyu ta taimaka mata ta shirya sannan suka fito bayan doctor ya shigo sunyi sallama. Tsaye suka samesa a jikin motarsa yana waya da alama a cikin su Daddy ne. Ƙin yarda tai ta kallesa duk da shi tana jin nasa idon a kanta. Aunty mimi zata sakata gaba ta tirje akan ita dai baya take so, kokuma subi napep.
       Faɗa aunty Mimi ta fara mata dan ta kaita wuya kuma, shiko kamarma bai san sunai ba ya shige motar abinsa bayan ya gama wayar tasa. Dole dai ta shiga gaban bisa tursasawar aunty Mimi……..✍????

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button