AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 45-46

??45and46??

A hankali Ameelah ta fara bude idonta, momie na zaune gefenta tayi tagumi, ta miqe da sauri ta qarasa inda take!

Qarema dakin kallo Ameelah tayi kafin abinda ya faru da ita ya fara dawo mata a qwaqwalwa! A firgice ta miqe zaune, tasa hannu ta fizge qarin ruwan da akai matah sannan ta dora hannu akai ta fasa wata razananniyar qara, jikinta sai kyarma yake nan danan taa hada xufa tana wani irin kuka marar dadin saurare!

Su abba da hilal da suke zaune a waje sukaji karar ta da sauri suka nufo dakin..

Can muka hango momie maqale jikin bango ta dafe qirji cike da tsoro, daqyar ta iya bin bango har takai qofa nan suka hado da hilal da Abbah suna shrin shgowa tare da likita!

Momie kam bata bisu ba sai dai ta tsaya riqe da qofa, su Abbah suka qarasa inda take suna tambyarta meya faru? Sai mexai faru? Muryarta ko kadan bata fita! Sai wani zazzare edo take tana kallonsu, saikace bata sansuba, edonuwanta sunyi jajir, Har lokacin jikinta bai daina 6ari ba!

A tsorace likita ke mata gwaje2..
Tashin hankali na hango muku sosae a fuskar hilal dasu Abbah, momie kam har ta fara kuka tana sambatu abinda ya qara qular da Abbah kenan!

Likita ya dade yana mata gwaje gwaje kafin ya fara musu bayani “gsky wannan aikin bana asibiti bne, rashin lafiyar Ameelah har yanzu mun kasa ganoshi, amma ina baku shawara kuje wuren malamai ku nema mata taimaka!

Momie ta dafe kirji tace “na shiga uku! Wannan wane irin ciwo ne, Allah wannan sammu ne aka mata, ture ne za’a mata, domin mu duk danginmu babu mai jinnu! Koma waye sai Allah ya saka miki!

Abbah ya watsa mata harara yace “don Allah ki shga goma ba uku ba, lafiyar ‘yerki zaki nema ko kwasar ma kanki zunubi xaki tsayayi wurin zato?

Daukar Ameelah zamuyi mu koma da ita can gidanmu mu nema mata magani? Ta daga kai tana gurnanin kuka cike da tausayin ‘yer tatah!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button