BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 38

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

38

…………Duk da da sauran safiya hakan bai hana ta samu tarba daga mafi yawan jama’ar gidan ba. Musamman ma yaran dan suna shirin wucewa school ne suka iso. Duk sai da suka shiga sukai mata sannu da yaya jiki, bayan wucewarsu shima Shareff yay musu sallama ya fita dan wajen aiki zaije. Mamie da kanta ta taimaka mata tai wanka, bayan ta fito ta ƙara taimaka mata ta saka kaya sannan ta fiddota falo wajen su Daddy da suka shigo dubata.
Kanta a ƙasa ta gaishe su duk suka amsa mata da kulawa da tambayar jikinta. Abba ne yay ɗan gyaran murya idonsa a kanta. Ɗagiowa tai a hankali ta dubesu, ganin su duka ukun idonsu a kanta yake ta maida ta sake duƙarwa.
“Mamana!”.
Abba ya kirata cike da kulawa.
Cikin rawar murya ta amsa masa. Yay ɗan murmushi da sake gyara zamansa. “Kin yarda muɗin iyayenki ne bazamu taɓa cutar da ke ba?”.
Kanta ta jinjina masa tana haɗiye hawayenta. Ya cigaba da faɗin, “Alhmdllhi naji daɗi da kika fahimci haka, ina kuma fatan ki kasance mai biyayya tamkar yanda shima ɗan uwanki ya kasance amatsayinsa na namiji. Duk da nasan abinda mukayi munyisane akan gaɓar data dace akaran kanku bawai zumincinmu kawai ba. Ki ƙara daurewa ki zama mai haƙuri da biyayya, domin aure dai an riga an ɗaura, ba kuma yanzu aka ɗaurasaba ko jiya, an ɗaurashi rana ɗaya dana ƴar uwarki kamar yanda Yaya ya faɗa ranar a gaban kowa, sai da aka ɗaura naki da safe sannan aka ɗaura nata da azhur, hakan yasa ko shi Shareff bai sani ba, mun kuma ɓoye ne saboda wasu dalilai, hakama a yanzu mun bayyana a gareku da kowa ma saboda wasu dalilai. Dan haka zaki tare ranar juma’ar nan insha ALLAHU a ɗakin mijinki. ALLAH yay miku albarka, ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka da MANZON ALLAH zai alfahari da su kamar yanda muke fatan yay alfahari da ku da mu baki ɗaya.”
Kuka takeyi sosai. Sai tausayinta ya kamasu, kiranta Daddy yay ta rarrafa zuwa gabansa. Hanunsa ya ɗaura saman kanta ya shiga saka mata albarka da mata nasiha mai ratsa jiki tamkar yanda Abbah yay mata. Shi dai Abie bai ce komai ba yana dai kallonta ne kawai. Hakama Mamie da aunty Mimi. Sai da suka tabbatar ta tsagaita da kukan da takeyi sannan suka fice su duka, Aunty Mimi ce ta dawo kusa da ita, jikinta ta jawota ta rungume tana lallashinta, a haka su Mom suka shigo suka samesu ita da aunty Amarya. Suma dai nasihar sukai mata da lallashi. Daga ƙarshe Mom tace hajiyar sudan zata zo ta ƙarasa aikinta tunda wancan yabi iska.
Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka har barci ya kwasheta, bata kuma farka ba sai kusan azhar da hayaniya ta isheta. Wanka tai cikin rashin ƙarfin jiki sannan ta fito, ganin akwatuna barbaje a tsakkiyar falonsu ga mutane cike anata kallo ya sata komawa da sauri tana faman tura baki. Amrah ta kira cikin roƙo tace ta kawo mata tea, babu jimawa kuwa ta kawo mata tana tsokanarta da fara bata labarin kayan lefen da aka kawo mata. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta kora Amrah waje ta sakama ɗakinta key dan bata buƙatar jin komai. Saboda ma ta kauda abun a ranta sai ta ɗauki lap-top ta kunna film abinta, tana shan tea tanayi, data gama shan tea ɗin sai ta kwanta ta cigaba da kallon a haka tana jiyo hayaniyar gidan har lokacin sama-sama.

   A falo kam ƴan uwa da abokan arziƙi da makota kowa ya yaba da wannan lefe na girma. Babu fariyya a cikinsa kuma babu ƙaranta, ango Shareff ya taka rawar gani duk da ya haɗa lefen ne a ƙurarren lokaci dan Daddy ne ya bashi umarnin yinsa a cikin kwanaki huɗu kacal. Jiya da dare kuwa sai gashi da akwatina set biyu kamar yanda akayi na Fadwa. Sai dai waɗannan shi da Aunty Amarya suka haɗosu ba kamar na Fadwa ba da Mom ce ta haɗa Mommy ma ta haɗa set ɗaya.
 Bayan watsewar gidan Mamie ta samu zama da Anam. Nasiha tai mata mai ratsa jiki da ɓargo, wadda ta ƙara sanyaya ranta da sake sakata karaya. Ta fahimci kowa son wannan *_Auren ƙadda ko biyayyar?_* nasu yake a gidan, bata da wani mai goya mata baya akan ƙinsa sai Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima. Duk yanda Mamie taso daurewa itama kasawa tai saida tai hawaye, dama dauriya kawai take na rabuwa da tilon ƴarta. Sai dai idan ta keɓe tana kukanta ko kuma agaban Abie da shima dai dauriyar kawai yake sai dai yana lallashinta.

  Washe gari alhamis akaje aka tsantsarama Anam jeren daya girgiza zukatan su Mommy, dan kuwa akwai ƴan rahotonsu a wajen a cikin dangin mahaifiyar su Daddy da suke manne da Gwaggo Halima. Ranar ma dai ƙaramin hauka aunty Halima tazo sukayi da su Mommy a gidan, anan ne ma su Daddy suka san Fadwa na gida bata koma gidan mijinta ba kamar yanda mahaifinta ya sharɗanta. Rai ɓace Daddy ya nema ba'asi, dan shima birkice musu yayi fiye da yanda suke zato da tsammaninsa. Ai fa babu shiri Fadwa ta fadi cewar Mommy da Mahma (Gwaggo Halima) sukace bazata koma ba. Ran Daddy ya ƙara ɓaci, a take yanke yayma Mommy saki ɗaya. Tsitt gidan yayi na wucin gadi dan zuciyar kowa sai da ta girgiza musamman Mommy ɗin dake cika bakin idan ya saketa sai mi daga farko, dan ita a tunaninta fa Daddy cika baki kawai yake babu wani sakinta da zai iyayi. Zai ƙara na biyu Abie ya shiga roƙonsa da magiyar dan ALLAH kar yayi. Yana matukar jin nauyin Abie, dan haka yay shiru batare daya ƙarasa na biyun ba ya bar wajen yana huci. Itama dai Gwaggo jan Mommy tayi sashenta tana faman yimata faɗan katoɓarar tata.
 Ranar dai haka aka kwana gidan rai ɓace, yayinda Abba da kansa ya ɗauka Fadwa ya maida gidan Shareff. Duk abinda ke faruwa a gidan Maheer ya kira Shareff ya sanar masa dan yaje gidan gaishesu ya tadda ƙura ta tashi. Amma sai Shareff ɗin baije ba dan yasan zuwansa ɗin sabon masifane, kuma har yanzu tsoron haɗuwarsa yake da Mommy. Abbah bai baro gidan ba sai da ya haɗasu yay musu nasiha mai ratsa jiki, daga ƙarshe ya sa musu albarka da gargaɗin sake barin wata ɓaraka ta shigo musu da har zasu dinga kawota gabansu matsayinsu na iyaye, ya kamata su dinga juriyar sasanta kansu kamar sauran ma'aurata su riƙe sirrin gidansu. 

  Washe gari aka tashi da hidimar sabon shagalin biki, dan kuwa dai Abie ya shirya gagarumar walima dama tunda ALLAH bai cika masa burinsa na gayyatar tarin mutane ɗaura auren tilon ƴar tasa ba kasancewar an ɗaurashi a sirrance ne. Abin zai baka mamaki idan kaga yanda mutane ke ɓullowa tako ina, da wanda invitation ya sama a ranar ɗaurin auren Maheer da wanda ma ba'a gayyata ba. Dan danan fa gidajen suka cika taf.
 Mommy da Abie yay tsaye tun a daren jiyan Daddy ya maidata ɗakinta abin duniya ya gama isarta ita da gwaggo, sai dai Gwaggo ta hanata cewa komai sai danginta da suka iso gidan keta kananun magana akan ɓoye musu auren da akai tun farko, dan zuwa yanzu dai kowa ya shaida Anam itace Uwargida duk da ba addini ne ya wajabta hakan ba, amma ga al'ada irin ta bahaushe mukance wadda aka riga ɗaurama aure itace Uwargida musamman ma wannan da akai rana ɗaya. 
 Gwaggo Halima dai bata leƙo gidan ba ma, tana can itama tana zuba tata tijarar a gidan ta sai dai mijinta ya tabbatar mata ko sawun inuwarta ne ya fita gate a bakin aurenta kuma saki uku yake nufi, wannan shine ya hanata fitowa. Sai daita bada umarnin canja komai na Fadwa a gidan Shareff. Dan tun sassafe akaje aka kwashe kayanta tas na furnitures da labulale da wasu a kayan kicin aka zuba mata sabbi ƙal ƙirar waje wai duk dan dai kar Anam ta fita wani abu dan dukiyar da Abie da Mamie suka zubawa ɗiyarsu harma da Aunty Mimi sai yamaɗiɗi ake da shi a dangi. Wasu ma a waya suka gani sai kuma yau da aketa zuwa ganin amarya da masu zuwa gulma wai dannar ƙirjin Fadwa. (????Basai an dannemu ba ma ku kwantar da hankalinku mu bama kishi????).

  Amarya Anam data ci kukanta tun daga daren jiya har safiyar yau tayi ƙyau cikin kwalliyar haɗaɗɗen lesirin da Abie ya mata, aka kuma naɗeta cikin alƙyabba kai kace daga gidan sarauta aka ɗakkota. Kuka dai da hawaye na ƙarewa da na Anam amarya sun ƙare, musamman lokacin da walima ke gudana dan manyan malaman addini aka ɗakko suka rugurguza wa'azi akan zamantakewar aure a musulunci da al'adar malam bahaushe. Duk da tasan haƙƙoƙin miji kan matar tasa, dana mata akan mijinta hakan bai hana hankalinta sake tashi ba da sake jinsu a yau a bakunan malamai. Anci an sha kowa ya godema ALLAH. Yanda amarya tai ƙyau hakama ango Shareffuddeen yay matuƙar ƙyau cikin ɗanyar shadda daketa maiƙo ga wani ƙamshi na musamman da kwarjinin da ALLAH ke sama duk wasu ma'aurata a ranar aurensu. Anam dai bata san da zamansa ba sai lokacin da za'ai hoto, bata yarda kuma ta kallesa ba fuskarta na rufe da hular alƙyabba, sai dai kamshinsa ya cika mata hanci matuƙa. Koda aunty Amarya ta buɗe mata fuska ma ƙin kallon sashen da yake tai har aka gama zuba hotuna datai matuƙar gajiya taro ya tashi lafiya gab da magrib. Baƙi sun fara bajewa, yayinda akaima Amarya Anam sabon shirin miƙata gidan angonta. 
 Gaba ɗaya iyayenta zagayeta sukai harda Gwaggo a falo, sabuwar nasiha akai mata mai ratsa jiki, tuni kuka ma ya kama gabansa a idonta, dan zuciyar tata ta bushe ta kasa hawaye sam. Sai dai tana saurarensu daki-daki. Mommy dai babu wanda zaice yaga idonta yau a gidan, amma duk da haka an fita hakkinta an kai mata amarya Anam har sashenta domin yin bankwana da ita a matsayinta na uwa. Sai dai kuma suna shiga ta tashi tai shigewarta ta barsu da danginta da basu da alamar niyyar barin gidan.
  Yanda tai ɗin ya ƙona ran Hajiyar sudan, dan haka batako tsaya tofa wani abuba ta kamo hanun Anam suka fito. Sauran sassan aka zagaya da ita harna Gwaggo data bama kowa mamaki da al'ajab, dan kuwa takarƙarewa tai tanama amarya nasiha. Babu dai wanda yace komai amma ta ciki na ciki.
  Lokacin da akai gurfanar da Amarya Anam gaban Abie da Mamie a matsayin sallama dolene ka tausayama waɗan nan iyaye da tilon ƴarsu. Dan kuwa dai duk dauriya da Mamie keyi daga ita har Abie ɗin sai gasu suna kuka har bakunansu suka gagara furta komai sai addu'a a gajarce, dole dai aka haƙura aka ɓanɓareta jikin Abie da ƙyar aka fiddota ƙofar gida inda motocin abokan ango su Fharhan ke jiransu...........✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button