AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 47-48

??47and48??

Daga asibitin wurin wani babban malami mai bada taimako suka wuce, sun mishi bayanin abnda ke damunta malam yasa almajirinshi ya kawo mishi ruwa a kofi ya tofa mata addu’o’i a ciki sannan ya watsa mata a fuska, tai wani irin zabura ta fara ihu da kyarmar jikin, nan malam yaci gaba da mata ruqiyya!

Duk yanda yaso Ameela tayi magana ko kadan bata fita, bugu (duka) kam ameelah ta shashi duk ta qara fita hayyacinta! Gata fara fatar jikinta tayi jaa sosai da manyan borarai,
Daqyar aka samu kafaffen Aljanin ya fita, nan ta kwanta ta fara nannauyan barci!

Hilal duk da yana namiji sai da ya zubda mata hawaye, ji yake kamar ya maida ciwon jikinshi saboda tsananin tausayin matarshi, momy ma kuka take cike da tausayi, wani duka akayiwa ameelah shi saita rufe ido, saboda ihun da ameelah keyi,
Abbah ne ke qarfafa musu gwiwan basu haquri yana kwantar musu da hnkali! (Su Ameela kam anji jiki, ko wannan ya isheta darasin cin Amanar Aure??)

Tufafin dake jikin ameelah duk sun lalace,

Abbah ne yace ma hilal yaje ya dauko mata kayanta saboda daga nan idan tafarka gida zasu wuce da ita saita qara samun sauqi! Jikinshi a sanyaye ya tafi cikin tunanin halin daya bar Ameelah!

Sai da yaje gidanne ya iske a bude kamar yadda ya barshi, yananan ynda suka barshi, qafarshi yaji ya daki wani abu akasa, ya duqa wayar Ameelah ne ya dago yana dubawa kusan 9 miss calls.

Bai duba ko na waye ba yana shirin ajewa wani kiran ya qara shgowa! “HMM” yaga an rubuta, ya dauka ya kara a kunnenshi yana shirin magana.. Hmm ya rugashi!

Cikin tattausan murya yake magana “haba! Haba!! Haba!!! My Ameelah ni babu abnda zaki cemun, kinsan yanda na shaqu dake bzanso kimin nisa ba koda na qaramin lokaci ne, ya za’ay ki brni tun jiya ba chat ba waya? Yayi shru yana jiran abnda zatace.

Shikau hilal mutuwar tsaye yayi da waya a hannunshi, ko motsi yaa kasayi! HMM yaci gaba “ya zaki shru ki qyaleni masoyiyah? Kinsan irin son da nake miki ko kin daina sonah ne? Nasan hkanma bzai yiwu ba amma kimin magana ko zanji dadi a raina!

Shi kadai yake magana yana qara ma hilal quncin zuciyah! Shi da kanshi ya gaji ya kashe har lokacin hilal yaa kasa cire wayar a kunnenshi yayi tsaye kamar wanda aka dasa!

??kuyi haquri plz da rashin jinmu kwana biyu dabaku yiba, duk muna exam ne???? Masu neman na bayanma su mana uzuri plz??

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button