BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 44

   
          ★A lokacin da Fadwa ke can tana kuka da tunanin kasancewarsu a tsakkiyar lambun fure mafi girman daraja a garesu ba hakan baneba. Anam ta jima zaune akan sofa barci na rinjayarta tsoro na fisgota, sai dai bata da wata mafita ko ƙwarin gwiwa saboda babu ɓarawo mafi iya sata kamarsa. Kujerar 1sitter ce guda biyu, hakan yasa bata samu gamsuwar kwanciyarba duk da ta naɗe dukan jikinta a kanta. Daga inda yake kwance yaka hango yanda take mutsu-mutsu tamkar magen data sha matsa a hanun mafarauta. Guntun murmushi kawai ya saki, akan laɓɓansa ya furta “Azababbiyar yarinya”. Yana lumshe idanunsa dake cike da barci. Kusan mintuna goma ya bata domin barcinta ya ƙara nauyi sannan ya miƙe a hankali ya taka gareta. Cikin dabara ya ɗagata gaba ɗayanta yakai saman gadon ya kwantar yana danne dariya. Shi baima taɓa tunanin tanada nauyin barci hakaba, hijjab ɗin ya zare mata sannan yaja mata bargo shima ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Tsakanin Anam da Fadwa bai san wanene yafi wani daru ba. Itama yaso zuwa sashenta yay mata sai da safe amma tsoron abinda zai tarar ya sakashi haƙura. Bai taɓa tunanin da gaske MAZA najin shakkar matansu a irin wannan lokacin ba, dan duk yanda yake jin kansa da mazantakarsa da ƙin ɗaukar shirme sai nauyi da kunyar Fadwa ke zagaye da jininsa duk da auren nasa yazo a cikin wani kashine da yasha banban dana sauran maza mafi yawa irinsa.
Numfashi ya furzar a hankali da juyowa gaba ɗayansa yana facing ɗinta, kallon fuskarta yake a cikin wani irin yanayi mai sanyi da zungurar zuciya, ya matsar da fuskarsa gab da tata tare da saƙala hanunsa saman jikinta ya rungumota a nasa jikin sosai, kamar wadda aka isarwa da saƙo ta buɗe ido, sai dai rashin ganinsa da ƙyau ya sata jan numfashi ta haɗiye tare da nasa da yake busa mata saman fuska. Jan jikinta tasoyi baya ya ƙara matseta.
“Yay……”
Kalmar ta kasa ƙarasuwa a zahiri tamkar yanda taso furtawa sai a cikin bakinsa, ba ƙaramin bugawa zuciyar Anaam tayi ba, duk da abinda takema tsoro kenan tun farko dama hakan bai hanata jin mamaki da shiga bazata ba. Bata da wani ƙarfin ƙwatar kanta, sai ma ƙoƙarin zare mata duk wani kuzarinta da razani yake ta hanyar cigaba da sarrafata a wani salo mai kashe jiki da ruguza dukkan alwashi na duk ɗiya mace mai lafiya. Tun tana iya cijewa harta fara amsar salon nasa dan takai shekarun da gangar jikinta ke a matuƙar buƙatar fiye da hakan ma. Sosai ya fitar da ita daga hayyacinta tamkar yanda shima nashi hankalin ya barranta da gangar jikinsa da zahirin rayuwarsa……….✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button