BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 55

…………“To na gode da gaisuwa”. Ya faɗa da miƙewa zai bar wajen. Riƙosa Shareff yay ya maida ya zaunar.
    “Wai haushi kaji?”.
  “Mizaisa naji haushi?”.
Murmushi Shareff yayi da cike lips. Sai kuma yace, “Manta kawai”.
   “Ka gwammace ka cigaba da riƙe damuwarka kenan. Look Musty! Idan kasan zaka iya shanyewa miyasa zakazo min nan to?. ALLAH kana bani matuƙar mamaki. A yanda muka riƙeka sam kai ba haka baneba, ban saniba ko baka yarda damu bane har yanzu oho. Well koma dai minene matsalarkace, mudai har gobe da jibi bazamu daina kallonka matsayi mai girmaba insha ALLAH….”
      “Humm Jamal”.
“Miye wani Humm Jamal. Na jima da fahimtarka ai Shareff kai har yanzu matsayin abokai gama gari muke a wajenka. Mune dai kawai ke ɗaukarka da muhimmanci dan bamu san ciwon kammu ba”.
     “Ya ALLAH ni kamun gurguwar fahimta ne kawai. Yanzu dai ajiye wannan harzuƙar taka gefe muyi magana.”
    Harararsa Dr Jamal yayi ya ɗauke kai. Shareff ya sake yin murmushi kawai.
       “Idan ka gama nuƙu-nuƙun to ina jinka”.
   Kafaɗa Shareff ya ɗan ɗage da taɓe baki, “Bafa wani abu bane babba. Akan auren nan ne dai kawai. Jamal na rasa ina zan ajiye zuciyata naji sauƙi. Mommy bori, Fadwa bori, itama kanta Juwairiyya bori. Duk sun kasa fahimtar komai da suke a kaina yake komawa bawai junansu ba. Jamal ALLAH jinina bana tantama a yanzu haka ya hau sama ƙololuwa”.
     Sosai tausayinsa ya bayyana saman fuskar Jamal, ya furzar da iska shima. Tabbas yaso Anaam, har yanzuma sonta baije ko’ina ba a zuciyarsa. Amma hakan baya nufin baza iya yin sadaukarwa ba. Shareff ya fishi dacewa da ita, sannan ya ɗarashi buƙatar zama da ita saboda wasu hujjoji daya riƙe. Yaɗan kallesa yana jinjina kai. “Tabbas matsalace wannan babba. Musamman ma ta Mommy dan na Fadwa da Anaam duk mai sauƙi ne a ƙarƙashin ikonka suke zaka iya ladabtar da su dole kuma su nutsu.”
     “Dama nasun bawai ya cika damuna bane, kawai dai bana son a yanda suken suma. Amma Mommy da Daddy humm, na rasa ina zan kama Jamal. Ko gidan na kasa zuwa gaishesu kwana uku kenan”.
          “Damuwa dole ce kam, domin Daddy Mommy duk sunada iko da muhimmancin bijirewaka kuskurene, babbar matsalar kuma a ra’ayin da suke mabanbanta, inda ace ra’ayinsu ɗaya ne nakane ya bambanta zaka iya sadaukar da naka ka faranta musu ta hanyar bin nasu. To amma yanzu gaskiya al’amarin akwai ruɗani, inba dai ɗaukar Anaam zakai kubar ƙasar nan ba kawai. Nan da wani gajeren lokaci sai ku dawo sannan Mommy ta huce”.
      “Ita kuma Fadwa fa? Sannan aikina fa? Ita kanta service takeyi miye makomarsa?”.
     Nannauyar iska Dr Jamal ya furzar da faɗin, “Ya ALLAH! ALLAH!”.
Shiru kowansu ya kasa cewa komai, tsahon wasu sakkani Dr Jamal ya katse shirun. “To ko Anaam ɗin zaka ɗauke zuwa wani ɓoyayyen guri a garin nan, inaga hakan zaisa Mommy ta ɗan sauka kafin asan mafita. Danni dai banga ta inda maslaha zata samu ba a yanzu tunda buƙatar Mommy kawai shine ka saki Anaam. Sai dai kuma idan sakin nata zakai…..”
      “Baka da hankali”.
Ya faɗa cikin tare numfashin Dr Jamal. Murmushi Dr Jamal yayi da haɗe hannayensa alamar ban haƙuri. “Understand me, nima nasan hakan abune mai wahala da bazaka iyaba, sannan bama zan so hakan ba. Amma kaje dai kayi tunani nima zan ƙara ko zamu sami wata mafitar datasha banban da waɗan nan na yanzu”.
     Kansa ya ɗan jinjina alamar gamsuwa da hakan, a dai-dai nan kiran Gwaggo ya shigo masa. Yay ɗan jimm kafin ya ɗaga wayar yakai kunnensa da sallama. Daga can ta amsa masa tamkar ba ita ba. Gaisheta yayi, nan ɗin ma ta amsa masa murya a sake. “Kana jina ko Mustapha! Ka kwantar da hankalinka nayi magana da ita. Sai dai wannan wasar ɓuyan da kake damu ba shine mafitaba a gareka inhar kana neman albarka. Ya rage naka kai tunani irin wanda ya dace, na barka lafiya”.
     Wayar ya sauke daga kunnensa, ya girgiza kansa da furzar da huci mai faɗi. “Jamal bara naje kawai”. Ya faɗa yana miƙewa da zura wayar a aljihu.
    “Wata matsalar ce kuma?”.
Kansa ya girgiza masa. “Wadda ake cikin ce dai. Gwaggo ce”.
   “Gwaggo kuma?”.
“Uhmm! Kasan dai bazataƙi goyon bayan ɗiyarta ba ai.
   Ya gane Mommy yake nufi dan haka baice komaiba. Har inda ya ajiye motarsa ya rakosa, ya buɗe ya shiga sannan ya bashi hannu sukai musabaha. Sai da ya fice Dr Jamal ya iya sauke ajiyar zuciya, tausayinsa yakeji har tsakkiyar zuciyarsa. Al-Mustapha mutum ne mai kyawun zuciya ga kowa dazai zauna da shi. Bashi da matsala komai nasa a nutse yake kuma a tsare, yanada halin manyan mutane, dan a lokuta da dama idan yay abu saika ɗauka tunanin wani babban mutum ne mai shekaru saba’in….

       Maimakon ya nufi gida sai kawai ya zarce wajen aikin da companynsu keyi. A can ya samu Khaleel. Ya danne dukkan damuwarsa da haɗiyesa yana mai kallon ƙanin nasa jarumi da halinsu ke kamanceceniya tamkar uwa ɗaya ta haifesu. Murmushi yay da miƙama Khaleel ɗin dake gaishesa hannu alamar yafi son suyi musabaha. Hannu Khaleel ya bashi suka gaisa, ya mika masa irin hular dake a kan duk wanda ke’a wajen. Babu musu ya amsa ya saka, daga haka suka fara zagaya ginin da ayanzu ya fara bayyana kansa gamai kallo. Tabbas aka kammala estate ɗin ba ƙaramin ƙyau da ɗaukar hankali zaiyi ba. Duk inda suka gitta ma’aikata gaishesa suke da girmamawa shiko yana amsa musu da kulawa. Inda yaga gyara yay magana, inda ya kamata ya yaba ya yaba musu. Hakan sai ya ɗauke kaso mafi yawa na damuwar da yake a ciki har lokacin sallar azhar yayi suka nufi massallaci. Koda aka idar da salla wani gidan cin abinci suka nufa anan kusa da ƙafa. A lokacinne kiran Fadwa ya shigo wayarsa. Ɗagawa yay yakai kunne sai dai baiyi magana ba.
    Muryarta a raunane cikin kuma ɗari-ɗari tai masa sallama. Amsa mata yay kadaran kadahan, sai duk ta daburce, amma cikin dauriya da in ina tace, “Am sorry dan ALLAH. Wlhy babu ruwana sai da nace karsu je. Ganin bazasuji maganata ba yasa na bisu da tunanin ko kana can.”
      “Is ok”.
Ya faɗa a taƙaice. Ita tasan is not ok a cikin muryarsa. Amma sanin baya son nacin magana saita saki waccan ɗin kamar yanda ya buƙata. “To ga abinci na kammala amma naga baka dawo gida ba har yanzun”.
    “Karki damu gashi zanci a inda nake”.
   Zatai magana ya dakatar da ita da faɗin, “Zanci na dare idan na dawo bye” Ya yanke batare da ya jira amsarta ba. Kiran nata ya ɗan sakama masa jin sassauci, dan garama ita, Anaam ko zai cika duniya da fushi ai bata taɓa nuna masa ta damuba a kwanakin datai gidan nasa duk da yasan sarai tana sane da komai na halin da yake a ciki dangane da aurenta. Yaja siririn tsaki a ƙasan zuciyarsa yana ayyana (Zanyi maganinki vary soon).
      Khaleel da tun shigowarsu yana wajen siya musu abinci ya dawo tare da waiter dake biye da shi. kujera yaja ya zauna. “Am sorry babban Yaya na daɗe”.
     “Don’t worry”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa akan wayarsa. Sai da suka fara cin abincin a nutse Khaleel ya ƙara maida hankalinsa garesa. “Yaya nikam kuna waya da Yaya Maheer?”. Idanu ya ɗago ya zubama Khaleel ɗin, kafin kuma ya girgiza kansa alamar a’a. Khaleel yaja numfashi ya fesar. Ruwa ya ɗauka ya ɗan sha ya ajiye. “Naje gidansa jiya da yamma. Saboda su Abbah suna maganar ya daina zuwa gida gaba ɗaya sannan wayoyinsa duk a rufe. Yaya banji daɗin yanda na samesa ba shida matarsa. Gaba ɗaya Yaya Maheer ya canja tamkar bashi ba. Sam babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninsa da matarsa abin ya tsoratani wlhy”.
      Kasa magana yay ya kuma kasa cigaba da cin abinci har Khaleel yakai aya, sai dai idanunsa gaba ɗaya launinsu ya sake canjawa. “Mike faruwa?”.
     “Yaya komai ma na faruwa, a yanzu haka so take tabar gidan amma mahaifiyarta ta tabbatar mata zata tsine mata inhar ta bari Yaya Maheer ya saketa. Shi kuma yaƙi bata kowacce irin dama wlhy bakaga yanda yake treating nata ba like dai wadda suke rayuwa a…. Mtsoww oh my god babu dai daɗin faɗa kawai. Na fara masa nasiha amma yaƙi saurarena, daga ƙarshe ma a gabana ya mareta wai tana haɗashi da ƴan uwansa, so abin is to much wlhy”.
      Numfashi ya sauke zazzafa ransa duk a jagule. Still dai ya kasa cewa komai kallon Khaleel ɗin kawai yakeyi. A ƙasan zuciyarsa kam yana jin rauni matuƙa. Ya rasa miyyasa Mommy ta kasa fahimtar rayuwa irin ta yanzu ta aure tasha banban data zamanin baya, a da daga maza har mata kowa nada kawaicin iya karɓar aure a duk yanda yazo masa. Amma a yanzu ba haka baneba, auren soyayyar ma yaya aka ƙare balle na tilastawa. Shi kansa dabai jureba za’a samu irin wannan matsalar ne a lokacin data tilastashi auren Fadwa. Amma daya jure yayta gayama ALLAH da tilastama kansa tanada mahimmancin amsar ko minene daga umarninta sai gashi ALLAH ya saka masa son Fadwa ɗin. Sai dai Mommy ta kasa fahimtar shida Maheer za’a iya samun banbancin juriya akan wannan al’amarin. A ganinsa data barshi ya aura wadda yake so da an samu maslaha. Dan gashi abinda takema gudun bai tsallaketa ba tunda ga Anaam dai matsayin matar gudan jinin nata bisa ƙaddarar UBANGIJI da babu wani hannu daya isa gogewata….
     Numfashi ya sauke a hankali saboda taɓasan da Khaleel yayi. Abincin suka cigaba da ci batare da wani ya sake magana ba, sai dai Shareff tsakura kawai yakeyi. Baimaci na kirki ba ya ture gefe. Haka Khaleel ya biya kuɗin suka sake komawa wajen masu aikin. Har yamma yana a wajen, bai tafi ba sai da masu aikin suka tashi. Sai da ya sai kayan fruits ya bama Khaleel ya kai musu can gida shi kuma ya zuba na nasa gidan a mota shima ya wuce. Ana kiraye-kirayen sallar magrib ya shigo, dan haka bai nema kowaba a cikinsu ya wuce sashensa. Ruwa ya fara watsawa jikinsa na ɗumi a gaggauce, ya fito ya saka kaya nanma a gaggauce ya fice massallaci dan har an fara sallama……….✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button