AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 81-82

?81 and 82??

Via OHW????

Afham yana kwance an kammala masa aiki, edonsa a bude yana kallon kafarsa, kamar zaiyi kuka,

Hilal yashigo dakin, ya isa gurinsa ya shaki wuyansa,

A daidai lokacin su umma da hajna da abban ameelah suka karaso cikin dakin, .

Afham sai kaki yake, hilal kuwa ko a jikinsa, matse wuyan yayi sosai, umma tana kuka takarasa gurinsa tana kokarin firgar hannunsa daga yuwan afham amma tagagara fitarwa,

Abban ameelah yayi saurin karasa gurin ya firge hannun hilal da sauri yasaki wuyan afham, edon afham sun fito sosai, abban ameelah yadaka hilal tsawa “meke damun kane hilal, yazakazo kasami marar lafiya kashakar masa wuya”

Hilal yana kuka yadafe kai wani irin bakin ciki yakeji da baa barshi yayi abinda yasoba,
Cikin kuka yadago kansa yace “abba shine fa “
Cike da mamaki abba yace ” shine wah?”

“Shine afham wadda yake soyayyah da ameelah” hilal yafada yana kuka

Afham yana kwance yana matsar wuyansa dake masa ciwo yaji ankira ameelah, da karfi yasaki wuyan yana cewa “eh nine dan Allah ina ameelah nah, wlh danta kawai nazo garin nan, dan Allah kutaimakamun kununamin inda take” yakarasa maganar yana hawayen, zafin son Ameelah yakeji har cikin zuciyarsa,

Gaban abban Ameelah yafadi, sai yanzu ya gazgata maganar hajna ” tabbas ameelah tana soyayya da wasu mazan a chart, wannan wace irin masiface take kokarin kunnu kai acikin wannan zamanin namu” duk a zuci abba yake wannan zance,

Hilal yana gefe sai kuka yake, tambayar zuciyarsa yake wane irin hukunci yakama yayanke akan ameelah,

Umma na hawaye takarasa gurin hilal tarikashi, duk zukatansu sundau zafi,
Afham yacika da mamaki, ganin kowa yana hawaye, duk ya firgita, muryarsa na rawa yace ” dan Allah ina Ameelah, kodai ta mutu ne,

Hajna tayi karfin hali tana kuka tace ” da ace mutuwa tayi da zai fi mata sauke fiye da wannan rayuwar datake ciki”
.
A daidai lokacin hawaye suka gangaro a kan fuskar afham yace “meya faru da ita…”

Cike da hargowa hajna taci gaba da masa magana ” ameelah matar aurece, ameelah akwai hijabin aure akanta, ameelah taci AMANAR AURE, kayi gaggawar zuwa kayi istigifari tun kafin Allah ya sauko da masifarsa akanku”

Tunda hajna tafara magana afham yagaga tsayar da kukansa, kuka yajeyi sosai..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button