BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 56

56

………Bai shigo ba sai da aka idar da sallar isha’i. Ya kwashi ledojin daya bari a mota. Na Fadwa ya fara ɗauka ya nufi sashenta. A falo ya sameta zaune cikin kwalliya da waya a hannu. Ga tv a kunne tana faman aiki. Yana mamakin yanda a koda yaushe waya bata barin hanunta, tun baya maida hankali akan hakan har ya fara sosa ransa, sai dai bazaiyi maganaba a yanzu sai anzo gaɓar data dace.
      Fuskarta ƙawace da murmushi ta taso garesa. Rungumesa tai da manna masa kiss a kuncinsa na dama. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi dan babu abinda yafi buƙata kamar ɗumin matarsa a yanzu. Ya sani ba ƙaramar jarumta yayi ba, dan rabonsa da Fadwa kusan sati uku kenan cikin na huɗu. Hanunta saƙale a wuyansa fuskarsu gab da juna. Bakinsu take son haɗewa amma ya kauda kai kaɗan dan ya tabbata ya biye mata bazai iya ƙyaleta ba kuma hakan ba daidai bane ba tunda akwai haƙƙin wata a kansa bayan ita ɗin.
     Cikin son basar da ita ya janye hanunta dake saƙale a wuyansa yana faɗin, “Ki shirya abincin”. Jiki a sanyaye ta gyaɗa masa kai, harya nufi ƙofa ta kasa haƙuri. “Har yanzu baka huceba ko? Kana ganin laifi na!”.
      Tsayawa yay, sai da takai aya ya waiwayo yana kallonta. Tai ƙasa da kanta zuciyarta na sake raunana dan da gaske abin ya dameta. Shima ɗin ta bashi tausayi, dan shi shaida ne Fadwa nada tsoro da tsananin gudun ɓacin ransa, wannan halin nata na ɗaya daga cikin abinda ya saka masa sonta. “Zan iya miki uziri ana yau, amma ki kiyaye dan anan gaba makamancin haka ta sake faruwa ni kaina ban san irin matakin dazan iya ɗauka ba har asu kansu, dan bazan ɗauka wulaƙanta matata da hanani zaman lafiya ba a gidana”.
      Bai jira cewartaba ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, zuciyarta na rage cinkushewar da tai……

    Idar da sallarta kenan takai bakin gado, muryar Mamie take son ji duk da sun gaisa ɗazun da safe. Maimakon normal kira saita ji sha’awar kiranta video call. Tana ƙoƙarin yin hakan da ɓare lollipop sweet takai baki ya shigo ɗakin. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janye nata dan wani irin matsanancin kunyarsa ta tsinci kanta a ciki saboda abinda ya faru ɗazun da shi ta yini cikin rai. Inda taken ya ƙaraso ya zauna kusa da ita gab. Batare data sake iya ɗagowa ta kallesa ba tace, “Barka da dawowa”.
     “Uhhumm”.
Ya faɗa a miskile idonsa nabin jikinta da kallo. Kaya ƙanana ne da sukai matuƙar kama ɗan jikinta komai ya fita fili tamkar an zana. Ya janye a kasalance dan dama acan ɗin ma kwalliyar Fadwa ba karamin tasiri tai a ransa ba. Ya yarda matan nasa duk ƴan gayu ne, sai dai Fadwa tafi Anaam son ƙyale-ƙyale, dan da wuya kaga fuskar Fadwa babu kwalliya hakan kuma na matuƙar burgesa. Saɓanin Anaam da zai iya cewa bai taɓa ganin kwalliya ba a fuskar tata ba, sai dai idan ya manta. Idan son samune itama zai so ta dingayi ɗin dan yana da tabbacin zata mata ƙyau.
       “Da rana mi kika ci?”.
   Ya jeho mata tamyar idonsa na kallon bakinta dake juya alawar a ciki batare data riƙe tsinken ba. Yanzu ma bata iya ta kallesa ba, ta damƙe wayarta da take juya a hanunta da ƙyau. Muryarta can ƙasa tace, “Noodles”.
    Ɗan jimm yay da tunanin taya ta dafa. “Dami kika dafa to?”.
  Ɗagowa tai ta dubesa da mamaki. “Kamar ya?”.
     “Nasan baki da gas ai”.
  “Nayi amfani da electric ne”.
Ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa, dan gaba ɗaya ya shafa’a ne ma, dama yau yaso a siyo mata gas ɗin a kuma haɗa mata tvn ta.. Duk yanda yaso basar da abinda ke tsikararsa ya kasa. Ƙara matso jikinsa yay a nata sosai da riƙo hannayenta duka numfashinsa na sauka a gefen wuyanta. A take tsigar jikinta ta tashi, taja jikinta baya zata matsa ya rungumota, kallonsa tai fuska a marairaice, sai dai bazata iya jurewa ba tai ƙoƙarin rissinarwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tallafo haɓarta..
    “Yanzu tsabar rowa bazaki sammin sweet ɗin ba?”.
Wutar kan Anaam neman ɗaukewa tai, tsigar jikinta ta tashi har tana ƙoƙarin yadda alawar babu shiri. Gaba ɗaya yanayin nasa da muryar dayay amfani wajen mata maganar ya matuƙar rikitata, dan bata taɓa jin irin muryar tare da shi ba. Hannu takai jiki a mace zata zare alawar a bakinta ya riƙe hanun tare da matsota suna kallon juna cikin ido.
    “A haka nake son sha”.
(Ya ALLAH) ta faɗa cikin zuciyarta, a zahiri kam tuni idanunta sun fara marmarin firgici da tsantsar mamakinsa. Ya kashe mata ido ɗaya da sake kusanta fuskarsu, baya ta ƙara jan jikinta ya bita, ta ƙara matsawa shima ya matsa, ta ƙara ya ƙara, sai kawai ta zube a gadon da ƙokarin tufo alawar waje kawai a ganinta hakan shine mafita gareta.
     Murmushi ya saki a karo na farko, shanyayyun idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya na bin fuskarta da kallo, ya ɗauka alawar ya saka a bakinsa ya ɓalla kaɗan. “Ni ban iya rowa ba zan sammiki” ya faɗa tare da ɗage mata gira ɗaya yana matso da bakinsa gab da nata.
“Ba gashi nan na baka ba”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa.
“A cikin bakinki nake son sha ni”. “Ban yarda ba”.
“Ba sai kin yarda ba dama tunda nawa ne”.
“Naka? Yaushe ya zam….” Ruff ya rufe bakin tare da tura mata sweet ɗin a nata bakin, ya haɗa da harshenta ya fara tsotsa. Wani irin miƙewa illahirin gashin jikinta sukai, takai hanunta saman ƙeyarsa da nufin janye masa kai hakan ya gagara. Domin wani irin salo yake mata mai narkar da ita, dole ta lumshe idanunta a hankali ta fara bashi gudunmawa. Sai da suka shanye alawar tas a cikin bakinta sannan ya janye. Kanta ta kauda gefe wata irin kunyarsa mai girma na ratsata. Sassanyan murmushi ya saki da leƙa fuskartata, tai saurin ɗaukar fillo ta ɗora tana murmushi itama. Ƴar dariya yayi da ƙoƙarin tashi tsaye. “Ga tsoro ga tsiwa, kona dawo mu shanye sauran?”.
        Da ƙyar ta iya fisgar numfashi ta haɗiye, ta bude idanu hannunta dafe da ƙirjinta. Dariyarsa ya danne da ƙyar yana gyara rigarsa da jifanta da wani kallo daya sata janye nata idon akan sa, “Oya tashi muje cin abinci”. Ajiyar zuciyar ta ƙara saki, batare data yarda ta kallesaba ta girgiza masa kanta. “Ni na ƙoshi fa”.
    “Amma kin san zan iya ɗaukarki daga nan har can kuma akwai Matata”.
          Har cikin rai maganarsa ta soketa, to ina ruwanta wayace ba matar tasa bace. Ta murgiɗa baki a zahiri da ɗauke kai gefe tana ƙunƙuni. (Wani yace ba matarka bace balle ka mana burga). Sarai ya jita, amma sai baice komai ba ya ɗan matso kusa da ita. Zabura tai gefe tana tura baki. “To bana tashi ba dai”. Hanya ya nuna mata. Hijjabin sallarta ta zara dayin gaba tana kumbura fuska, ya biyota a baya yana murmushi dan ya gama yanke shawarar ayita ta ƙare kawai ya tabbata haka shi zai kawo masalaha ta ƙarshe da zuciyarsa ke tabbatar masa..

     Sun sami Fadwa harta kammala shirya abinci, a cikinsu babu wadda ta kalli ƴar uwarta, kuma kowacce ta tsuke fuska babu sauƙi. Shi dai ya cigaba da shan alawarsa yana ƙumshe dariya, a zahiri kam shima tashi fuskar a tsuken take. Fadwa dake zuba masa abinci ta ɗago tana kallonsa, da ido yay mata alamar thanks. Ta ɗan saki murmushi, sai dai ta tsurama sweet ɗin bakinsa ido. Fahimtar hakan da yayne ya sashi zarota ya miƙa mata, ƴar kaɗan ta rage a jiki yama kusa shanyewa, hannu ta kawo zata amsa fuskarta da murmushi itama Anaam dake ɗayan gefensa tai kamar zata ɗauka kofi ta tanƙwaɓe hanunsa sweet ɗin ta faɗa cikin miya. Fiskewa tai kamar bataga abinda tai ba, hasalima taƙi kallonsu. Wani irin takaici da baƙin ciki ya turnuƙe zuciyar Fadwa, amma sai batace komaiba.
      Kallonta yay ta gefe ido shikam dai, sai kuma ya maida ga abincinsa guntun murmushi na suɓuce masa. Ganin har sun fara cin abincin bata da alamar zubawa ya sake ɗagowa ya kalleta. “K bazaki ci abincin ba?”.
Fuska ta ɗan yatsina da taɓe baki, “Ni ban iya cinshi ba”. Karon farko Fadwa ta kalleta, itama fuskar ta yamutse baki a taɓe. Cikin gatse da jin bazata iya shiru ba tace,
“Sai ki fara koya ai”.
Itama a gatsen da taɓe baki tace, “Ba buƙatar hakan”.
Baki Fadwa ta sake laɓewa da ɗauke kai abinta. Itama sai ta harareta ta cigaba da buga game ɗinta.
     Duk yana jinsu amma yay shiru bai sake yin magana ba, sai ma hankalinsa daya maida ga abincinsa hankali a kwance kamar bai san sunai ba. Har suka kammala dai Anaam bata ci ba, shine ya fara barin dining ɗin ya koma falo ya zauna. Fadwa dake shan lemo a hankali ta saki murmushi, dan da farko tayi zaton zai kama lallashi Anaam ɗinne kamar yanda ta san itama Anaam ɗin tayi ne dan ya lallasheta. Amma sai gashi yay biris. Mikewa tai tana tattare kayan da sakin ƴar karamar dariya. “To mudai wannan amarya ta gidanmu uhumm babu alamar ta cika amarya, hausawa na cewa amarya kota buzuzu ce ɗokinta ake, sai dai mu gata mutum a namu gidan bata da wani fawa”.
     Da gaske saƙon na Fadwa yana isa har tsakkiyar kan Anaam. Dan kuwa da turanci take maganar hakan yasa komai ta jisa. Zuciyarta ta fara luguden dakan fusata da sukar da kalaman ke mata amma sai ta saki murmushi a zahiri. Babu burin zamanta a wannan gidan hakan yasa bata fatan Shareff ya nema wani abu a gareta, dan hatta kissing ɗinta da yakeyi tayi alƙawarin baza’a sake na huɗu ba. Sai dai tabbas saita shayar da Fadwa mamaki cikin sauƙi batare da ta rasa mutuncin nata da take tattali ba… A yanzu dai batace komai ba har Fadwa na koƙarin barin wajen fuskarta ƙawace da murmushi. cigaba da zama a dining ɗin tai kamar mai latsa waya, a zahiri kam komai ta kasayi tsabar raɗaɗin da ƙirjinta ke mata…..
      “Amarsu mu kuna lafiya”..
Fadwa ta faɗa tana ɗaga mata yatsu biyu da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci gefen fuskar Shareff. Fuskar tata ya shafo shima yana murmushi. Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kauda daga kansu, dama ta gefen ido take kallonsu. Jitai bazata iya barmata ba, dan haka ta miƙe tasha gaban Fadwa dake gab da fita…
Cike da salon ƙularwa fuskarta ƙawace da murmushi take kallon Fadwa da mamakin yanda ta tareta ya sata diriricewa, to amma a gareta hakan zai zama riba tunda tasan Shareff bazai ragawa Anaam ɗin ba.
Anaam data gama fahimtarta ta ƙara sakin murmushi da naɗe hannayenta a ƙirji “Amaryar data kai mace ba’a samunta ta sauƙi ai, saboda tsadarta tafi tsada tsada madam, ki rubuta ki aje a duk lokacin dana sallama wlhy sai kin zama ƴar kallo a wajen mijin naki, idan kin isa mu ƙulla”. Ta ƙare maganar ƙasa-ƙasa tana kashema Fadwa ido.
Yawu mai kauri Fadwa ta haɗiya saboda ganin alwashi cikin idanun Anaam, ta saci kallon gefen Shareff sai taga su yake kallo. Murmushi ta saki cike da kirsa. “Ayya Anaam miya faru da wannan magana haka?, ai shi ɗin mijinmu ne mu duka ba nawa kawaiba, kinga kuwa basai mun ƙulla wata yarjejeniya a kansa ba, kuma indai nice wlhy nama ƙara muku sati biyu akan ɗayan”.
Anaam dako kallon inda Shareff yake batayi ta saki wata siririyar dariya data ƙona ran Fadwa da tafa hannayenta. “Woow! kai kai kai Uwargida abun birgewa. Muna godiya da wannan ƙyauta mai tsada”. Sai kuma ta kashe mata ido da maida muryarta can ƙasa kamar mai raɗa. “Karki damu kinada kaso, za’a samo miki tukuycin baby da zaina tayaki hira tunda kin hana masa zuwan abokin wasansa yayansa duniya”.
Duk da a hankali sosai Anaam ta faɗi furucin ƙarshe kaɗan ya rage zuciyar Fadwa ta wantsalo waje. “Sautin bai miki ba na ƙara n…..” Da sauri Fadwa ta fice cikin sassarfa daga falon, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin jikinta har tana kifawa kamar zata faɗi. Anaam ta danne dariyarta da ƙyar, da binta da kallo harta fice. Sai da Fadwan ta fita da kusan mintuna biyu sannan tabi bayanta zuciyarta fes tunda ta rama.
Da kallo ya bita ta gefen ido, ya jinjina kansa da sakin murmushi dan duk abinda ya faru a tsakaninsu yaji. Hatta maganar farko da Fadwa tai a dining, yayi shirune dama dan yaga wane mataki ita kuma Anaam ɗin zata ɗauka. Wato Fadwa a gabansa ne take nuna ita ɗin mutuniyar kirkice, ita kuma Anaam bata iya ɓoye-ɓoye ba sai take nuna nata babu wani munafurci a ciki. idan ya auna da kallonsa da Fadwa takeyi tana magana cikin canja yanayi danta kunnasa ne ya hau kan Anaam kenan kamar yanda taga yanayi a kwana biyun nan idan tai makirci. Lallai mata sai ka barsu, idan kai wasa sai su kaika wuta da sheɗana, dolene ya nutsu wajen ƙara fahimtar halayen kowacce kuwa.
Duk yanda yaso cigaba dayin kallon kasa hakan yay, dan kalaman Anaam babu abinda suke sai tsikarar zuciyarsa, dole ya miƙe ya kashe komai ya shiga bedroom ɗinsa. Sabon shirin barci ya sabunta da mulke jikinsa da turarurrukansa masu ƙamshi har kusan kala biyar, haka kawai yake jin saka ɗaya bai gamsar da shi ba. Bakinsa kansa yasha Mouth fresheners kusan kala uku, ya sake duban kansa a mirror ya saki murmushi da kashema kansa ido ɗaya… “Dole ne yau a tabbatar min da wannan tsadar da tafi tsadar tsada my girl”.
     
       ★Ransa fes ya fito hanunsa ɗauke da fresh milk. Kansa tsaye sashen Anaam ɗin ya nufa, baiyi mamakin rashin ganinta a falo ba. Sai da ya fara shiga kitchen ya ɗauka ruwa da glass cup sannan ya nufi bedroom ɗinta bayan ya kashe komai ya rufe ko ina.
     Tunda ta fito a sashensa da murmushi ta iso nata sashen, ya kuma gagara barin fuskarta har tai shirin barci dan dama tayi wankanta, brush kawai tayi ta haye gado batare data ɗaura jacket ɗin rigar barcin ba a kan ta cikin data kasance ƴar fingila iyakar cinyoyinta, sannan hanunta siriri ne. Rufda ciki ta kwanta da jan bargo ta lulluɓe har kanta tana cigaba da sakin murmushi………✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button