NOVELSRANA DAYA

RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 14

        CHAPTER 14

BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????

ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925

Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana

Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki

kare mutuncin auranki.” Salma ta ce, “Na gode

• Yaya, Yaushe zan fara zuwa?”

Ya ce,

“Ina son nan da ranar Monday (Litinin)nake son ki soma zuwa insha Allah.” Salma tayi ta godiya!

Ranar ko baccin kirki bata yi ba, ta tashi

tana ta kwatanta irin tafiyar da zata yi in zata Makaranta. Haka kuwa washegari sai gashi da form, da jaka, da takardu, da uniform kala biyu. Tamkar

  • sallah Salma taji, ya ce

“Saura safa da takalmi.

” TaCe Yaya duk kasuwa kaje ka siyo?”

Ya ce

“A’a Makarantar suke badawa. Takalmi da safa ne suka fadì kalar da za a siya.”

Sun je Makarantar an yi mata tambayoyi, in da suka gano tasan abubuwa sai dai bata jin Turanci.

Da za su sa ta SS1 sai suka ce sai dai ta maimaita JS2.

Salma, ba ta damu ba, ita ko JS1 ne bata da matsala. Ranar Litinin kuwa randa Salma zata fara

zuwa Makaranta dama kwana tayi bata runtsa ba,gani take kafin gari ya waye za a tashi duniya.

Tun kiran farko ta farka ranar ba dakinta yake ba, tayi wanka ta zauna jiran ayi kiran shiga

*Masallaci, Ranar ko karin kumallo kasa yi tayi

Riga da siket ne, siket din mai fadi kadan ya Wuce gwiwa.

Amma suna saka wando baki irin damammen nan, sannan safarsu tana zuwa Kwauri daidai in da wandon ya tsaya, sai riga fara da farin karamin hijabi, siket din kuma ruwan hoda.

Hakan yasa kayan suka yi mata matukar kyau.

Ta taje gashinta ta kama shi. Ta kalli madubi, sai

ta tuna wata Sajida a kusa da gidansu can Zariya,

suma haka suke saka kayan Makaranta, ita da

kannenta su hau keke kowa da nashi.

Ita dai suna bata sha’awa tun da, amma Sajidar

sai take musu dariya in taga sun fito suma za su

tafi, sai take ce musu Almajiran Gwamnati.

Tayi juyi a fili ta ce, “Sajida dama za ki ganni

yau, nima Salma na hau layin dalibai masu neman ilimi

Ta dibi biskit ta zuba a Jakar ta zauna jiran

Yayanta ya shigo. Murmushi ya saki lokacin da

suka hada ido, tayi matukar birge shi a cikin kayan Makarantar.

Yana tsaye bakin Rofar ya zuba hannayenshi

biyu cikin aljihu. Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa

tare da fadin “‘Muje ko baby.

» Ya fadì haka ne don tayi masa kama da baby

Ta rataya jakarta a gadon baya, ta dauki

makullin dakin. Ya miko mata kudin namanta.

sannan ya bata wata dari biyar din yace Ki hau

Mashin in an tashi, canjin kuma kiyi amfani da shi.

Ta ce,

“Yaya na dauki biskit ba sai nayi amfani da kudi ba.” Yace, “Ki bar shi.” Suka fito, ta mika mishi makullin,

“Kulle min Yaya.

” Ya amsa yana

Nuna mata yanda zata yi, domin ba kullum ne yake nan ba.Ta dube shi

“Bari na yi ma Anty Aliya sallama.

” Ya ce

“Yi sauri min ti daya da rabi.

Dan gudu ta kwasa, tare da tsalle ya girgiza kai

*Yarinyar nan da shirme bare taji ta a cikin

uniform me saka dalibi Kiriniya.

Ta samu Aliya tsaye a kusa da window tana

leke. Salma ta rusna ta gaida Aliya, sannan ta ce

sai ta dawo. Bata jira amsawarta ba ta juya don kar

ta shiga lokacin da Shatima ya bata.

Da dan tsallanta ta koma gurinshi.

Ya tada mota zata hau baya, ya ce “Kina son ki nuna ma

“Yan Makarantarku ni Direbanki ne ko?”

Tayi dariya tare da komawa gaba. Da suka zo fita, ta mika ma Maigadi kudin nama. Ta ce, *Yau na dari biyar ni ke so

Ya ce

“To.”

Shatima ya kalleta

“Za’a soma adana kudin ne?” Ta ce Ai na dari uku ni ke siya duk kwanakin nan, yau da kana dakina ne zan kara.

Ya cE

“Au! Yau ina dakin baby ne ko?”

Tayi dariya,

“Kullum kana dakina Yaya sai ka manta,

” Ya CE

“Lokaci zai zo da zan tuna.

” Ta ce,

“Allah ya kai mu.”

Ofishin Shugaban Makarantar •suka je, daga

nan aka nuna ma Salma aji. Ta daga mishi hannu

tare da fadin Bye-bye Yaya.

” Cikin murmushi yace

“Bye baby.

A cikin ajin an nuna ta a matsayin sabuwar

daliba, aka nemi da ta fadì sunanta. Ta mike ta ce,

“Sunana Ummu Salma A. Bashir.

Suka yi mata

sannu da zuwa. Malamin ya nuna mata wata yarinya.

“Ga waccan itama sunanta Ummu Salma, kije

kusa da ita na hada ku kawance.Cikin sakin

fuska ta kalli Salma,

“Zo mu zauna.” Cikin turanci

tayi mata maganar.

Salma ta kan ji amma bata iya maidawa ba.

Umma Salma Sadi Dankasa ita ce Kawar da aka

yi wa Salma, tana da kokari ga salo da iya yi,

rawar kai kuwa ba a magana.

Suna shiga falo Amna ta ce, “Ko’ina ya yi kura

me aikin ta soma aikin shara.

Ya ce mata “Bari ya

duba Nafisa itama cikin ne.

Amna ta tabe baki

bata ce komai ba.

Ya samu Nafisa kwance bata jima da dawowa

dega amai ba. ya ce,

“Aman nan yayi yawa, ko dai

asibiti zamu je?” Ta ce,

“Ba za ta iya tashi ba.

” Ya dauki wayarshi, ya kira layin Likita ya fada mishi

halin da Nafisa take ciki.

Ya ce,

“Ya zo asibitinshi da mota ya dauki

Nurse ta saka mata ruwa, shine kawai abin da za’a

iya yi mata.

Ya CE

“To.”

Haka ya dauki mota

yaje ya kawo Nurse ta zo da komai ta hada ma Nafisa ruwa.

Aliya da ke leke ta window ta ji haushin hakan,

dama tana cike da takaicin yanda yake ririta

Nafisar, ga Amna ma ta dawo. Ta dauki wayarta ta
tura mishi sakon korafi.

‘Haba my love, ban zaci za ka yi min haka ba,

gani a gida sai ka dauko Nurse daga waje?

Gaskiya ban ji dadin haka ba.

Sakon na shigowa ya duba, guntun murmushi

yayi bai damu ba yasan Aliya tana da fahimta, da

ya yi mata bayani zata, fahimce shi.

Sai da Nafisa ta samu bacci sannan ya kira

Mama a waya yace Don Allah Hamida ko Momi

wani ya zo saboda dare, yanzun haka ruwa ake yiwa Nafisa kari.
Mama tace

“Jikin ne har yanzun?” Ya ce,

“Ciki ne da ita, sai wuya take sha, amai yayi yawa.

Mama cikin murna ta ce,

“Allah Ya bata

lafiya. Hamida sai ta zo tunda itace ba ta zuwa

Makaranta sun gama jarabawar fita.Yayi godiya

suka yi sallama. Ya tafi dakin Aliya don fahimtar da ita.

Tam! Ya same tacikin fushi, ya ce

“Haba

Aliya, keda ni ke gain kin fi su hankali, kuma za

ki fisu bani hadin kai?”

Tace

“Ai ni gani nayi ilimina bai yi min

amfani ba, in ba zan taimaki mijina da kuma

abokan zamana ba.

Ya kama hannunta

“Na

fahimce ki my love, amma kin san halinku na

mata, nasan ba za ta yarda ki sa mata ba ne.

Aliya ta ce, “To yanzun haka zaka sa mana ido

muna matanka babu taimako a tsakaninmu, babu

jituwa, ba za mu iya cin abinci kwano daya ba,

gaisuwa ma ta gagara tsakaninmu, ko dan su suna

jin su ‘ya’ yan wasu ne? Amma ni da Salma ai muna gaisawa, duk da

sakarcin kuruciya irin na Salma ta fi min su tunda

za’a gaisa. Ka iya tunawa fa ko makocinka ne

Musulunci ya gindaya sharadin makotaka

tsakaninku, bare matanka.

Wannan fa aiki ne babba a kanka, domin

kiwonmu Allah Ya baka, gashi za’a soma haihuwa

a gidan tun yanzun gara kayi digin hada kan yaranka.

Ya janyo ta zuwa jikinshi,

“Ina sonki sosai

gurin sa ni a hanya, ki taimaka min gurin hadin kan iyalina, ke ce ki ka fahimce ni.

” Aliya ta dan ji dadi, yanda ya nuna mata.

Salma kam bata da wata matsala, babu kowa da komai a gabanta sai karatunta, matsalarta daya in
an bata assignment bata samun me taimaka mata
in ta z0 gida, sai in ta koma Makaranta Salma

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button