BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 62

Chapter 62

………A waje suka sami aunty Mimi tare da Dr Bilkisu. Khaleel ne yazo ɗaukarta ita gida zata wuce. Anaam ta shiga zazzame jikinta a nasa amma yaƙi sakinta har sai da ya sakata a mota. Ya ranƙwafo zai sumbaceta ta kauce tana faɗin “Kai yaya wai bakajin kunyar aunty mimi”. 

   Kai ya kaɗa mata da lumshe idanunsa “Ƴar kaɗan”.

 “Kake jin kunyar tata?”. Ta tambaya cikin sigar waro masa idanu. 

“Eh mana ba mamata bace. Ba buƙartar na ɓoye mata muhimmancin autar mata ai”.

    Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta tana murmushi. “Ni dai babu ruwana”

  Murmushi yay da sumbatar kunenta. Ƙarasowar Aunty Mimi wajen ya sakashi ɗagowa. Sai lokacin takejin batare da Aunty mimi zasu tafi ba. Fuska ta kwabe da rokonsa zatabi aunty mimi ama yaki. Sai kawai ta kama hawaye.

   ★Shiru babu mai magana a motar har suka iso gida. Har mai rake ta gani tana so amma ta gwammace tai haƙuri da tace ya tsaya ya siya mata. Itace ta fara fita a motar tun kafinma ya kashe, daga shi har Aysha suka bita da kallo. A ransa ya ayyana (Ni nasan maganinki yarinya).

  Aysha ce ta kwashi kayansu, a dai-dai lokacin Fadwa ta fito daga sashenta dama tana laɓe duk tana kallonsu tun shigowar motar gidan. Tayi ƙyau cikin kwalliya sai baza ƙamshi ake. Tai masa sannu da zuwa Aysha ta gaisheta. Itace ta taya Ayshan kwashe kayan zuwa sashen Anaam ɗin. Sun sameta kwance cikin kujera ido a rufe kamar mai barci, kuka take son tayi akan hanata bin aunty mimi amma yaƙi ya fito, shine tai luff a wajen zuciyarta na suya. Sallamarsu baisa ta buɗe idanun nata ba, har sai da Fadwa tace mata ya jiki. Ciki-ciki ta amsa mata, Fadwan ta nuna kamar bata damuba ta sake mata addu’a sannan ta fice.

   Aysha datai tagumi ta girgiza kai kawai. Tashi tai ta fara gyaran sashen duk da bawani datti bane ba. Harta kammala da falo ta koma bedrooms Anaam na’a wajen kwance, Shareff kuma bai shigo ba. Ayshar ce bayan kammala aikin nata ta fito tace mata ta tashi taje tai wanka ga ruwa can ta haɗa mata. Batare data tanka mata ba ta miƙe. “Ki fara shiga ruwan zafin kamar yanda doctor tace.”

  Kanta kawai ta jinjina mata tai shigewarta. Aysha ta bita da kallo cikin tausayi, dan ita tausayi take bata, saboda ta fahimci abinda Anaam ɗin ke gudu danta jigata a matuƙa a hanun Yaya Shareff ɗin.

  Shigowarsa ce ta katse mata tunani, yabi falon da take bazama turare da kallo, sai dai baice komai ba yakai zaune.

   Burner ɗin Aysha ta ajiye da nufar kitchen, babu jimawa ta dawo ɗauke da ruwan. Zata zuba a kofi ya karɓa goran ruwan, murfin kawai ya buɗe ya kafa kai. Bai ajiye ba sai da ya shanyesa tas, da alama ƙishin yakeji dama. Sai lokacin yace, “Tana ina?”.

  “Tana ciki yin wanka”.

Ƙofar ya kalla na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya miƙe. “Ki shirya zuwa anjima saina maidaki gida”.

  Da to ta amsa masa. Shi kuma ya shige corridor ɗin bedrooms ɗin Anaam. Tana faman ƙunƙunin ruwan da Aysha ta zuba mata na sit bath yayi zafi da yawa ya shigo, cikin sauri ta juyo kuma a rikice dan babu komai a jikinta. Daburcewa tai gaba ɗaya tama rasa ina zata saka hannu ta rufe, yi yay tamkar bai ganta ba, ya ƙaraso cikin toilet ɗin. Ruwan da take sirkawa ya sakama hannu, ya ɗago yana kallonta. Juyar da kanta tai gefe da ƙara tsuke fuska. 

   “Humm” 

Kawai yace ya fara ƙara ruwan zafin. 

 “Yayi zafi fa da yawa”.

Ta faɗa da sauri kamar zatai kuka. Dai-dai nan ya ɗago dan ya masa yanda yake buƙata, da sauri ta yunƙura zata fice ya damƙota, ƙoƙarin ture hanunsa ta shigayi tana wani ciccijewa ita a dole bata wasa bace. A karon farko ya saki murmushi, hannun nata ya saki ya damƙe towel ɗin, ta ɗago a matuƙar firgice tana kallonsa. Ido ɗaya ya kashe mata da cije gefen lips ɗinsa shima, dole ta kauda kanta dan salon nasa saida tsigar jikinsa ta tashi. Matsota yay tare da ranƙwafowa bakinsa saitin kunnenta. 

   “Bakin ya mutu ne ƴammata?”.

Fuskarta ta sake kaudawa gefe da son ƙwace hanunta. Sai kawai jitai ya since towel ɗin nata. Ruɗewa tai, tai ƙasa zata duƙe ya ɗagata cak ya dire a ruwan zafin. Azabar data ratsata ta zafin ruwan ta sakata sakin ƙaramar ƙara mai kama da kukan shagwaɓa. Matso da fuskarsa yay gab da tata, saukar numfashinsa akan tata fuskar ya sata ɗan buɗe idanunta dake rufe, dai-dai lips ɗinsa na sauka kan nata, sai kawai jikinta ya hau rawa. Ya cigaba da binta a wani salo daya saka jikinta saki lokaci guda, sai dai bai samu haɗin kanta ba kamar yanda yake buƙata. Bai damu ba ya cigaba da sarrafata a hakan tunda dai saƙonsa na isa kamar yanda yake buƙata. Nisan tafiyar ya sakata tuna azabar da tasha a daren shekaranjiya, ga gargaɗin doctor na ta kiyaye har sai ciwonta ya warke. Kota warke ɗin ba buƙata take ba balle yanzun. Laushin da gaɓɓansa sukai ne ya bata damar janye jikinta, ta miƙe zumbur jikinta na ɓari. Bashi da zaɓin daya wuce shima miƙewar, ta nane da bango tana girgiza masa kai ganin ya ɗago idanunsa da sukai matuƙar canja launi yana zuba mata.

   Hannayensa duk biyu ya dafe da bangon tana a tsakkiyarsa. Ƙasa tai da idanun nata da sauri tana ƙara damƙe towel ɗin data fisga tun miƙewarta ta suturta jikinta. Ƙasa ya farayi da hanun damarsa a hankali har zuwa kan makunnar shower, sai saukar ruwa kawai taji a kansu a bazata harta ɗan tsorata babu shiri ta ɗago, bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba, dan wani irin al’amari daya girmi ƙwanyarta take hangowa a cikinsu da har suke neman sare ƙarfin gwiwarta, faɗawa tai jikinsa kawai ko hakan zai bata nutsuwa. Haka yake buƙata dama, ya saki ɗan murmushi da naɗe hanunsa duk biyu a bayanta ya rungumeta ruwan na cigaba da sauka a kansu. Kusan a tare suka saki nannauyan numfashi, cikin dabara ya janye towel ɗin da taketa faman riƙo yay ƙasa da shi, tsam ta matsesa dan bata buƙatar ya ganar mata jiki. Murmushi mai ƙayatarwa ya sake saki da ƙara matsetan shima yana saki wasu zafafan ajiyar zuciya a jere….

    Gaba ɗaya ya ƙulleta da kunya, tai wuff ta fara fitowa daga toilet ɗin da alama bakin tsuwar dai ya mutu, sai dai ko gaban mirror bata kai ba shima ya fito. Tana ƙoƙarin ɗaukar hijjab dan tasa ya riƙesa, saman gado ya wurgasa tareda ɗaura mata towel ɗin hanunsa saman kai ya fara tsane mata jiƙaƙƙiyar sumarta. 

   “Har yanzu fushin ne dai baki huceba?”.

  Tayi kamar bata jisa ba, sai dai taɗan saci kallonsa ta gefen ido fuskarta a kwaɓe. 

  Ya ɗan ɗalle mata lips. “Nifa bana son shariya”.

Bakin ta dafe da janye hanunsa da towel dake saman kanta zata bar wajen. “Ni karka sake kulani, kuma matarka ta daina shigomin sashe ban son gulma. Kuje can ku ƙarata kuma cinye kanku tsabar son kai”.

   Dariya sosai taso kufce masa, amma yay ƙoƙarin dakewa sai dai murmushinsa ya ɗan bayyana. Shima ƙarasawa yay gaban mirror ɗin inda takai zaune saman stool tana ƙoƙarin zuba mai a hanunta. Ta bayanta ya ranƙwafa tare da ɗaura kansa a wuyanta ya dafe duk hannayensa akan katakon mirror ɗin. 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button