BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL


DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA…!

STORY,WRITTEN & EDITED
BY
SIS NERJA’AT.

 _COMPILATION BY._

*HAWWA M.U (REAL $MASHER).

????????????????

 _*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA*_

           ????????????????


  _(TRUE LIFE STORY)_

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA AND SAINAH {UMMUN MEENAL}

Kuyi hak’uri na canza sunan daga BA LAIFINA BANE zuwa DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[Onward together]
{ We give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
   *BASED ON 2RUE LIFE*

Page 1⃣➖2⃣

Kwance take saman makeken gadon da yake cikin d’akin ta lullu6e jikinta da blanket idanuwanta a lumshe suke ammah ba bacci take ba,
Saman side bed d’in giya ce da sauran kayan maye a aje.

Ahankali ta6ud’e idonta tare da jawo wayarta da take gefenta ta duba zaro manyan idanuwanta tayi ganin har k’arfe ukku ta yi.

Masha Allah nace ganin natural beauty, fara ce ammah ba chan ba tana da doguwar fuska ga tsawon gashin kai, idanuwanta manya ne sosai tana da dogon hanci siriri sai d’an k’aramin bakinta.

Janye blanket d’in da ta lullu6e da shi tayi tare da safkowa daga saman gadon doguwa ce ammah ba chan ba, tana da ‘yar k’iba daidai jikinta.

Material ne red nd black colour a jikinta duk ya matseta duk motsin da xatayi sai jikinta ya amsa.

Dasauri tajawo veil d’inta tayafa.

Daidai lokacin aka bud’e toilet d’in da ke cikin d’akin wata macece mai k’iba tafito jawur da ita mai kyau sai dai ‘yar gajera ce jikinta sanye da towel daidai gwiwarta tana rik’e da wani k’arami tana goge fuskarta da alama daga wanka tafito.

Kallonta takai wajenta tana murmushi tace” sapna sai ina kuma,

Cigaba tayi da d’aukar abinda take buk’ata tana zubawa cikin handbag d’inta ba tare da ta juyo ta kalleta ba tace mummy lubna gida zanje ne,

6ata fuska tayi tace haba sapna tun yanzu, ” ba fa nan kika kwana ba duka fa wajen 11am kikazo.

Sowie mummy wlh na ce ma ummanah ba zan dad’e ba idan ban koma ba ai ba zataji dad’iba tunda bance mata zan kwana ba.
Fridge d’in da yake cikin d’akin tabud’e daga lemuna sai kwalaben kayan shaye-shaye a ciki kwalbar giya tad’auko taxura cikin jakkarta sannan tajuyo ta sakar ma matar murmushi har dimple d’inta yalotsa sannan tace bari inwuce mummy.

“”Ohk sapna sai munyi waya.””

Fitowa tayi daga d’akin a parlour ta iske Teema da wani mutum tayi d’ai-d’aya a jikinsa shi kuma yana ta shan sholisha daga gani ka san ba ya cikin hankalinsa.

Ba tare da ta kallesu ba tazo zata wuce Teema ce tad’ago kanta takalleta tace a’ah baby sapna ‘yar wajen lubna har kin fito kenan sai kuma ina.

Ko inda suke bata kallaba tace, ” gida zanje,
Ta6’e baki teema tayi tace kedai wlh kina da matsala sai ana hutawa sai kikawo wani zancen gida.

Ba tare da sapna ta bata amsaba tafice daga d’akin.

Tafiya take har ta kusan kai bakin gate d’in gidan tacikaro da sumy tana shigowa tangyad’i kawai take domin a buge take.

Ta6e baki sapna tayi tara6’a ta gefenta za ta wuce rik’o hannunta sumy tayi tace baby sapna sai ina?

Kallonta tayi a wulak’ance tace Aunty sumy zanje indawo ne.
Haba sapna duk kiran da nayi miki jiya ammah baki zoba ko laifi nayi maki.

K’ara tsuke fuskarta tayi tace bakimin komai ba kawai ban samu time bane.
Kwace hannunta tayi daga rik’on da tayi mata tace” am Aunty sumy ina saurine ana jirana munyi magana later.

Bata jira amsartaba ta bud’e gate d’in gidan tafice.

Mai adaidaita sahu tasamu tace yakaita Kurna tayi mashi kwatancen daidai inda zai aje ta.
Tunda suka kama hanya tunani kawai take irin rayuwar da take miyasa naza6a ma kaina irin wannan rayuwar kuma na kasa dainata,
Ta yi nisa cikin tunaninta tajiyo mai adaidaita yana cewa hajiya mun fa iso wace hanya za mubi,
Firgigit tayi daga tunanin da take tace yauwa da ka shiga hannun haggu ka aje ni.

Daidai wani madai-daicin gida tasafka tanufi cikin gidan.

Gidane mai d’auke da d’akuna biyu sai kitchen da toilet a tsakar gidan.

Dasallama tashiga gidan daga cikin d’aki aka amsa mata.

‘Dakin tanufa d’akine d’an madaidaici parlour da bedroom ne.
Da sallama tashiga wata matace da shekarunta za sukai 42 take zaune saman darduma da alama sallah tagama ganin kamannin su da sapna kawai zaisa kagane mahaifiyata ce.

Murmushi tayi tare da amsa mata sallamar.

Sannu ummanah ya gidan.
Yauwa sapna lafiya lou har kin dawo?
Eh ummah.

Tun d’azu nasa ran dawowarki ammah sai ynz kika dawo.

Am so sowie ummah wlh wani d’an abune yatsaidani wash na gaji ummah bari inje ind’an watsa ruwa.

Toh shikenan inkin gama ga abincinki chan kitchen abinda kikeso ne aka dafa.

Yauwa ummah na ji dad’i wlh.

‘Dayan d’akin tanufa wanda daga gani mallakinta ne key taciro daga cikin handbag d’inta tabud’e d’akin ba laifi yana da girma gadone da wardrobe sai dressing mirror da kujera 3 setter sai kayan kallo a cikinsa komai na d’akin ash and black colour ne sai toilet daga gefen hagu.

Kayanta tacire tafad’a toilet tawatsa ruwa sannan tafito wardrob d’inta tanufa tad’auko English wears tasanya riga da wando, simple makeup tayi sannan tafito tanufi kitchen murmushi tayi ganin dambu ne ummah tayi d’auko abincinta tayi tanufi d’akin ummah tana ci suna hira har tagama sannan taje tamaida plate d’in.

‘Dakinta takoma tasanya key, bedside tabud’e tad’auko wasu k’wayoyi tasha kanta yafara juyawa dakyar tatashi tahau saman gado takwanta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita….

Chan cikin barcinta taji ana buga mata d’aki firgigit tayi tafarka tace na’am ummah.

Ke kitashi hakanan magrib ta gabato Ke da bakida aiki sai bacci.

Toh ummah na tashi.

Wucewa ummah tayi tana ta fad’a.

Ahankali tasafko daga saman bed d’inta tanufi toilet, alwallah tayi tazo tagabatar da sallah ko da tagama bata tashi daga saman abun sallarba alkur’ani tad’auko takaranta har aka kira isha’i tatashi tayi.

‘Dakin ummah tanufa lokacin tana cikin addu’a zama tayi gefenta har saida tagama addu’ar suka shafa tare sannan ummah tajuyo takalleta tana murmushi tace sapna ya dae?

Itama murmushin tayi tace bakomai ummah hira nazo muyi,

Toh shikenan fara d’auko mana abinci muci sai muyi hirar.
Toh tace tare da mik’ewa tanufi kitchen.

Bayan sun gama cin abinci suka cigaba da hira sai wajen 9:00pm ummah tace sapna tashi kije kikulle gida kiwuce kikwanta nima bacci nakeji

Toh ummah sai dasafe.

‘Dakinta takoma tayi wanka sannan tahau gado takwanta wayarta tacire daga charge taduba, 5 missed takani tana dubawa taga mummy lubna ce tsoki taja ta aje wayar gefenta.

Addu’ar bacci tayi takwanta batayi minti biyar ba wani kiran yak’ara shigowa.

Kamar ba zata d’auka ba saida takusa tsinkewa sannan tad’aga tayi sallama.

Daga chan 6angaren aka amsa mata tare da cewa daughter halan kinyi bacci natasheki?

A’a mummy lubna bana kusa ne lokacin da kika kirani.
Murmushi tayi tace har hankalina ya tashi na d’auka kinyi bacci bamuyi wayaba.

A gadarance tace no idona biyu mummy

Ohk, kihau chart muyi hira,
A’a mummy lubna wlh yau ban jin yin charting sbd a gajiye nake bacci nakeji.

Toh shikenan,
Yauwa daughter please gobe kishigo da wuri za muje kirakani wata anguwa.

Shagwa6e fuska tayi ba dan ta so ba tace Allah yakaimu mummy.

Nan mummy lubna tafara jan ta da hira ganin ta k’i biyeta yasa tace daughter ko dai bacci?

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button