INAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 51-55

51*
Arewabooks@Mamuhgee
Qin wucewa tayi bedroom dinta tabi bayan Abbi Wanda baisan tana bayansa ba Saida yashiga palonsa taji mutum a bayansa Yana juyowa suka hade Saura kadan ta Fadi ya tarota ta dawo jininsa.

Shiru tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa dayake kokarin hanawa karban kowane yanayi.

Cikin nutsuwa ya zareta Yana cewa”

Meyake damunki ne kwanakin Nan Inayah?

Murmushi tasake tana kamo hannunsa bayan ya zauna itama ta zauna gefensa tareda shige Masa sosai tana cewa”

Abbi Ni bansaniba ko nayi lefi yanzu ka daina ji Dani kaman da,.

Ko Dan Haj umma Bata Sona ne?….

Wani kallo ya juyo yayi Mata da idanuwansa dasuka Dan sauya cikin Dan fada yace”

Karki Kuma cewa haka,
Ki Dena hada matsayinki Dana ummana kowa matsayinsa daban…karna sake Jin hakan a bakinki.

Ahankali tace”

Sorry Abbi na dena
Amma Abbi ai zaka barni a matsayin matarka ko?????…..

Rintse idanuwansa yayi da wani irin yanayi na mamaki da fara kosawa da zancen
Yaushe Inayah ta Zama haka akan aurene Bai saniba?
Bude idanuwan yayi tareda juyowa ya zuba Mata su gabaki daya Yana kallon bakinta da yayi maganar zuwa kirjinta dake harbawa da sama sbd fargabar zancenta Mara control daya sake fitowa bakinta ba Shiri.

Farare idanuwanta dake kallonsa cikeda kauna Mai girma ya maida NASA idanuwan Yana kalla….

Hannunsa dake cikin nata takuma kamawa tana kallonsa a sanyaye.

Kasa cewa komai yayi Yana kokawa da tunanika dake yawo akansa Yana kokarin kwantarda kansa.

Ahankali ta furta sunansa cikin wata kasalalliyar murya wadda ta sanya tsigar jikinsa tashi sbd numfashi Mai dumi data furzo a fuskarsa bayan Kiran sunan nasa.

Ganin har lokacin baice komaiba sai idanuwansa Daya dauke ahankali daga kanta Yana maidawa kan tv Dake kunne.

Ahankali cikin seta murya yace”

Haryanzu maganar aure Bata fita bakinkiba Inayah.

Yanda yayi magana da wata shaqaqqiyar murya yasa jikinta mutuwa itama ta kwantar da kanta a kan hannunsa tana cewa”

Abbi Ni naka auren kawai nakeso yanzu ai.

Sake danne numfashinsa yayi Yana basarwa.

Sosai tayita yimasa fira wadda duka yawanci shagwabane ta ringa zuba Masa wadda tagama take neman lalata kamewarsa da wuce tunaninsa akan yanda Inayah din take abubuwan dabaisan a Ina tasaniba.

Tana tafiya dakinta ya miqe ya nufi toilet din bedroom dinsa Kai tsaye ya sakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa dasuka sauya Yana sake riqe kansa da kamewa.

Ita Kam tana komawa daki sallar ishai tayi zuciyarta cikeda farin cikin yau tayi fira da Abbinta kaman da
Tayi Shirin bacci ta haye gado tayi kwanciyarta tana jin yanayi Mai qarfi fa girma a zuciyarta gameda Abbinta Wanda takejin yanafin na dah.

Washe gari fes ta shirya cikin haricca long knitted skirt and blouse milk sai vincci loafers ta fito ta wuce aiki Bayan taje ta gaida Haj umma
Umma yaganah Kuma tare sukai breakfast Abbinta Kuma Bai fitoba da alama Bai tashiba.

Agurin aiki yau ma umma Hadiza tazo sunyi fira sosai kafin tadawo gida.

Tun a harabar gidan tasan anty Hafsat tazo sbd taga motar CM daya.

Batai tsammanin samun harda dr farhataba a gidan Dan haka duk fitarta da Anty Hafsat Basu wani samu sinyiba gashi Haj umma ta cika kowa da kulawarta akan Dr farhat wadda itama sosai take nuna Jin dadin hakan Dan tasan tagama samun guri a gun AA MAJEED.

Har dare Basu samu sunyi maganaba yanda ya kamata saidai sama sama anty Hafsat din tasake nanata Mata akan itace Zata gyara aurenta yazama kaman kowanne aure da kanta.

Bayan tafiyar anty Hafsat da Dr farhat rasa abin kamawa tayi saidai ta shiririce gurin waya da Neesah wadda suka qarasa shiriricewa akan firarrakinsu na Yan Mata yanda suka Saba.

Sallar ishai tayi ta fito zuwa dakin umma yaganah sbd sunci abinci already tun dazu taredasu Anty Hafsat.

Tana Shiga dakin zubbi tace”

Abincin Sir yazama ready zaa aje a dining ne kokuma zaa kai Masa dakin Haj umma?
Ko a palonsa zaa Kai?

Kallon Inayah umma yaganah tayi daga zaune tace”

Kije ki Kai Masa palonsa basai an jera a dining ba.

Fitowa tayi tareda zubbi batareda taje dakinta ta sauya kayaba ta dauki qaramin tray din da tea ne akai sai faten dankali dayaSha kayan ciki da curry.

Kai tsaye palonsa ta nufa da tray din tana shakkar kada abbin yayi Mata fadan kayan jikinsa sbd akwai sanyi gashi Riga da wandon baccine ajikinta masu santsi Kuma wandon ba har qasa bane ko bra Babu ajikinta.

Tana shiga palon sanyin AC daya Gama gauraya da turarensa ta shaqa tareda nufan table ta ajiye tray din tana dagowa Yana fitowa daga bedroom dinsa sanyeda pyjamas shima
fuskarsa tayi fresh kaman baya Shiga Rana.

Akan kayan jikinta idanuwansa suka fara sauka ya dauke Kai Yana qarasowa ya zauna.

Zama tayi gabansa tana daukar tea din ta miqa Masa tana cewa”

Abbi barka da da fitowa.

Numfashi yafara saukewa ahankali kafin ya dago ya kalleta tareda sakin taqaitaccen murmushi yace”

Barka Dr Inayah majeed.

Dadi taji sosai ta taso daga gabansa ta dawo gefensa kusa dashi sosai tareda dafa cinyarsa Saura kadan ya qware da tea din dake bakinsa tayi saurin janye hannunta tana kallonsa Dan itama batasan a cinyarsa ta Dora hannunba.

Daqyar ya hadiye Wanda ya kurba a bakinsa tareda juyowa ya kalleta idanuwansa na gangarawa ga bakinta dake motsi tanason yin magana Amma takasa sbd idanuwansa dake Neman rudar da ita.

Qamshinta ya shaqa ahankali tareda Dan rufe Ido ya bude Yana ajiye cup din hannunsa ya juyo gabaki daya Yana kallonta
Magana yakeson yin Amma qamshinta yayi Masa yawanda yake kokawa da nutsuwarsa ya hadiye numfashi ahankali zai bude Baki yace ta tafi tayi saurin Kai hannunta kan bakinsa ta rufe sbd tasan korata zaiyi….

Saukar tafin hannunta Mai taushi akan bakinsa yasashi rufe idanuwansa dasuka sauya ya bude ya watsa Mata idon numfashinta na shiga hancinsa tareda qamshinta Kai tsaye Wanda yasa numfashinsa Dan sauyawa.

Janye hannunta yayi Kai tsaye Yana fuskewa tareda daukan cup dinsa yakai bakinsa Yana kurba a natse yace”

Kije ki saka kayan sanyi ki kwanta akwai sanyi yau.

Zuciyarta dake bugawa da qarfi ta dafa da sauri tareda kallon gurin tana Jin yanda bugun zuciyarta ke qaruwa.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta Jin Bata motsaba
Yaga hannunta kan kirjinta dayaketa kaucewa kalla sbd yanayin datake ciki….

Sosai tsatsayyun kirjinta suka nuna basa batareda bra sbd yanda suke motsawa kadan cikin santsin rigarta.

Kaman Mara lafiya ya dauke Ido daga kanta yakasa tambayarta lafiyarta data dafe kirji sai kawai a hankali yace”

Kije ki sauya kafin sanyi ya kamaki.

Bata musaba ta miqe ta nufi kofa ta fice sbd bugawar da kirjinta yakeyi yasata Shiga fargaba da tunanin itakuma.

Tana fitowa Palo suka hadu da Haj umma data fito daga dakin umma yaganah dubota da ciwon kan datace tana Dan ji tun yamma.

Da boyayyan mamaki take kallon Inayah wadda ke tafiya a sanyaye hankalinta baya ma kan Haj umma din Dan Bata lura da itaba.

Kai tsaye dakinta ta wuce tareda fadawa kan gado tana shigewa bargo ta lumshe ido tanajin sabon feeling Mai qarfi akan Abbinta.

Daqyar tayi bacci da daren Dan haka tayi lattin tashi…

Shima Abbi ranar baisamu wani bacci ba Dan haka tunda safe ya shirya ya fice sbd zuciyarsa dake buqatan iskan da Babu Qamshin Turaren ‘yarsa ko kansa zai sake.

Da wuri Inayah ta dawo Dan kawai tasamu fira da Abbinta Amma Bai dawo da wuri ba
Qarshema ranar sai dare yadawo Bayan sunyita jiransa itada Haj umma Amma sai kusan 10 yadawo Kuma Kai tsaye yayi musu Saida safe ya shige sbd Yana tareda gajiya.

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button