BABU SO 62

“Mi matata kuma tayi? Ko zaki huce haushinnne a kanta. Faɗamin, wai BABU SO! MIYA KAWO KISHI?”.
Dakatawa tai daga shafa man datai niyyar farawa, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi suka haɗa ido ta cikin mirror. Da sauri ta janye nata tana cuna baki gaba. “Yaya kaima kasan SO ɗin da kishin. Da zaka rarrabe munma wlhy dana biyaka”.
Murmushi ne ya sake suɓuce masa, yasa hannu ya karɓe man hanunta ya ajiye, sake ƙoƙarin ɗauka tai ya riƙe hannun. Dole ta ɗago tana kallonsa, hakan ya bashi damar da yake buƙata, ya sarƙe idanunta a cikin nasa yanda ya tilasta mata tsaiwa suka kurama juna ido, kallon juna suke irin na tsakkiyar idon nan mai ratsa jinin jiki da bargo ya sunce duk wani ƙwarin laka da jijiyoyi. A hankali lips ɗinsa suka fara motsawa…
“Kin tabbatar idan na rarrabe mikin zaki biya ni?”.
Da wani salon zamtowarta jiki a kasalance ta janye idanunta a slowly, shima janye nasan yay da wani salon lumshewa da buɗewa tare da miƙewa da ƙyau ya juyota suna fuskantar juna saboda kujerar na juyawa.
“Yayaaaa!”.
Ta faɗa a shagwaɓe.
“Yayoo”.
Ya bata amsa da sake ranƙwafowa akanta tamkar ɗazun, banbancin kawai yanzu suna fuskantar junane. Turashi ta ɗan farayi amma ko gezau, sai ma hanun daya riƙe ya ɗaura saman fuskarsa daga gefen kunne. “Idan kin isa kalla cikin idona ki maimaita abinda kika faɗa”.
“Ba buƙatar haka ai Yaya tunda nasan kaji. Aysha fa na gidan nan, kaima kuma matarka nacan na jiranka”.
“Uhmm Madam pretender ke kuma budurwa tace ko?”.
“Hu’um nayi me da kai? Kamun tsufa”.
“Yanda kikai dani daren shekaranjiya mana”.
Janye hanunta tai da ƙoƙarin juyawa tana faɗin, “Kai dai ka sani”.
Yanzu kam ƙaramar dariya ya saki mai faɗi da miƙewa sosai akan ƙafafunsa. Yitai kamar bata jisa ba taci gaba da shafa manta yana kallonta kamar ya samu tv. Saukar kiran salla a kunnensu ya sakasa kallon agogon ɗakin, ya ɗan furzar da numfashi dan yasan sai ya sake sabuwar alwala.
Binsa tai da kallo ta gefen ido, yana shigewa ta taɓe baki da miƙewa tana magana ƙasa-ƙasa. Kaya ta saka sauri-sauri kafin ya fito. Tayi ƙyau sosai dan ƙanan kaya sun zame mata jiki matuƙa, har takai komi ta raɓama ɗan jikinta sai ka ganta kamar ka sace. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, dan ya tabbata ya cigaba sunan alwalarsa karyayya again. Ita bama tasan yanai ba, powder take ɗan shafama fuskarta da ɗan lipsgloss, dan ko kwalli ba sakawa take ba sai Mamie ta tsaya a kanta. A ransa yake raya da kwalliyar tafi haka daya so, sai dai yasan ita ƴar darun tasa a wajenta hakan normal ne. A haka ɗinma tayi ƙyau sosai.
Ita ko sanin kaya yake canjawa yasa taƙi juyowa, harya gama shiryawa cikin wandon jeans blue da pitch shirt mai dogon hannu. Jin tsaiwarsa a bayanta ya sata ƙoƙarin barin gaban mirror ɗin, amma saiya riƙota ta hanyar saƙala hanunsa saman cikinta ya manna bayanta da ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba. Ɗagowa tai tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta. Ganin ya ɗago lipstick da dayan hanunsa ta maida idonta akai. Saman lips dinta ya ɗaura, zatai magana yace mata “shiii!”.
Shiru ta haɗiye abinda take son faɗar, shi kuma ya fara goga mata. Sai da ya gama ya juyota suna fuskantar juna, bakin ta ɗan tunzura gaba ganin yanda yake kallonta.
“Nifa shanyewa nakeyi shiyyasa bana sawa”.
“Oh really? To bara na shanye abuna kafimma ki shanye min”.
Idanunta ta waro waje da zaburowa zatai magana ya samu damar sauke lips ɗinsa akan natan. Dole ta koma tai laƙwas dan bai musu kamun wasa ba……..✍