BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 63

    Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko’a shigowarta gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce, musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana ayyana zaima tufƙar hanci….

    ★★★

 “Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta. 

   Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi kuma blood?”.

 “Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”

  Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi. “Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama munafunci kesata yimin wani abun”.

   Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka abincin?”.

   Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.

  Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba. 

     Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya ɗiba yakai bakinsa tayi. 

  “Wai da gaske kakeyi?”.

Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.

     Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace, “Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.

  Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.

 “I’m not…”.

Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala’in diriricewa. Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare. “Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.

    Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke murmushin ba.

    Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki? Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita ba. 

  “Yaya ka gani fa ka koreta?”.

“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da doctor ɗin can kar naje barruwa.”

  Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa. “Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.

    Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.

 “Ke minene naki sunan?”.

   “Kanwarka kaima da kowa an sani”.

    “Really?”.

  “Yap!”.

“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.

   “Kai ka san wani garden Yaya”.

“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye kayana k……”

  Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya haɗiye sauran maganar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne……..✍

Next Chapter

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button