BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 63

Chapter 63
63

………Tsaf ya shanye jambakin, zaune takai tana sauke numfashi, shima barin wajen yay da ɗan hanzari, tanaji ya buɗe toilet amma bata iya ta ɗago ba. Babu jimawa ya fito da alama wata sabuwar alwalar ya sakeyi. Ƙofa ya nufa batare daya yarda ya sake kallonta ba yana faɗin, “Ki tashi kiyi salla”.

    Iska ta furzar mai ƙarfi da dagowa tana kallon kanta ta cikin mirror, sai kawai ta samu kanta da kai hannu ta shafi lips ɗin nata da sakin murmushi. “Fitinanne”. Ta faɗa a hankali tana mikewa. Itama alwalar ta ɗauro, bayan ta gabatar da salla samun kanta tai da komawa gaban mirror ta sake gyara fuskarta da ƙyau cikin simple kwalliya. Kwalli, lipstick ɗin daya saka mata ta ɗan gyara girarta siririya da ƙara powder. Ita a karan kanta sai da ta tsaya kallon kan nata dan wani ƙyau taga ta kara, tai guntun murmushi da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta..

     Ana idar da salla ya dawo gidan, saboda makara salla daya nema yi bai shiga sashen Fadwa ba ya wuce, yanzu kam daya dawo sai ya fara nufar can, wannan ƙa’idarsace, akowace salla in har yana gida sai ya tabbatar da mace tayi hankalinsa ke kwanciya, ko yana office yakan ƙokarta ya kira domin tambayar kinyi salla, hakan ya ƙara ƙarfafa Fadwa domin waya takan ɗauki hankalinta ta kasa tashi yin salla akan lokaci kafin zuwanta gidansa matsayin mata. A bedroom ya sameta ta idar da salla fuskarta duk babu walwala. Ya ɗan tsura mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙaraso ciki sosai. Sau ɗaya ta kallesa ta janye idonsa da masa sannu ciki-ciki.

   “Wani abu ya faru ne?”.

Ya tambaya a maimakon amsa mata sannun da tai masa. Batai magana ba, sai dai ta sake ɗan tsuke fuska. 

  “Nasan kin jini fa”.

Kamar bazatai magana ba sai kuma ta ɗago idanunta dake tara ƙwalla tana kallonsa, “Soulmate karka juyamin baya dan kayi aure, maƙiya zasu iya yimin dariya”.

   Mamaki shinfiɗe akan fuskarsa yake kallonta. “Juya baya kamar ya? Anyi wani abu ne?”.

   “In ma ba’aiba ga hanyar yi nan an ɗakko ai. Tunfa da matarka ta dawo gidan nan yau baka sake leƙoni ba, kana ganin hakan adalci ne? Yaufa ko zuwa kacemin na tashi nai salla bakayi ba, kuma tun ɗazun kana’a sashenta ita dan daga can ka wuce massallaci, gaka nan harda canja kaya alamar yin wanka”.

  “Dama kin saka a ringa miki gadina ne? Ko kuma shiga sashen nata ma akwai wata ƙa’ida ta mintunan da zanyi na fito? Ni da matata kuma kina tuhumata dayin wanka kamar wanda ya ajiye wata karuwa”.

    “Niba haka nake nufi ba, amma dai koyaya ai sai kana adalci. Jiya yini guda kuna tare a asibiti, hakama yau tun fitar safe da kai kuka dawo tare kana a sashenta”.

 Sosai ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa, idanunsa daya tsareta da su har suna canja launi. “Okay ke da sokike na watsar da ita kenan a asibitin nazo na tare a wajenki bayan nine sanadin zuwanta can. Ko kuma dan kar ranki ya ɓaci bazanyi wanka a sashenta ba?. Look Fadwa idan kikace zaki ɗaukemu zuwa wannan layin bazaki taɓa shan lalai a wajena ba. Idan kin manta bara na tuna miki, Juwairiyya matata ce, idan yanzu na shiga inda take ta rayamin kasancewa da ita zan samar da wannan farin cikin nai wanka na fito koda anjima hakan zai ƙara bijiromin idan ma wannan kikema zagaye-zagaye zargin nayi. K da ita duk abu ɗaya kuke a wajena, ina fatan kuma tsaida adalci akan kowaccenku. Duk wacce take da wani tuggu nason rinjayata gareta ita kaɗai na cutar da ƴar uwarta ALLAH ya hanata wannan damar ko wacece a cikinku. Abu na ƙarshe dazan gaya miki shine daga yau ki sani Ina son Juwairiyya! bawai cushenta akai minba kamar yanda na fahimci ke tunaninki ke kaiki. Yanda na aureki domin so bisa jagorancin iyaye haka itama na aureta, kuma koda ace iyayenmu basu ɗaura mana aure ba ni da kaina Zan nema aurenta, dan hakan burina ne, hatta wannan gidan da sunanta aka ginashi itama, kema shaidace tunda sashe biyu kika tarar. Kinga sai ki sakama zuciyarki salama, ki nisanta kanki da zama mai fuska biyu a gareni, dan bazan daina kasancewa da ita ba domin farin cikin. Sannan ita bata taɓa nuna damuwa da kasancewata a wajenki ba abinda ke gabanta takeyi, mtsoww stupid har kina faɗamin wai na dinga adalci”. Ya juya ya fice a fusace.

   Da gaske Fadwa tayi mutuwar zaune tun fara maida mata raddi da yayi, ga wata irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinta sharkaf. Buga ƙofar da yay da ƙarfi ya sata zabura ta dawo hayyacinta, rawa lips ɗinta suka fara alamar magana take sonyi amma taƙi fita, sai kuma ta mike zumbur tana rarumar wayarta ta kunna fitila duk da kuwa ɗakin akwai hasken wutar nefa. Tabbas maganin data zuba ɗin gashi nan, sannan ya taka kuma ai kamar yanda Aunty Safarah da Mama suka tabbatar mata idan ya taka babu wani magana da zatai ya musa mata. Hakama zoben da suka bata na mallaka har biyu gashi a hanunta, sun kuma tabbatar mata mata da yawa suna rububin saya kuma yana aiki akan mazajensu. Mi (hakan ke nufi?) ta tambayi zuciyarta ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri idonta ƙyam akan zoben mallakar dake a yatsanta tana murzashi da tunanin ko batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo. 

    *_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa, kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. ????????haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi’ar da suke nuna mana kuma ba itace rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana’a akwai na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa ganinsu a idanun al’umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama ɗorarre).

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button