BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 68

Chapter: 68

……..Yau ta kasance cikar kwana bakwai na kwanakin Anaam a gidan, miji zai koma hanun Fadwa kenan. Sai dai kuma tunda garin ma ya waye bata ganshi ba. Tunda sassafe ya fice sakamakon kiran daya samu daga Engineer ɗin dake kula da aikin ginin wani ƙaton mall da sukeyi na wasu larabawa da suka buɗe branch anan kano. Shine ya zana mall ɗin kamfaninsu kuma ke ginawa, to yanzu a dalilin wani mai musu zagon ƙasa wata matsala ke neman shigowa. 

    Su dukansu ma babu wanda ya san baya gidan sai zuwan Khaleel tare da mai haɗama Anaam tv. Anaam taji wani iri dan a tunaninta ko abinda ya faru a daren jiya ne ya sakashi fitar tunda sassafe. Amma sai batace komai ba dama duk sukuku ta tashi. Itama Fadwan ta jingina fitar tasa ne akan abinda ya faru jiya da dare, sai dai saɓanin Anaam ita tsorone ya kamata da tunanin kodai ya gano tana tiktok ne? To amma idan hakane ai ba fita zaiba wayarta zai fara bincike. Sosai ta shiga taraddadi, cikin tsaida mafita ɗaya ta nema zuwan su Sima gareta. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu sun iso harda Bibah da Siyyah suka ƙulle a ɗaki suna tattaunawa. Maman Abu ta girgiza kai da jinjina wautar Fadwa matuƙa, abinda duk ya faru tsakaninta da Shareff jiya ta gani, ta kuma fahimci raye-rayen da Fadwan keyi Shareff ɗin bai sani ba. Shiyyasa ta tsorata da tunanin ya ganta a jiya. Inama Fadwan zata saurareta data bata shawarar dawowa kan hanya domin gujema zuwan ranar dana sani, dan ta tabbata waɗan nan ƙawayen nata data bama amanar rayuwarta sune waɗan da zasu fara kaita ƙasa kafin su Aunty Malika. Mata irin Fadwa da yawa rashin alƙiblar kansu ke tarwatsa musu rayuwa da nasarori koda ace akwai wasu ƙyawawan halaye abin dubi tattare da su, kafin su farga taurarinsu ya gama disashewa a idon duk wanda zai kasance zagaye dasu, a lokacin kuma dukkan damanmakinsu sun kufcewa yunƙurinsu da taɗesu ga zuwa nasarar da su suke kallo a cikin idanunsu duk da suna ƙoƙarin cimmatane a cikin kuskure na son zuciya.

    Anaam kam dai sukuku ta yini har yamma akan rashin ganinsa, zuwa la’asar sai zuciyarta ta kasa dauriyar ɗauka dan koba komai shi ba abin yadawarta bane ba. Wayarta ta ɗauka, ta gwada kiransa yafi sau goma kafin tai ƙuru ta danna number da ko saving nata ta gagarayi amma ta gama haddaceta tun a kiran da yay mata jiya bayan ta gama ganin kundin sirrinsa mai ɗauke da sirrikan da ita kaɗai suka shafa.

    A lokacin yana zaune ne ya gama yin liƙis da gajiya da yunwa. Dan duk yau ruwa kawai yake iya kaiwa bakinsa tsabar zafin da kansa ya ɗauka akan al’amarin dake zagaye da su. Bashi ba hatta Fharhan da Khaleel da wasu a cikin staff ɗinsa a jigace suke. Juma’a guda haka ta riskesa ko wanka baiba da kayan dake jikinsa kanana sukaje sallar juma’a. Baiko duba waye mai kiran ba ya kai kunnensa. Can ƙasan maƙoshi tai sallama kamar maijin tsoro. Curo wayar yay a kunensa da mamaki, ganin tabbacin ita ɗince ya maida yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da har tana iya jiyowa. Ta ɗan murmusa daga can, tare da langaɓe kai kamar tana a gabansa.

  “Yayaaa!”.

 Yanda ta ambaci sunan cikin ƴar shagwaɓa ta saka tsigar jikinsa tashi, yaja numfashi a slowly.

  “Uhhum autar mata”.

Ta saki siririyar dariyar data ƙara tunzurashi. “Yaya ka rufamin asiri da sunan nan kar mata sumin duka”.

     Murmushi yayi a karon farko, da ɗan gyara zamansa. “Kice na faɗa da shela ko hakan zaisa su tabbatar ke ɗin ta ƙarshe ce tabbacin Autarsu”.

  “Nidai ba ruwana gaskiya. Wai kaje ina ne?”.

  “Yawo mana”.

“Yawo fa Yaya? Ai nasan baka yawo, kai da kullum kana company ina zaka aiki, ina ka dawo aiki”.

    “Oho shaidar da kikamin kenan?”.

  “ALLAH gaskiya na faɗa. Dan ALLAH ina kaje?”.

“Kina kewata ne?”.

Kamar tana a gabansa ta rufe fuskarta da filo. “Ɗan kaɗan”.

  Dariya yayi kam yanzu har Fharhan na kallonsa. 

 “Wato ɗan kaɗan? Autar mata kiji tsoron ALLAH fa”.

    “To ai nama daina ji yanzu gaba ɗaya”.

  “Oh-oh, maimakon na samu ƙari sai a kwashemin ma duka? Aji tausayina mana diamond girl”. 

     Sosai take dariya sai dai a nutse, (kece farin cikin duniyata) ya ayyana a cikin zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa. Ji yake tamkar yaga kansa a gabanta kawai. Daga can Anaam data tsagaita dariyarta da iya gaskiyarta tace, “Am serious gidan babu daɗi dan ALLAH ka dawo”.

    Da ƙyar ya iya danne zuciyarsa dake tsalle-tsalle, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Mi kika tanada min ne?”.

  “Duk abinda kace kana so”.

“Kin tabbata ko minene shi zan samu?”.

     “Ga wani ma tun kafin kazo”. Ta faɗa dayin kissing wayar. Har tsakkiyar kansa yaji saukarsa. Kafin ya samu damar cewa wani abu ta yanke wayar ƙit. Ƙoƙarin dakatar da ita yake amma bataki jisa ba, yay ƙoƙarin sake kiranta taƙi ta ɗaga, hanunsa ya kai yana murza goshinsa da cije lips.

    Itako dariya takeyi daga can zuciyarta cike da farin ciki mai ban mamaki. A haka Aysha ta shigo falon ta sameta. “Blood wai kin san wace kwamacala na gani kuwa?”.

  “A ina kenan?”.

Anaam ta faɗa tana tashi zaune da ƙyau. Cikin tsananin ɓacin rai Aysha takai zaune. “Wai ƴan iskan ƙawayen can na Fadwa fa naga takai sashen Yaya suna masa gyara”.

   “What!! gyara fa?”.

“Wlhy na rantse miki gasu can ma kuwa”.

   Miƙewa Anaam zatai Aysha ta maidata. “Kinga kwantar da hankalinki ba so nake kije ba. So nake kiyi duk yanda zakiyi Yaya ya dawo gidan nan yanzu shine kawai maganinsu. Dan yanzu in bai gani ba su Mommy zasu iya ƙaryatawa tunda ba san laifin Fadwan suke ba”.

   Shiru Anaam tai tana kallon Aysha. Tabbas maganarta haka take, sai dai kuma ta yaya zata saka Shareff ɗin zuwa bayan yanzu suka gama waya ma…….

    A lokacin da su suke shawarar yanda zai dawo gida a garesa ma akwai himmar hakance tattare da shi. Jiyay gaba ɗaya tattaunawar tasu ta gundiresa. Ya miƙe yana tattare takardun gabansa. “Fharhan kubar abinda ya rage zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a ƙarasa. Tunda namayi magana da Abie sai zuwa gobe zamu tattauna da shi yau yana Abuja shi da su Daddy”.

   Mamaki shimfiɗe a fuskar Fharhan yake kallonsa. “Dude amma kaine fa kace sai an ƙarasa komai yau miye na canja shawara?”.

     “Na gaji ne, ga yunwa na neman fara katsamin hanjin ciki”.

  “Uhhmyimm!!. Kodai soyayya malam. Lokaci yayi da zaka bar wani ɓoye-ɓoye ka buɗe mana mu kalla ko ma samu na kwaikwayo”.

     “Banza ɗan sa ido”.

   “Naji ba komai. In ka isa kace ƙarya na faɗa mana. Da an langare ana mana ciwo tunda kaji ka samu sai mukaji tsitt”.

   Spoon dake cikin kofin daya sha coffee ya dauka ya jefa masa. Fharhan yabar wajen da gudu yana dariya. Gaba yay shima yana faɗin, “Munafuki mai barci da ido ɗaya. Haka zaka ƙare rayuwarka a bibiyar tawa bakai aure ba tuzurun banza”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button