INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 66-70

66_*
Arewabooks@Mamuhgee
Yana barin dakin Bai samu nutsuwa sosaiba Saida ya koma dakinsa ya daga waya ya Kira babban Likitan Daya sani mutuminsa ne sosai a Australia yayi Masa bayanin halinda Inayah din ke ciki
Dr Aron yayi Masa bayanin ba komai bane cikin qanqanin lokaci Zata warke sumul idan tanashan magani da kulawa.

Umma yaganah kuwa kitchen Takoma da kanta ta dorawa Inayah din farfesun qoda da hanta Mara ruwa ko sai veggies kawai.

Kafin tagama tana kitchen anty Hafsat suka iso itada Safnah da mimi dubiya duk da Mimi da Hafsat basusan menene ciwon na Inayah ba anty Hafsat ce kawai tasani Kuma itama hankalinta tashi yayi da umma yaganah ta sanar Mata anyiwa Inayah din dinkine.

Sai bayan azahar ta farka jikinta a sanyaye ba qwari sbd tsamin da jikin yayi,

Tashi zaune tayi ahankali tana Dan rintse Ido sbd ciwon dake jikin nata.

Mimi ce cikin kulawa ta ringa Mata sannu tana tambayarta Yaya jikin nata,
Safnah ma cikeda kulawa tayi Mata ya jiki
itadai ba bakin magana saidai Kai kawai datake dagawa ahankali..

Anty Hafsat kuwa tanason yimata magana da dama Amma ganin su Mimi yasa batai dinba ta Bari sai Inayah din da ita suna  su Daya.

Kallon anty Hafsat tayi fuskarta a Dan marairaice ta bude Baki tace”

Anty Hafsat zanje toilet ki taimakamun.

Jin hakan yasa Mimi ficewa daga dakin ta nufi dakin Haj umma Dan su gaisa tunda Koda suka shigo sun tsaya su gaisa Amma tana toilet gurin wanka,
Safnah ma bin bayan Mimi tayi Dan gaida Haj umman su dawo.

Suna fita anty Hafsat ta Kama Inayah dake tafiya ahankali kaman me koya suka nufi toilet.

Fitsarin datai shima kusan Jin take kamar tayita kuka tana dorawa Abbi laifin.

Ruwan dumi tashiga na Yan mintuna kafin tayi alwala ta fito tana tafiyar ahankali batareda an taimaka mataba sbd ruwan data Dan Shiga din ya rage Mata radadi kadan Kuma taji Dan sauki saukin radadin.

Sallah tafara Yi tana idarwa ta gyara zamanta ahankali tana daukan wayarta da kusan massages dinsa ne suka shigo duk a jere gasunan Yana tambayarta Yaya jikin nata tareda kalmar

“I’m sorry babyn Abbi”

Karanta sakonnin kawai tayi batareda ta maida Masa amsaba zubbi takawo Mata farin cous cous da farfesun da umma yaganah tayi Mata sai ruwa Mara sanyi.

Ta ‘dan ci abincin sosai sbd rabonta da cin abincin arziki tun shekaran jiya da wainnan abubuwan suka fara samunta.
Tana gamawa anty Hafsat ta Bata magani Tasha daga Nan tasake Dan sakewa su Safnah na dawowa daga gaiso Haj umma suka fara Yar fira sama sama Mimi na sake tambayarta meke damunta shiru kawai Inayahn tayi sbd Batasan me zatace ba kokuma ta fada wani ciwon daban Wanda zaisa zancensu ya Zama biyu itada anty Hafsat Dan Batasan me tacewa su Mimin na damunta ba.

Fira sukayi ringa yimata dukkaninsu a dakin umma yaganah suka koma sbd umma yaganah din datace su koma can cikin dubara sbd dakin na Inayah yanzu kaman na mijinta ne tunda Yana kwana ciki ga curtains din dakin da Safnah ta nace da tambayar meya samesu suka katse da qarfi haka¿

Babu Wanda ya sani bare ya bada amsa amsa
Inayah data sani amsar Bata faduwa daga bakinta jiya Abbinta ya balla gado yau Kuma tace damqi curtains ne sun balle¿

Suna dakin umma yaganah sunata fira Haj umma na Palo zaune masu sauya curtains sukazo suka wuce bedroom din Inayah din aka gyara ballewar da akaiwa can Inda suke daga saman aka maida curtains din suka fita suka wuce yau dai Bata ce ko kalma daya ba Ido tabisu dashi harsuka Gama suka fice,
Ko MAJEED Dake gidan, shima yashigo dasu Bata tambaya ba sbd gudun jin abinda zai bata ruwa.

Su Mimi a Nan suka wuni se magriba suka wuce aka bar anty Hafsat ita Saida tayi Isha a gidan ta wuce Bayan tasake tattaimakawa Inayar tasake shiga ruwan dumi da sauran abubuwan dazasu taimaka Mata gurin warkewa da wuri.

Neesah da Anty Hafsat sunyi dariyar Inayah din harsun gaji Amma dai anty Hafsat Bata nunaba Neesah kuwa zagewa tayi tayi abarta a vidcall dasukai tana cewa”

Babes, stitches fa?
Are you for real????
Wlh Nima inason hakan idan time Dina yayi….ihun dariya takeyi tana sake mamakin Inayah data kasa magana sai Bata fuska da cewa”

Abinda yafi stitches dinma Zaki samu idan dai bakinki bazai rokarwa kanki Alkhairi ba,
Anfada Miki ba stitches dinma da sauki ne bare anyi?
Ni bani ba sake yin sex na rufe bazan qaraba.

Dariya Neesah keyi tana sake mamakin yanzu Abbinsu ne da wannan aikin.

Suna Gama waya bayan tafiyar anty Hafsat tanason komawa dakinta tayi wanka ta kwanta Amma takasa sbd fargabar yauma Abbi zai iya zuwa Kuma tasan sauran azabar dazata biyo bayanta
Dan hakan ta qi tafiya Dole toilet din Umma yaganah tayi wanka bayan tasaka zubbi taje ta dauko Mata towel da kayan baccinta.

Ta gasa jikinta sosai tareda shiga ruwan dumi tagama ta shirya cikin kayan baccinta masu kauri ta haye gadon umma yaganah ta kwanta abincin dare dama tun anty Hafsat na Nan sukaci.

Umma yaganah data gamo firarta a dakin Haj umma tadawo ta tadda Inayah kwance kan gadonta ta lafe tayi bacci abinta
Kallo ta bita dashi tana sakin murmushi tace”

Dama waya fada Miki barno gabas take¿
Ai hakan yamun daidai daga yanzu Zaki rage rawar kan tunda kinsan asalin menene auren yanzu sauran haihuwa itama ki sani saimu samu lafiyar bakin Nan naki.

Toilet ta wuce bayan ta kashewa Inayah din wutar dakin tayo duk sauran abinda zatayi tayo alwala ta fito Dan sun saba basa kwanciya sai sunyi alwala Kuma wannan din duka MAJEED ne ya koyar dasu ya sabar musu da hakan.

Kan gadon ta kwanta tareda Inayah din dayake gadon Gabba ne
Addua kawai tayi ta shafawa kanta da Inayah Tai baccinta itama.

Da asuba umma yaganah da fada da komai suka Shiga ruwan zafin sbd Inayah dake maqalewan bataso
Haka ta bude Mata Ido batari suka shiga ruwan ta Dan jima ciki kafin tayi alwala ta fito tayi sallah.

Tana idarwa komawa tayi ta kwanta batareda ta kunna wayarta data kasheba Dan tasan Abbinta Kira zaiyitayi itakuma ko muryarsa shakkar ji takeyi batareda ta warkeba sbd tasan muryarsa na shiga kunnenta zuwa gurinsa zatayi sbd tayi kewan ganin Abbin nata.

Sai qarfe goma ta tashi Kuma a Nan takuma wanka ta saka wata qaramar Riga Mara nauyi da tsayi sosai
A daki aka kawo Mata breakfast dinta tayi tana gamawa ta koma gadon ta haye tanason kunna waya Amma ta daure taqi.

A nasa bangaren a zaune yaga safiyar ranar tayi sbd ko rufe Ido yayi idan ba ganinta zaiyiba radadin budesu yakeji,

Wayarta Bata Shiga,
Massages dinsa ba reply,
Yayi yawon dakinta a cikin daren yakai so biyar Kuma Haj umma na jinsa duk zagayen yawon dayake
Amma tayi shiru tana mamakin ikon Allah ikon Gaskia.

Qarfe goma yasan tana tashi yawanci Dan haka karfe goman ya fito a shirye cikin ash brioni suit da black Christian louboutin fullcover shoes yafito Yana fidda wani sahirtaccen qamshi me sanyi da Dadi fuskarsa a natse saidai zuciyarsa a hargitse take rashin ji ko ganin Babynsa.

A dining sukai breakfast shi dasu umma Amma Babu Inayah
Ya kasa daurewa ya Dan dago a natse ya kalli umma yaganah yace”

Yaya Inayah?
Ya jikinta?

Nauyi ne ya rufe umma yaganah da Haj umma data saki Baki tana kallonsa har zai iya tambayar jikin Inayah a gaban idonsu bayan kowannensu yasan menene matsalar Inayah din.

Cikin Jin nauyi umma yaganah tace”

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button