BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 68

   “Aniyarka ta bika wlhy, insha ALLAH nanda 2months zaku kaini”. Fharhan ya faɗa daga jikin motarsa yanama Shareff dakuwa.

      Murmushi yay da buɗe mota ya shige batare daya sake tanka masa ba….

   Tafiya yake amma ji yake kamar motar bata sauri, ya ƙara gudu tamakar mai shirin barin garin na kano. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, horn yayi har sau biyu amma maigadi bai buɗe masa ba. Yay dan tsaki da buɗe motar ya fita ya ƙarasa shiga da ƙafa da niyyar yima maigadin faɗa sai ya samu ashe yana bayi ne. Kansa kawai ya girgiza yay gaba, dan ya gwammace zuwa anjima ya shigo da motar kawai.

   Harya nufi sashen Fadwa ya fasa, kai tsaye nasa sashen ya nufa dan yafi buƙatar watsama jikinsa ruwa kafin komai. Tun a ƴar barandar gaban sashen nasa yaci karo da takalman mata. Mamaki yay matuƙar kamashi wani gefen zuciyarsa kuma na ayyana masa ko Mommy ce da muƙarraban ta, to amma takalman basuyi kama da wanda Mommy zata iya sakawaba dan duk hills ne. Kamar mai tsoron shiga ya tura ƙofar a ɗarare. 

  Dai-dai nan Amal dake goge-goge a falon ta ɗago da tunanin Fadwa ce da taje ɗakko turaren mopping ta dawo. “Yauwa baby kin ɗakk….” sauran maganar ta maƙale a harshenta. Ƙaf yawun bakinta ya ƙafe ta saki towel ɗin hanunta ƙarami da take goge-gogen da shi.

   Ana haka itama Bibah dake gyara bedroom ta kawo jiki zata fito, ai ba shiri ta koma da sauri cikin harbawar ƙirji. Sima dake kitchen ce ta shiga ƙwalama Amal kira, sai dai Amal ta kasa amsawa saboda tsabar firgita datai da ganin Shareff. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa dake cike da gajiya sun matuƙar kaɗawa zuwa launi mai razani. Duk da baice da su komai ba kowacce a cikinsu jikinta rawa yakeyi, Amal sarkin tsoro ta fara daga hannaye sama cikin rantsuwa da rawar murya..

   “Wlhy tallahi ba laifinmu bane ba yallaɓai, Fadwa ce ta sakamu mu taimaketa da aikin, amma ALLAH ba mune muka kawo kammu ba, kuma aikin kawai muke maka ba wani abu ba…”

   “Eh wlhy aikin kawai mukeyi Yaya Shareff”. Cewar Siyyah cikin son karfafa kai dan ita bata ruɗe kamar Amal ba, amma daka ganta kasan a firgice take. Sima kam tuni ta fice a kitchen ta ƙofar baya, itace taje a birkice ta sanarma Fadwa dake kitchen tare da Mmn Abu ana haɗa abincin tarbar Shareff ɗin. Ita kaɗai ta nufo sashin a rikice, sai dai tana ƙoƙarin hana ruɗewar tata a zahiri saboda shawarar Sima.

   Bibah dake bedroom kam taƙi fitowa, da sauri ta shiga kiran Gwaggo a waya. Tana ɗagawa ta sanar mata komai. “Bibah k mahaukaciyar inace da zaki biyema wannan sakarar yarinyar keda ke shirin shiga gidan matsayin matar gida. Duk yandama za’ai karki sake ki yarda Mustapha ya ganki a cikinsu. Inba haka ba kini sai k da shi sai dai kallo”.

   “Gwaggo kar kimun haka dan ALLAH”.

  “To laifinama zaki gani kenan? Yanzu banda ku shashshune taya zaku zauna ƙawa na baku aiki”.

  “Wlhy Gwaggo na biye musu ne kawai dan dan tace ɗakinsa ne, nidai ki taimakeni yaya zanyi na fito gashi can a falo ya tsare su Amal.”

“Humm sai ki jira matar gidan ta shigo, kiyi amfani da wannan damar kiyi wuff ki fita batare daya ganki ba”.

   “To to…to Gwaggo nagode sosai, idan da wata matsala zan kiraki dan ALLAH”.

  “Naji”.

Gwaggon ta amsa tana yanke wayar. Cikin laɓe baki.

     Shigowar Fadwa tayi dai-dai da saukema Siyyah data matsoshi cikin kwarkasa lafiyayyen mari da sai da taga taurari masu maƙata????????. Ba ita da aka maraba hatta Amaal sai da ta dafe kuncinta da zabura baya kaɗan ya rage ta faɗa kan kujerar dining.

  “Ya salam! Soulmate mari kuma? Shamsiyya ce fa?”.

   Wani matsiyacin kallo ya jefeta da shi fuskarsa na wani irin fusatar azabar dake soya masa ƙirji. Ƙasa tai da idanunta, amma saita matso garesa cikin dauriya ita a dole tana son fahimtar da shi………✍
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO View: 314 Words: 1.7K

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button