BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 73

   Gaba ɗayansu cin abincin suke cike da nishaɗi, dan kowacce ta samu irin farin cikin da take buƙata daga mijinta. Wanda a nata wautan gani take itace ɗaya ƙwalli ƙwal a zuciyarsa. Shiko cin abincin yake wani yanki na hankalinsa naga umarnin su Mommy, sai dai wani yanki najin matuƙar farin cikin ganin farin cikin matan nasa da har kowacce ta kasa ɓoyewa. Koda suka kammala Fadwa bata wani jimaba tare da su tai musu sai da safe ta wuce zuciyarta cike da kishin mijinta. Anaam kuwa ta shiga tattare kayan waje guda. Falo suka koma ita dashi, ya zauna a 3sitter tare da jawota jikinsa....
  Sai da ta bari sun shagala da kallo yana mai cakuɗata a yanda yaso sannan taja numfashi. “Yaya gobe zan koma gun aiki ko?”.
     Tamkar saukar aradu yaji maganar amma sai ya danne. Yay shiru kamar bai jita ba sai da ta ƙara maimaita masa tana ɗagowa ta kallesa. Shanyayyun idanunsa ya zuba mata na wasu sakanni. sai kuma ya dan lumashe da kaɗa mata kai kawai. Ta sauke ajiyar zuciya tana mai hamdala ga UBANGIJI. “Nagode Yaya wlhy na zata zakace a'a”.
“Humm”. 

Kawai yace mata.
Tasan ya shaƙa dan haka tai shiru, ita dai tunda ya yarda zata koma ai Alhamdulillahi koma mi zaiyi mai sauƙine kuma. Saida ya kammala kallon labarai sannan suka mike. Ta fita domin zuwa tai shirin barci shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa bayan ya bata umarnin idan zata dawo tazo masa lipton. Ya mata hakane dan kartai tunanin ƙin dawowar. Kamarko ya sani batai niyyar dawowa ba. Amma babu yanda ta iya kodan son komawarta aiki salin alin tabi umarnin nasa.
Sai da ta shafe kusan mintuna talatin sannan ta dawo cikin zumbulelen hijjab har kasa da cup na lipton. Rashin ganinsa a falo ya sata nufar bedroom ɗinsa kai tsaye. A bakin gado ta samesa yana haɗa wasu takardu da laptap ɗinsa alamar kayan zuwa office yake tattarawa. Ta ajiye cup din a bedside drawer dake gefensa.
“Jazakallahu khairan”.
Cikin jin daɗi ta amsa da “Amin ngd”.
“Kin rufe falon ko?”.
Hakan ya bata tabbacin nan ɗin zata kwana dai, dan haka ta girgiza masa kanta.
“Okay ki rufe kawai”.
Nan din ma kanta kawai ta jinjina cike da tsoro. Sai dai babu yanda zatai dole taje ta rufe ɗin ta dawo. Ta samesa ya fara shan shayinsa. Ya nuna mata gadon da fadin, “Bisamillah ki kwanta gobe akwai fitar safe. In kuma kikace zaki mun irin lattin da kike mun a gida zan tafi na barki ne”.
Baki ta ɗan tura masa batare da tace komai ba. Hijjab ɗinta ta cire ta hau gadon ta kwanta tana mai addu’ar ALLAH yasa kar yace yana bukatar komai. Dan duk da zaren ɗinkin da kansa ya fita saboda yawan shiga ruwan zafi da takeyi ba ƙaramin tsoro da fargaba take shigaba a duk lokacin data tuna za’a iya sake ratsa wajen again. Sauri-sauri tai addu’a ta gyara kwanciya da rokon ALLAH zuwan barci kafin ya kammala shan shayin nasa………..✍

????Abun dariya abun tausai????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button