BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 78

_

     Kwanaki sun cigaba da shuɗawa, ta tabbata dai Gwaggo Halima ta dawo gida da zama, dole ta share sashen Baba Umar da babu wanda yasan a duniyar da yake yanzu ta zauna. Mommy kuma ta koma gidan Baba Ibrahim kamar yanda ya shardanta mata, dan ya hana su Shareff bata wajen zaman da sukai niyya. Yayinda Gwaggo ke cigaba da jiyya mai wahalarwa a asibiti. Dan kuwa babu wani mai jiyyarta sai Nurse’s dake kula da ita. Mommy din ma data raina da kanta tace bazata iya jiyyarta ba dan ƙafar tata duk da likitanci na kula da ita wari takeyi matuƙa. Su Daddy basuyi butulci ba tare da su Baba Ibrahim da mahaifin Fadwa ke biyan kuɗin zamanta a asibitin. Hakama Fadwa na gidansu, mahaifinta ya amshe wayarta, ya kuma kwashe dukan ƴan aikin gidan yanzu itace ke komai ga ƙanenta, girki, gyaran gida, ya baza camaras tako ina, inma bataiba ko baya gidan zai gani, hakama waya kota ƴan uwanta ta ɗauka da nufin kiran wani itama tasan sauran. Duk ta fige ta fita a hayyacinta saboda kuka da tsananin ƙulafucin mijinta da takeyi, ga Gwaggo Halima ta mata nisa yanzu, ƙanenta kuwa sai zuba mata rashin kunya sukeyi tunda dama a haka suka taso na ƙasa baya girmama na sama da shi. Satinsa uku a gidan maganar auren Babansu ya tashi da wata hamshaƙiyar mace ƴar boko mai babban mukamin gwamnati a jihar ta kano………..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button