BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 8

           Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko’ina na falon yace, “Mom tana ina zan makara?”.
      Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.
    Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.
      “Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai da na tadata ta shirya”.
        Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare inada meeting ne mai muhimmanci”.
      “To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.
   Komai baice ba ya juya ya fita.
         Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba. Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta haɗa mata yayi.
     “Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi nima.”
      “Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar matching?”.
    “Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.
   Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda Khaleel ke hararta.

       Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza’a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da shi daga gida da buga game a waya har suka iso.
      “Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.
     Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.
       Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur mana”.
    “Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”.
    Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba. Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.

         Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da addu’a.
        Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff. Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake, sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.
        Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace, hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne. Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka shi kawai saika sake nazari kafin?”.
         “Okay yayi”.
Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan. Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company ɗin…

       Da lokacin tashi yay addu’a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta, har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar motarsa wajen tasan addu’arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.
     Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi? Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.
      Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za’a sauke ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko. Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.
          Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi…. Kafinma yace wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.
       Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin, “Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.
       Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya sata kallonsa a sace tana muy-muy da baki alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa. Sai da ta karanta symbol ɗin wajen ta gane Saloon sukazo, mamaki ya sata dubansa dan batasan mi sukazo yi wajen ba. Ido suka haɗa yana ƙoƙarin kai waya kunensa tai saurin ɗauke nata. Shima janye nasa yay da cire wayar daga kunensa hango Fadwa na fitowa a wajen tamkar tarwaɗa. Tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfa, sai veil siriri data yafa iya kanta ta naɗesa a kafaɗa, ga wani uban glasess daya cinye rabin fuskarta sai dai ya mata matuƙar ƙyau kasancewarta fara ƙyaƙyƙyawa. Gefe da gefenta ƴammata biyune suma ƙyawawa kamarta farare tas da su. Yanda suke dariya zai tabbatar maka wata maganar sukeyi dan har ita Fadwan fuskarta cike take da murmushi. A hankali Anam taja siririn tsaki daya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai dai ta wani kauda kai gefe kamar wadda taga kashi. Sarai ya fahimci dasu Fadwa take, amma sai baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita fuskarsa sam babu walwala dan ya tsani taron ƙawayen Fadwa da suka zame mata kamar jela. Idan ka ganta da wannan yau gobe da waccan zaka ganta, na jibima daban ne………..✍

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button