Zee Baby Book 1 Page 4

*Free Page*
page 4
…..sosai take kuka tana kiransa hankalinsa atashe yazo bakin kofar ya jingina yana sabke ajiyar zuciya yarasa ya zaiyi da zee baby gashi baya son kukanta hankalinsa tashi yake ahankali cikin sanyin murya ya kirayi sunanta ” Zee babyna yi shiru banason kukanki kinji kara sautin kukan tayi tana buga kanta da kofar tana kiransa arikice ya bude kofar ya sunkuyo gabanta ya dagota yana bata hakuri tayi shiru bazai karaba tunda bataso jikinsa ta shige tana sabke ajiyar ziciya bayanta yake bugawa alamar lallashi ransa duk babu dadi shi sam yanzu bayajin shawar kukanta yafi daga masa hankali hannuta yaja suka iso gun kujerun parlon suka zauna tana manne jikinsa har yanzu ajiyar zuciya take sabke dan taji haushin gudunta da yai ya rufo kofa fuskarta ya kamo yana goge mata hawaye ” zee babyna kiyi hakuri ki yafemin bazan sakeba kinji kanwata idanuta ta zuba masa tana taro baki alamar bata hakura ba murmushi ya sakar mata
yana hura mata idkar bakinsa a idanunta lumshe idanu tayi ta saki murmushi ta boye kanta akirjinsa gashinta yake shafa mata yana mata hira mai dadi aikuwa ta fara dariya saida yaga kamar dariyar tayi yawa ya bari kuma cikin ikon Allah duk yada, take manne jikinsa baiji komaiba game da shawarta sai tsantsar kaunarta da take ratsa jininsa da tsokarsa har kusan karfe biyu da rabi ya ga fah batada niyar bacci har gyangyadi ya fara fur ta hanashi idanu ya bude ya kalleta” kanwata kiyi hakuri ki barni na kwanta kinji zee na? ganin yada idanusa sukayi ya bata tausayi duk batason rabuwa dashi ta dauré ta jinye jikinta anashi ” Ahukhuya muje ka kwanta mik’ewa tayi ta kama hannuwansa suka nufi d’akin ashe duk zaman da suke a parlo Jamal na labe yana kallonsu ajinsa ko wani abun zasu oho yanaga sun nufo d’akin ya koma da sauri ya kwanta har dakin suka shigo tana rike da hannusa kiss ta masa ” mu kwana lfy murmushi yayi ya daga mata kai ficewa tayi daga d’akin
ta rufo masa, kofar dakinta ta nufa naga ta daga hankadan pillow ta dauki wata yar kwallaba ta bude murfin ta kafa bakinta saida tasha rabi ta maida ta buye ta dauki wasu kwayoyi ta zuba bakinta tana taunawa ta kunna kida ta saki sauti wakar larabci ce sai tikar rawa take baji ba gani sai ihu take da tsalle da juyi kafin zuwa karfe biyar abubuwan da tasha sunyi mugun ratsata sai tangadi takeyi amma haka ta Mike taje tayi Alawlla tasaka Riga doguwa ta tayar da sallah amma ta kasa tsayuwa sai azaune tayi tana gamawa ta bungire saman daddumar sai bacci ya kwasheta,,
***************************************
Bayan kwana ukku zuwa wannan lokacin zee da Mahabeer sunyi muguwar shakuwa bata iya nisa ko nan da can tare sukaje sukayo sayaya tsaraba kaf yan gidansu yayo masu tsaraba tare sukaje kabah yayi umarah wacce da kashigo garin ake rakaka kayi yayima zee baby Addu’ar shiriya da shaye shayen da takeyi dan ya kamata tasha kuma ajikinsa mayen ya fara kamata har kuka yayi ummi Raiyan tace ai shine babban abinda yake daga mata hankali shiyasa ta matsu tabar Nigeria dan tasan acan ina zataga kayan maye shiyasa ya kara Sata jikinsa dan yasan saida lallaba sun gama shirya kominsu na tafiya yau suke tashi karfe ukun dare zee baby har cikin ranta batason tafiyar amma da ta tuna sati dayane zatayi taji tanaso taje kasar hausa ta ga ya take ya tsarinsu da Al’adunsu yake tasha kunshi kafa da hannu kitsone dai ba’ayimata saboda tausahin gashin da santsinsa ko anyi tsefewa yakeyi ga zafi da ciwon kai da yake Adabarta shiyasa bataso
su manal da jannat da Radia tun safe suke gidan suka gaji da raye rayansu kuma suka koma kukan rabuwa saida ummi Raiyan da Mahabeer suka lallashesu sukace ai sati daya zatayi ta dawo tukun hankalinsu ya kwanta suka saki jikinsu sukaci gaba da sabgar gabansu, sai bayan sallahr magrib sukayi shirin zuwa Jeddah gaba dayansu sukayi rakiya zuwa Jeddah, karfe tara suna Jeddah Airport zazaune sai lokacin ummi Raiyan takejin ciwon rabuwa da Zaeenaba amma ta dauré dan tasan idan zee din ta gani zatace bazata ba yawonsu su zee suka tafi da su jannat sai sayaya take duk ba sanin mutanen tayi taji tana son kaimusu abubuwan nan k’asar sai wajan sha biyu suka dawo Mahabeer yacewa ummi Raiyan su tafi dan bayaso sai lokacin tafiya yayi ta kafa kuka rungume juna kuwa suka suna kuka su dukansu sai daket ya lallabasu sukayi shiru Jamal ma sallama sukayi Mahabeer yayi masa godiya sosai da karamcinsa Jamal yace saboda zee gashinan zuwa Nigeria Mahabeer ya amsa dan yasan karyace Raiyan ta kara rumgume zee tanata sumbatarta itama sumbatarta takeyi sun jima ta jata gefe tayi ta mata fada ta nutsu tako amsa ta da to suka rabu kowa na hawaye abinda yasa zee bata damuba saboda ance sati dayane zatayi shiyasa su manal da kuka suka shiga mota suka tafi ji sukeyi kamar su bita, kuka ta fara daket yasamu tayi shiru
Sai karfe biyu da rabi suka shiga cikin jirgi saboda shirin da Mahabeer yayi bazaka taba cewa ba balarabe bane ba zee ko baka ganin komi nata sai kwayar idanuta to dama Al’adar garince haka jirgin cairo ne suka shiga sai karfe ukku da yan mintuna sukaji alamar jirgin zai tashi zee ta fara rawar sanyi dama jikin Mahabeer ta jingina kallonta yayi yaga tana karkarwa jikinsa ya janyota ya rumgume ya ciro mayafi ya lullubeta kara shigewa jikinsa tayi” zee,na menene? jinkita ya taba yaji zafi gum hankalinsa ya tashi dan yaji zazzabine ya zubo mata hannuta ta sakalo wuyansa tana hucin zazzabi ga rawar sanyin da takeyi kiransa tayi”Ahukhuya? ” Na’am zeena yi hakuri kinji jirgin tashine zaiyi bari ya tashi na samo miki magani kara matseta yayi yana lallashinta yada ya shigar da ita jikinsa yasa ta rage jin sanyin cikin sa’a wani balarabe cikin ma’aikatan jirgin masu rabon abunci yazo wucewa Mahabeer ya tsayar dashi duk da yaga sauri yakeyi cikin sa’a ya tsaya ya tambayeshi da turanci maganin zazzabi yakeso matarsace babu lafiya yace” ok ya jira jirgin ya daga yanzu zai kawo masa, godiya yayi masa ya tafi yaji dadi sosai da za’a samu maganin tasha karfe uku da rabi dai dai jirginsu ya daga zee na manne da yayanta tana rawar sanyi hankalinsa ya kara tashi jirgin na tashi zee ta fara kwarara amai jikinsa ya rumgume tsam har ta gama yana bubbuga bayanta hankalinsa atashe ” my zeena sannu kinji kai ta daga masa dagata yayi ya mike ya janyo jakarsa ya ciro wata jallabiya baka mai shegen kyau ya ciro karamar Jakarta itama ya ciro mata abaya shi ya fara zuwa ya gyara kansa cikin toilet ya canza kaya tsaf sai yafi d’azu kyau ya dawo ya kama hannuta suka tafi akofar toilet ya tsaya ya bata kayan ta shiga ta canza ta wanke fuskarta da bakinta
ta fito ya kamo hannuta suka dawo ya feshesu da turare ya zauna ta kwanta jikinsa ya lullubeta bai jima da zamaba mutumin ya kawo masa maganin harda ruwa da dan abin masarufi cimarsu ta larabawa ya lallabata ta danci ya bata magani tasha dan batada matsala da magani saboda ta saba cin kwayoyi Allura ce ko zata mutu babu uban da ya isa ya mata ita tanasha ya rungumeta yana lallabata ba jimawa tayi bacci ajiyar zuciya ya sabke ya duko ya mata kiss saman goshinta ya kara shigar da ita jikinsa ya rufeta ruf, koda akazo rabon abunci bai amsaba dan shi bai fiye cin abunci ba idan yana tafiya kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanusa dan bacci yakeji bai jimaba ko baccin ya daukeshi jirginsu na sharara gudu cikin hazo